Sashe 51
Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da fara'a dai a fuskarta tace "Pah, ai domin ganawar bawa da ubangijinsa babu buk'atar neman izinin wani, da zaren yanayi ya bayyana ga bawa na lokacin ganawa da ubangijinsa, babu wani mahaluki da ya isa ya masa shamaki da hakan, indai ba mala'ikan d'aukar rai ne ya ziyarcesa ba."
Cikin fushi da d'aga murya yace" Shiru! Kina so ki ce min akwai wani ubangiji ne bayan abun bauta Ghira?"
A take ta amsa da" Akwai, wanda ya hallici talakawanka, ya hallice ni kuma ya hallice ka, abun bauta Ghira ba komai bane kamar yanda ba kowa bane face marar anfanin da ba zai anfani ko da kiyashi ba."
Dhurani dake gefe yna ta hararenta jin an tab'o huruminshi yasa shi mak'ale murya yace" Gimbiya Zafeera, shi wannan abun bauta Ghira da ki ke magana a kan shi, shi ne fa yayi komai da kike gani, da izininsa komai ke faruwa, da kuma amincewarsa ke kanki kike raye a yanzu."
Wata malalaciyar dariya ta saki ta kalleshi da kyau tace" Sai kuma gashi a gidan dana rayu babu sassak'en gunkinshi, to kenan ta ya har ya rayar da ni?"
I'ina ya fara yana rarraba ido yace" E..to..ai buwayarshi..."
D'aga mishi hannu tayi fuskarta a had'e sosai tace" Dakata, buwaya da kake magana a kai ta Allah mad'aukakin sarki ce, da kuma wannan buwayar zan buwayeku har sai mutanen garin nan sun gane gaskiya sannan sun fara bauta ga addinin daya cancanta, da sannu zan fayyace musu ku d'in hadimai ne kawai ga k'irkirarren abun bauta dan cika tunbinanku da kuma aljihanku."
Nunashi tayi da yatsa ta d'aga girarya d'aya sama tace" Daga k'arshe kuma, kar ka kuma saka min baki yayin da nake magana da mahaifina."
Juyawa tayi kan saeki Musail da ya ji gabanshi ya fad'i na shakkun abinda zai fad'a mata, Khatar kam da sauri yayi k'asa da kanshi yana satar kallonta, dan shi kam haka kawai take tsoratashi tun had'uwarsu a Larhjadin.
Cike da k'arfin hali sarki Musail yace "Kinga Zafeera, ba'a son sake ganin wannan taron da kika min yanzu a cikin gida na, idan ba haka ba kuma zaki tilastani na d'auki mataki a kanki."
Sakin murmushi tayi tace "Shikenan Pah ba za'a sake ba, amma tunda ka ce a cikin gidanka ne baka so, ka ware mana waje na musamman da zamu dinga yin ibadarmu hankali kwance, ko kuma mu koma babban gida dukanmu."
Cikin b'acin rai kamar zai cijeta yace "Ke kina lafiya kuwa? Ina fad'a kina fad'a?"
Yar dariya tayi ta girgiza kai tace "Pah, ba kana fad'a nake fad'a ba, sai bayan ka fad'a nake fad'a."
Had'e dariyar tayi ta saka murmushi a fuskar sannan tace "Zan iya tafiya Pah?"
Wani huci ya shiga saukewa kafi ya d'aga hannu ya mata alamar ta fita kawai, dariya tayi irin ko a jikinta nan tace "Nagode."
Saida ta kalli Khatar da kanshi ke k'asa kafin ta saki murmushi ta fice a fadar, cikin farin ciki da jin babu abinda zai faru ta samu Juman tsaye tana jiranta inda ta barta, kama hannunta tayi suka nufi b'angaren Juman d'in tana tambayarta "Me ya faru a ciki? Ya gani ko?"
Ba alamar damuwa tarz da ita tace "Ya gani, kuma babu abinda ya fad'a, zamu ci gaba da taimakon Allah."
*Tana* fita Dhurani ya sauke numfashi ya kalli Adah daya rik'e hab'a, sarki Musail kuma saukowa yayi daga kujerarshi yana fad'in "Ina! Ta ya haka zata dinga faruwa? Ya zanyi yanzu?"
Dhurani ne ya kalleshi yace "Ai matakin kawar da ita kawai zamu d'auka ranka shi dad'e, dan in ba haka ba labarin nan ya kusa tabbata a kan mu."
Cikin k'araji sarki Musail yace "Amma ai tun zuwanta na shirya hakan dan mutuwarta ta zama kamar had'ari, da zuwa yanzu jana'izarta muke gabatarwa."
Khatar ne ya d'aga kai ya kalli saeki Musail d'in yace "Sarki na, ku bar min komai a hannu na, ni zanyi wannan aikin."
A haukace Musail ya kalleshi yace "Kai da ta shigo nan kanka ke k'asa, ta ya ne zaka kashe mana ita?"
D'an murmisawa yayi yace "Mai martaba, ai *wata kokowar* (wanda bai siya ba ya siya ba, mai nemanshi ya tuntube ni, akwai cakwakiya) bata buk'atar jarumta, tunani take da buk'ata."
Dhurani ne yace "Hakane kuma, ina ga a bashi dama ranka shi dad'e."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan, sai ka jaraba mu gani me zaka iya."
Shi ma jinjina kai yayi yace "Nagode ranka shi dad'e, daga yanzu zuwa daren yau zaku ji kukan hadiman da suke tare da ita."
Daga haka su ma zaman na su ya k'are dan abinda ke damunsu kenan, sun zauna ne da niyyar tattauna maganar ruwa da ta zo mishi da ita, amma bala'in da ta zo da shi ya girmi waccen sai ma ya mantar da su gaba d'ayansu.
*Alhamdulillah*
01/01/2022 脿 11:40 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*LU'U LU'U*_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
_SADAUKARWA GA_
*'YA'YA NA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*29*
Kamar jiranshi ake ya koma b'angaren shi Adah ya mik'o masa wayarshi yace "Yallab'ai ana kiranka a waya."
Kallonshi yayi kafin ya sa hannu ya karb'a ya duba lambar da babu suna, k'arasawa yayi cikin falon ya nemi guri ya zauna tare da aje wayar gefenshi har ta tsinke, a tsanake Adah ya kalleshi yace "Ranka shi dad'e, na ga har kiran ya tsinke baka d'aga ba?"
Yatsin fuska yayi yace "Bak'uwar lamba ce."
Cikin ladabi Adah yace "Hakane ranka shi dad'e, amma akwai yiwuwar wani mai mahimmanci ne, duba da lambarka ce ta manyan mutanenka."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce wani abu sai kiran ya gajeren sak'o ya shigo wayar, kallon Adah yayi yace "Duba ka gae aka ce."
D'auka yayi ya duba kamar yanda ya ce, da sauri ya kalleshi yace "Yallab'ai, *Abraham Joshua* ne fa, komishinan kud'i da kake shirin yanda zaku tattauna da shi."
Da sauri ya zura hannu ya karbi wayar yana k'ok'arin maida kiran yana fad'in "Ka tabbata? Abraham Joshua?"
Kiran da ya sake shigowa yasa sarki Musail kallon wayar, jim yayi bai d'aga ba na yan dak'ik'u, daga bisani kuma sai ya d'aga, Adah na gefe yana kallonshi jin yanda suke gaisawa kamar sun san juna dama, bayan gaisuwar ne Abraham ya d'ora da "Ranka shi dad'e sarki na, dama wata muhimmiyar magana ce ta sa na kiraka."
A tsanake shi ma ya amsa da "Muhimmiyar magana kuma? To ina jinka, Allah yasa dai lafiya?"
Da fara'a yace "Ah lafiya lau, dama d'an waje na ne ya ke fad'a min ya ga d'aya daga cikin 'ya'yanka kuma ya na so."
Shiru yayi daga haka na dak'ik'u sannan ya d'ora da "To na amince masa ya nemi aurenta a wajenka, saidai ya cika sauri dayawa, da na fad'a masa zamu je tare nan da kwana biyu bayan na dawo daga tafiya, sai ya nuna bai yarda da hakan ba, 'ya'yan manya a kowane lokaci farautarsu a ke, dan haka ya ce shi zai fara zuwa a yau, ni sai na zo daga bayan."
Numfasawa yayi sosai sannan yace" Fatan dai ba muyi gaggawa ba ranka shi dad'e?"
K'urawa Adah ido yayi yana kallo tare da shiga kogin tunani, hark'allar da yake son k'ullawa da kwamishinan kud'in ta isa ta sa ya amince masa, dan haka ya d'an murmusa yace" Ok, wannan ai ba matsala ba ne, ya zo kawai, nan ma kamar gidan su ne."
Numfashi ya sauke kusan sau uku kafin yace" Amma...wace a cikin gimbiyoyin na wa?"
A hankali yace" E to...ina jin dai kamar k'aramar."
Jim sarki Musail yayi sai kuma ya tab'e baki a ranshi yake fad'in" Idan ta zama gawa kafin nan sai a maida auren kan gimbiya Zafreen."
A zahiri kuma murmushi yayi ya amsa da ba komai kawai sai sun zo, har da tagomashin fad'in" Zan tura dreba ya je ya d'aukoshi."
Da sauri Abraham yace" Yallab'ai sai dai ba shi kad'ai ya taho ba, tare yake da mai tsaron lafiyarsa."
Jinjina kai Musail yayi yace" Wannan ba damuwa bane, ko su na wa zasu zo akwai masaukinsu."
Suna Ida wayar ya kalli Adah yace" Ka kula da komai Adah, ka tura dreba ya d'aukosu a filin jirgi, sannan ka sa a shirya musu tarba ta musamman, dan neman aure zasu zo."
Da sauri Adah ya kalleshi cikin ladabi yace" Ranka shi dad'e a gafarce ni, amma neman auren wa daga cikinsu?"
Ba tare daya kalleshi ba yace" Zafeera."
Da mamaki yace" Zafeera kuma? Ranka shi dad'e wacce muke shirin turata wata duniyar, me ye hikimar yin hakan?"
Wani lallausan murmushi yayi yace " Ka zuba ido kawai ka sha kallo."
Rusunawa yayi ya jinjina kai tare da fad'in" Na barka lafiya sarkina."
*Suna* zaune d'akin Juman hadimai biyu suka shigo da farantan abinci, Ayam dake duba zoben da Juman ta nuna mata na azurfa wanda ta ce Urab ya bata shi, ajeshi tayi kan k'aramin teburin, suna zuwa su ma suka aje kwanukan akan teburin, a tsanake Juman ta kallesu tace "Me aka dafa yau?"
Cikin ladabi d'ayar ta shiga bud'e mata kwanukan dan ta gani da idonta, murfin kwanan ta aje a k'asan zoben, hakan yasa Ayam data gani tace "Mik'o min zoben nan?"
D'aukowa hadimar tayi ta mik'o mata, karb'a tayi saidai sub'utar hannu yasa zoben sub'ucewa ya fad'a cikin farfesun kifin da ke kusa, da sauri Ayam ta furta "Oh Allah."
Da sauri hadimar ta d'auki cokali tana fad'in "Oh! Sannu gimbiya, bai fallatsar miki ba?"
Girgiza kai tayi tace "A'a, ki gaggauta ki ciro shi."
Cokalin ta sa ta d'auko zoben nan na azurfa, abun mamaki ya canja kala yayi bak'i sid'ik, sam Ayam bata fahimci me sauyin zoben ke nufi ba, amma Juman da ta san komai tuni ta mik'e tsaye tana dafe da k'irjinta tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Kallonta Ayam tayi tace "Mah, me ya faru? An ciro shi ai."
Hankali tashe tace "Ayam baki gani bane? Guba ce a abincin nan."
Zabura tayi ita ma ta mik'e tsaye tace "Guba kuma? Ta ya mah?"
Nuna mata zoben tayi da hannun hadimar har ya fara rawa tsabar kad'uwa tace "Dubi zoben mana ki gani, ya canza kala."