← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 141

Sashe 95

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin Maheer yasa dawani £3 kalan gudu yaje wurinshi yace "kai Maheer menene wat is it"? Harwani zufa ke ketomai a goshi da kyar ya iya yanunama Hamad cikinshi hakan yasa dasauri Hamad yakai hannunshi yaja riganshi yana kallon cikinshi vakai 0 hannu yataba Maheer yay wani kalan G kara. "Ahhhhh" dasauri Hamad yace "Innalillahi Maheer, ina zuwa I hope inada that iniection ohh no" Hamad yatashi yafita daga dakin dagudu zuwa side nasu baiwani jimaba yadawo dawani kwalban allura yana zuwa yajawo yahada yama Maheer a jijiyan hannunshi sabida yasami relief dawuri yadaura kan Maheer daya bala'in lankwashe akan cinyanshi yana gogemai zufan dayake na tsantsan pain, kusan 1hr suna ahaka kafin cikin yafara lafama Maheer dudda bawai sakinshi yayi duka ba, tashi Maheer yayi ahankali ya jingina da kujer gwanin ban tausayi ya lumshe idanu kawai kaman wanda baida kowa, Hamad jiyayi kaman zaimai kuka. He wanted Yasmeen tai punishing Maheer but at this rate Maheer is suffering way too much, danma yanada dauriva da danne zucivanshi vau kusan kwana takwas fa basa tare, tashi Hamad yayi yadauko ruwa yakawomai kasa karban ruwan ma Maheer yayi hakan vasa Hamad yasamai abaki kadan yasha Hamad a ijive yadafa Maheer yace "dama kanada ciwon ciki ne? Baka taba fadamin ba" adan hankali Maheer yace "bantaba yi ba sai yau" sosai Hamad yaji kaman yamai kuka adan hankali yace "har yanzu Yasmeen bata hakura ba?" Gyadamai kai Maheer yayi kawai yadauke kanshi zuwa gefe yay shiru, dan shiru Hamad yayi kafin ahankali ace "Maheer kanada chronic ciwon ciki you have to do something about it irin wannan shine ke kashe maza dayawa da ban shigo dakin nan ba dabansan yazaka kasance ba" dan shiru vavi vakalli Maheer din gain ya lumshe idanu kawai tashi Hamad yayi yace "muje kaje ka kwanta" batare da Maheer yabude idanunshi ba vace "I can't stand up now anima zan tashi" kallonshi Hamad yay sosai kafin yajuya kawai yafita daga dakin yawuce flat nasu sama yawuce direct zuwa gaban dakin da Yasmeen ke ciki knocking yayi, cikin wahalallen baccin daya kwashe Yasmeen akasa taji ana knocking, bude idanunta tayi jin knocking ake yasa tasan ba Maheer bane tashi tavi ahankali jikinta ba karfi taja dogon hijabinta har kasa tasaka tataho wajen kofan tabude kadan Hamad tagani tsaye ahankali yace "inason magana dake come out" yana maganan yajuya, hakanan Yasmeen taji gabanta yafadi bata taba ganin Ya Hamad yaci serious hakaba sai yau. Slippers dinta Yasmeen tasaka tabude kofan tafito tabishi, wani daki da aka kulle da kwado taga yaciro key dake hade dana mota dake hannunshi yabude yajuyo yace "bismillah shigo" gyadamai kai tayi ahankali tabishi & tashiga dakin itama tamaida kofan tarufe, babu komi cikin dakin sai kuieru dawasu drawers hakanan, kujera daya Hamad yanuna mata alamun ta zauna kafin yawuce yajawo wani drawer, yace "few things na mahaifiyata daya rage ne anan dakin sit" ahankali Yasmeen tazauna kan daya daka cikin kuierun tana kallonshi dan batasan mesa vatadata cikin dare ba Hamad baimataba kiranta ba, wasu yan pictures guda uku haka Hamad yaciro daga drawer yana kallo sannan yajuyo tareda mikama Yasmeen yace "look at this pictures" hannu Yasmeen tasa ta amshi hotunan dayake bata takalla hotunan old pictures din da ne, dan daga yanayin black picture a wajen zaka gane cewa nadane, wani mutumi tagani makaho da sanda a hannunshi wanda tana gani tasan Baba ne, yadata Hamad yana yaro sai wanda kallo daya tamai tasan Maheer ne dabai wuce Nanan su ba kokuma tace da kadan yafi Nanan su, fuskanshi adaure tamau kaman yana shirin dambe akai hoton ga kayan jikinshi duk yagaggu har a Hamad ma yafi na jikinshi kyan gani, sosai take kallon hoton wanda Maheer kawai take kallo aciki bawani ba, anatse Hamad yace "duba sauran" nabiyun tazaro takalla Maheer ne shikadai zaune akasan gada wani bridge haka ya daure fuska tamau kaman wanda ke shirin dambe nan ma da mutane lokacin akalla zaikai shekara bakwai haka nan ma kayan jikinshi yagaggu ga majina bushashe a hancinshi, sai kuma last picture data kalla wanda kaman ma Maheer baisan anyi hotonba yana karkashin wani bishiva shi kadai vadaura hannunshi akan fuskanshi yana kuka sosai, dasauri tadago kanta takalli Hamad ga mamakinta hawaye tagani akan idanun Hamad yasa hannu dasauri ya share, Hamad is a very emotional person gashi da tausayi, ahankali Hamad yace "Yasmeen inason kanina sosai, duk wanda zai cutarmin dashi kova wahalar mini dashi tsananshi nake sosai wh, dan Allah kada ki cutarmini da kanina kema" Hamad yay maganan was sababbin hawaye na zubomai dasauri ya sharesu Yakalli Yasmeen anatse ace "naso Maheer shine zai baki tarishinshi dakanshi but I guess bazaitaba iyawa ba dan baida surut baida magana ko kadan Maheer" Hamad vasakeyin shiru kafin ahankali yace "inaso nabaki labarin Maheer ne sabida ki sassauta kowani kalan hukunci kikemai ko kikeso zakimai Hamad yasakeyin shiru kafin ahankali yace "bantaba gain yaron daya taso cikin kunci dakuma lonely life kaman Maheer ba, toro, damuwa ba kaman Maheer, dudda ni iyayena duka biyu makafi ne suka haifeni, dudda mahaifiyata tarasu amman nafi Maheer jin dadin ravuwa nesa bakusa ba" yasake yin shiru kafin ahankali yace "mahaitiyar Maheer was a criminal yar fashi ce though shi karan kanshi baisan labarin ta ba but dai yar fashi ce bayan an kamata aka kaita gidan yari KIRIKIRI FEMALE PRISON a lagos sunanta Hafsatu, Mahaifin Maheer was a guard a prison din sunanshi Aliyu Maheer, yaya akayi oho rana daya akaga mahaifiyar shi da ciki agidan yari matan datai kusan 2vrs a prison din rana dava aka ganta da ciki, dudda taso tai abortion but ba halinyi agidan yari, investigation wayamata ciki aka fara tafada Aliyu ne dalilin dayasa aka sallameshi a aiki kenan aka koreshi daga aikin gidan yarin, itakuma tacigaba da rainon cikin dabataso dudda taso takashe dan cikin ta hanvar kin shan magungunanta da sauransu ahakadai ta haifi Maheer anan gidanyari, ba'a rabata dashi ba haryay shekara daya da rabi tareda ita dudda bawai wani kula dashi takeba wani zubin idan yana kuka ba sai prison guards mata sunzo sun danneta tabashi nono da karfi dayaji, kafin 6month Maheer nacin komi inii Maman dan ita keba da labarin a area mu, akarshe dai sabida Maheer data haifa gwamnati tayafe mata laifinta tafito nan sukai connecting da mahaifin Maheer kulle dan sabida shine aka yafemata tafito ta raini danta da kyau so hakanan ta yarda sukai auren yadawo da ita nan Abuja cikin chan wani kauye a maraba dasu axis na nyanya dan sufara rayuwa afresh" Hamad yadanyi shiru nakusan 2min kafin ahankali vace "Fateema a asalin ghetto side na nyanya muka girma, area da thugs, criminals, waye waye ke zama, tunda nake bantaba ganin iyayen dazasu haifi yaro amman kaman basu suka haifeshi ba sai akan iyayen Maheer, kallonshi suke a mistake child, basason haihuwa to babanshi agbero mahaifiyarshi ma haka, basa bashi abinci, basamai wanka, basamai wanki, basu sashi makaranta ba, baida ma takalmin kafa, kusan mahaifiyarshi tamafi tsaneshi ne sabida gane take sabida shi takasa cigaba da rayuwanta, takasa komawa past life dinta, gashinan tazauna batada kudi kuma bata isa tabarshi ba kada asake maidata prison, sannan kullum mahaifin Maheer da ita bala'i suke, dambe, dambe, dambe kaman yan gidan dambe makota harsun gaji da shigowa ana rabasu, ke amsa sansu kina shigowa cikin layinmu kikace gidan dambe zaa kawoki gidan mu danmu makotansu ne duk haya muke agidan, Maheer na yaro but he is such a sad boy sabida vanda kullum mamanshi da babanshi dambe sukeci har kofar gida kuma basu rabu ba, wani zubin dambe babanshi har Riga yake cirewa a titi, Maheer tsoron iyayenshi ma yake kaman yaga doddanni, kaman baya cikinsu idan zaiyi kwana biyu basu ganshi ba bazasu taba nemanshi ba, kullum dare saidai varaba yashiga ya kwanta kusada kofa yay bacci akasa, sannan kusan kullum akan Maheer karami suke juve anger su bayan fada suma yaron nan shegen duka saisa yake mutuwan tsoronsu yaron yazo yanada bakin zuciya da taurin ral, Maheer has been a traumatized little boy kinsan mesa Maheer baida magana sannan baya dariya kullun zakiga fuskanshi ahade"? Dasauri Yasmeen ta girgiza kai Hamad yace "sabida iyayenshi, kinsan ya akayi muka zama friends"? Girgizama kai Yasmeen takarayi shiru Hamad yayi hawaye suka kara fadomai daga idanu yashare dasauri yace "Mamanshi bata bari yay magana da kowa agidan mu da area mu, idan suka fara fada suna dambe toro saiyasa yafito vana kuka vana neman inda zai bove vadaura hannuwanshi biyu haka akunne" Hamad yadaga hannayenshi yana nunama Yasmeen vace "yahau kuka sosai yana juye juye da neme neme munada wani babban cage na kaji Maman mu lokacin" Hamad yadanyi shiru kafin ahankali muryanshi narawa sosai dan he's damn emotional yace "cage din kajin nan, nan Maheer kezuwa yashiga ya boye tareda kaji yataushe kunnenshi yana kuka sosai • tun safe har dare ba ruwa ba abinci, duk idan naje kaima kajinmu abinci naganshi yana kuka yasa hannu akan lips dinshi vana kallona alamun nai shiru kada in nuna yana nan Maman shi tazo ta dakeshi, ragowan abincin mu dana kawoma kaji zai karba vahauci yana kuka ahaka daganan abincina sainaki ci nakawomai yaci Nima sainashigo cage din dagani sai shi sai muyita wasa yadaura kanshi kan kafadanta yay bacci kaman baya bacci agidansu yana munshari ya rikemin hannu gam irin kaman kada natafi na barshi" hannayenshi Hamad yadaga yadaura kan idanunshi yanadan huci mai zafi sabida kuka itama Yasmeen tasa bayan hijinta kan idanunta kawai sabida kuka labarin na wani kalan sosamata rai, kusan 3min Hamad yayi ahaka sannan yazare hannayenshi yasauke ijiyan zuciya ahankali ace "watarana fada yay fada agaban Maheer suka kunna wuta adakinsu wai saidai sumutu dukansu dan Baban Maheer yace mata zai kara aure, Maheer yagudu yafita daga dakin yana taushe kunnenshi yana kuka yashiga cage na kaji yalabe as usual, dakinsu yakama da wuta kafin kice me wuta yakama duka gidan ma yan gida aka fara fitowa waje kowa dagudu, nadawo daga makarantan allo kenan da allo a hannuna naga wuta yakama gidanmu gasu Baba duk awaje naji ana cewa ai mutanen prison dinnan ne suka sa wuta wato iyayen Maheer, dasauri najujjuya banga Maheer adandazon mutanen wajen ba, dudda ana ihu ana kirana saida
Chapter 95 · 0% Book details