← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 141

Sashe 137

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gobe zamu gama ba page 165 ne End [8/20, 11:05 AM] SAFIYYA: Da kyar Yasmeen ta iya tashi tsaye tana goge fuskanta tadauki lafayanta tadaura akirji bazama ta iya dukawa daukan sauran kayan ba su bra da pant dan cinyoyinta ciwo suke ahankali da dafa bango tawuce tafita daga dakin tana fita Maheer yafito dan baimayi komiba abayin wajen kofa yayi, kofanshi yabude kadan yana kallonta saida yaga tabude kofan dakinta tashiga hankalinshi ya kwanta dan kartaje tafadi dan yasan abinda yamata sannan yakoma bayi yayi wanka agurguje yafito ya shirya cikin jean da riga yafice zuwa masallaci. Bayi Yasmeen taje ta gasa kanta sosai sannan tayi wanka gabaki dayanta kamshin Maheer take tafito ta shirya tai sallan anan kan dadduma bacci yay awon gaba da ita. Dudda kalan shegen baccin dake cinta but zuciyanta gayamata breakfast dazata ma mijinta yake cus tasan Maheer yadade baici proper abinci ba bude idanubta tayi da kyar ta tashi tanaso ta faranta kai dan tasan tabata mai, tashi tayi wayan dake kan side drawer tadauka kawai ta kira Baba kai tsaye ringing biyu yadaga tagaidashi anatse tace "Baba inaso Farida tazo zata tayani girki" kaman ba Baba ba dasauri yace "too gatanan zuwa bari nakaita nasata a abin hawa" murmushi sosai Yasmeen tayi ganin yanda Baba ya chanza tace "nagode Baba" katse wayan tayi ta ijiye tasake shiga bayi wanka tayi tabude sip din taciro wani jean tasaka blue dawani baby pink shirt bamata tasa lafiyayyen dan kunne dayay matching d sarkan ta da har yau bata taba cire shi daga wuyanta ba tadan bude boturan gaban rigan kana hango tudun boobs nata tai parking shukun kanta wh tai bala'in kyau kaman ba Yasmeen ba wanka yayi da turaruka sannan tafito ahankali take tafiya tashiga sauka daga stairs tawuce kitchen komi sabi wasu abubuwan bama abude ba ga kayan abinci, sotake tayi sinasir, tayi farfesu, tayi kunu, tayi shayi da coffee, sannan tayi laflyayen jellof na basmati rice dakuma juice he hopes Farida zata iso yanzun nan, fara aiki tayi tana komi ahankali dan batada karfi sosai. Sun dade amasallaci dan meeting akeyi duk sabida Maheer ana tayashi murna fitowa Hamad yayi daga mosque sabida call din da akamai daga Hospital keke ya hango akofar gidansu, dauke kanshi yayi yacigaba da wayan dayake I ihun dayaji me keken yayi. "Dalla Malama kibani kudina" yasa Hamad yajuyo yakalli kofar gidan nasu sai alokacin yaga Farida dukta rude takoma baya dasauri jikinta narawa, baima tsaya idasa wayanshi ba dasauri yayi wajen yana kaiwa daidai me keken ya miki hannu zai fizge hannu Farida dawani kalan sauri Hamad yace "kai laflyan ka kalau? Arude Farida tajuyo takalleshi ganin Hamad kaman jira take tasaki kuka sosai tace "Ya Hamad kagawai saina bashi dubu daya kuma 500 ne ake kawo mutane nan anguwan" Dasauri Mai keken yace "karya take agabana Babanta yasata akeke yaciro dubu yabata tabani ta boye dayan dari biyar dinne inaji tana fadi wai kudin anko zata tara" turobaki Farida tama me keken tana kara komawa gefen Hamad kaman zata shige jikinshi duk atsorace take kana gani kasan bata saba hayaniya ba, dan murmushi kadan Hamad yayi yasa hannunshi a aljihun wandonshi yaciro 1k yamikama mai keken yace "koma menene basaika mata ihu ba babu kyau harassing mata bakaga yarinya bace ba" karban kudin mai keken yayi yace "yallabai naga zata rainamin wayau ne amman nadaina, sai anjiman mu" ballamai harara Farida tayi takai hannunta tana share fuskanta mai keken yaja yawuce, Hamad yajuyo yakalleta yace "sai tsoro amman kin iya neman fada" abala'in shagwabe tana bin keken daya wuce da kallo batare data kallo fuskan Hamad ba tace "Ya Hamad ai 500 ake kawoni gidan nan meruwan shi da kudin da Baba yabani dan sa ido kawai" ta ballama keken harara da manyan idanuwanta farare tass, hakanan Hamad jiyayi gabanshi yafadi dasauri yadaina kallon fuskanta yace "wace kawarki zatai aure?" Dasauri Farida tajuyo da kanta takalleshi tace "yar ajinmu ce Hafsat sunanta ina kiranta Hafcy itane Besty na Ya Hamad" tafiya Hamad yafarayi tana biyeda shi yace "nawane ankon"? Batare data kawo komi ranta ba tace "11k ne kala biyu, kaga atampan 5k, sai ashobe 6k, kaga yanzu inada dubu dayan nan natara 7k kenan" dan zaro idanu Hamad yayi yace "iyyee nida da har zance kibani rancen kudin amman tunda anko zakiyi nahakura" dasauri Farida takalli fuskan Hamad cikin son gasgata maganan shi tace "Ya Hamad da gaske zaka ranci 7k din ko wasa kakemin"? Tsayawa yayi dan gabanshi tasha tamai tambayan, yana kallon idanunta yace "da gaske nake" dasauri tace "kudin na gida gobe nakawo maka I promise" Hamad na kallonta yace "ankon bikin fa" dasauri Farida tace "nafasa wh, inhar zaka tambayeni rancen 7k nasan bukatan ka is more important than anko na inada wasu sabbin kaya harna salla na ma na nan sainasa" dan murmushi Hamad yayi she's so innocent kaman Yasmeen,hannunshi yasa ta gefenta yabude kofan gate dinsu ahankali yace "to shiga gida bari nakoma mosque" murmushi tayi tace "bye Ya Hamad" tamai waving hannu murmushi yamata tawuce tajuya tashiga tayi hanyar flat na Yasmeen hakanan samin kanshi da kallonta Hamad yayi kaman wani abu yashigeshi yau game da Farida, yakasa rufe gate din saida tabude kofan flat nasu Yasmeen tashiga sannan yasauke jiyan zuciya tareda rufo gate din yadaura hannunshi kan zuciyanshi dayaji yana bugawa sosai sannan yajuya yakoma mosque. Wuraren 9 Maheer yashigo gidan lokacin Yasmeen da Farida na jera abinci a dinning tana ganin Maheer Farida tazo dasauri tace "Ya Maheer ina kwana tun dazu nazo baka dawo ba daga masallaci ba" murmushi yamata yaji dadin ganinta sosai yace "Ina Ammi da Nana" murmushi tayi tace "duk sunce na gaisheka, Ya Maheer dama haka Anty Yasmeen kemaka girki kala kala mu agida fa bata mana girki dan satan kallon Yasmeen yayi ta gefen ido dake kallonshi yace "bari naje nai wanka nazo naci" gyadamai kai Farida tayi takoma dinning Yasmeen harta shiga kitchen dan bataso Farida tagane sunada matsala ta kwalama Farida kira, Farida tashigo kitchen din, Babban kula guda uku Yasmeen tabata akan tray tace "gashi tayani kaiwa side nasu Baba, saiki dawo ki dauki juice" gyara daurin dankwalin kanta Farida tayi sannan ta karba tawuce tafita dogon rigan atampa ne jikinta ja kaganta kaganta kaga Yasmeen saidai bata gama kai Yasmeen tsayi dan she's just 17 Kwanan nan zata shiga 18, wucewa side din Baba tayi sallama tayi tareda bude kofan tashiga Baba ne kadai afalo dasauri tashiga tace "Baba ina kwana Farida ne" murmushi Baba yayi yace "Mamana yau anzo mana ziyara". [8/21, 11:34 AM] SAFIYYA: Murmushi sosai Farida tayi tace "Baba Anty Yasmeen tabani labarin wani tsiren dakake bata nima yau nazo kabani nawa' tai maganan dinning ta ijiye tray ta juyo gabaki daya tama manta tadanhau dakali kafin taje dinning din duka hankalinta nakan Baba kawai tai missing step lankwashewa kafanta yayi tafadi sosai wani kalan mugun kara tayi tana wUcewa arude baba yatashi yace subuhanallah Farida Farida meyafaru Hamad Baba ya kwalama Hamad kira yana tahowa wajen daidai Hamad na saukowa aguje ganin Farida tama kasa tashi tafashe da kuka sosai awajen dan taji zatin faduwan dasauri da Hamad da Baba suka dagata ihu tayi tafada jikin Hamad innocently dan kaman tai targade takeji, cikeda jin zafin ciwo tace wayyyo00 Ammi kafana yakarye" kajita da surutu wallahi taje tafadi cikin kuka Farida tace Baba tsiren dan dariya hamad yayi yarinta yayi yawa amma wai mutum yana kuka yafadi yake tambayar tsire maza duba hamad,duk ni hannunshi yasa yadauki yar kafanta ahankali yadaura kan cinyarshi her legs is so clean kumbunanta a gyare Farida na kallon Hamad dake kallon kafanta tana kuka tace "Ya Hamad na karye" Gyadamata kai Hamad yayi yace karyewa mai sauki ne kaman yanke kafar za'ayi" wani kalan fashewa da kukan tashin Farida tayi Baba ya make kan Hamad yace wai maisa dakai da Maheer kun iya mugunta ne jibi yanda kakesa yarinya kuka" sake tallabe kan Hamad Baba yayi yace "kaga munafuki akwai wanda yakaika kwadayin tsiren ne" dan murmushi Farida tayi dudda tana kuka karaf a idanun Hamad akunyace ta noke kanta tana murmushi tayi wani kalan shegen kyau daidai nan Hamad ya gyara kafan ihuuu Farida tayi dan unexpected yamata dan kwalin kanta yafadi gashinta yazubo ta tsefe rabi baa tsefe rabi ba sai abin yabada wani style tai kyau sosai kallo daya Hamad yama gashin yatashi yace "kihuta anan anjima saiki tafi Baba kabata naman sorry" yay maganan yana wucewa dinning zama yayi yana bude kulan Farida tashiga daura dan kwalinta Baba yaje dakinshi yafito da nama yace "Hamad zokaje kamata micro waving" dan daro idanu Farida tayi adan tsorace tana goge zufan goshi ta tace Duk Baba zanci haka' hararanta Hamad daya taso yayi ya karba yawuce kitchen yaje yayi microwaving yafito yasa a plate yakawo mata daidai lokacin Malah na sallama yashigo tareda Ahmad hadarai Hamad yayi yakalli Faridan murya chan kasa yace maisa kika fito haka ba mayafi" hakanan taji wani iri sabida yanda yahade rai ahankali tace "na manta ne can you walk"? yatambayeta ahankali gyadamai kai tayi, bata plate din yayi yace "tashi kitafi to" ahankali ta tashi baima bata chance na gaida su Malah ba tawuce tatafi tana dingishi sai akkkareta yake har gaban side nasu Yasmeen saida yabude mata kofa tashiga sannan yawuce yadawo side nasu. Ta Maza yayi a falon yahade rai kallon kasa kasa Ahmad kemai aranshi yace finally ai da na dauka wani cuta ke gareshi yanda baya kula mata" Ahankali Farida take tafiya tana dingishi daidai Maheer na saukowa daga stairs Yasmeen kuma nafitowa daga kitchen atare dukansu biyun suka ganta, kafin Yasmeen tayi magan dasauri Maheer yashigo falon yataho wajen da so much care yace "meya sami kafanki? Ahankali Farida tana kallonshi kaman zatai kuka tace "faduwa nayi a side din Baba" naman hannunta Maheer ya kalla saikuma yajuya yakalli Yasmeen bayabo ba fallasa yace "mesa kika bata abu mai nauyi takai mesa baki aika gateman ba"? Kasa magana Yasmeen tayi tasauke kanta kasa dasauri Farida tace Ya Maheer Wallahi ba nauyi nama ijiye kulan tass kafin nafadi, dana juyo ne" Ahankali Maheer yazaunar da Farida kan kujera yace ina zuwa"? Sama yakoma yadauko wani balm yadawo ya tsugunna gaban faridan
Chapter 137 · 0% Book details