← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 141

Sashe 17

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kusan atare Wike dake rike da wata computer yadawo da Dan dayaje kawo waya, office din suka wuce Wike yazauna yana kunna laptop dinshi yace “Oga abinda bansamo maka game da CP ba shine abinda yafaru ranan da aka haifeshi but everything na samo” yay dan murmushi yana wani kalan alfahari da kanshi yace “Oga dan gidan talakawa ne CP sosai a Dutse aka haifeshi yanzu haka anan gidan da iyayensu suka mutu suka bari yake zama shida wanshi dan kasuwa da kaninshi suna awon abinci akasuwa, su uku iyayensu suka haifa maza, matanshi daya yaranshi uku, kaga bank statement dinshi da informant nawa na banki yaturomini yajuya laptop din yana nunama Maheer, kwata kwata babu wasu manyan makudan innanahan kudin dasuka taba shigo mishi balle muce zamuyi pinning nashi dawani act of corruption, Oga mutumin is as clean as pure water, ba’a taba kamashi da karban cin hanci ba kowani aikin banza, bayabin mata, baya shan giya baya shan taba duk wani abu dazamu dan iya amfani dashi muyi threatening nashi bayayi and mutumin is as stubborn as rock yaya zamuyi kenan”? Shiru Maheer yayi sai chan yace “kace baya karban bribe and he’s from a poor family?” Gyadamai kai Wike yayi, Maheer yakalli bank statement nashi yana yatsine fuska yace “banda this chicken change money salary nashi babu wani kudi dake shigowa account nashi”? Wike yace “kwarai kuwa” jinjina kai Maheer yayi kafin yakalli Dan yace “sa number shi kabani wayan”? Saka number Dan yayi yay dialing yamikamai karba Maheer yayi ahankali ya danna wayan yasaka a speaker ya ijiye kan table.

Wayan na gab da katsewa aka dauka cikeda kamala Baba yay sallama. “Assalamu Alaykum” shiru Maheer yayi bai amsaba, kafin cikin wannan shegen voice din nashi yace “Commissioner Ibrahim Ibrahim” shiru Baba yayi sai chan ya murmusa da kanajin sautin murmushin sa tacikin waya yace “the famous, the kingpin, almighty Pablo Escobar, to what do I owe the honor?” Hannu Maheer yamikama Dan alamun yabashi taba hakan yasa Dan ya kunna yabashi da sauri saida ya zuka ya fuzar sannan cikin isa da takama Maheer yace “Nigeria kap da kewaye babu wanda ya isa yataba kayana! Banyi fushi ba sabida nasankai yaron Oga ne kuma sako kake aikamini dan haka miliyan nawa, kokuma ince biliyan nawa, wait dala miliyan nawa kakeso?” Cikeda isgalanci da tsantsan rashin kunya Maheer yace “nasan baka taba ganin sama da dubu dari biyu da hamsin ba arayuwanka, Commissioner Ibrahim Ibrahim name ur price banda lokaci meeting gareni in the next 45mins” wani kalan murmushi Baba yayi tareda girgiza kai yace “yaro kasami duniya saisa harkakeji ka isa kabani kudi daga kudaden dakake making a saida kwayoyin shaye shaye to bari kaji!” Baba yay maganan cikin kakkausan murya yace “ni Commissioner Ibrahim Ibrahim bana karban cin hanci da rashawa kuma bazan fara akanka ba koda ko zaka bani duka kudin duniyan nan ne, and listen to me your drivers might be hard but nan da few minutes or couple of hours zanyi cracking nasu, Pillow, Pablo ko wakake da suna, empire ka na saida kayan shaye shaye dakai kanka sun soma zuwa karshe I will makesure I bring you to justice koda shine the last thing I will do as a police offer, saina makesure na kawo karshenka ni Ibrahim Ibrahim nai maka alkawarin nan” dan murmushi kadan Maheer yasaki, yace “I wanted to be nice saisa personally nakiraka bansa an kiraka ba, zan maka alkawari kaman yanda kaima kamin alkawari, ni Pablo Escobar namaka alkawari koda ire irenka ku dubu kekaina bazan taba daina harkana ba! Idan kaga nadaina sana’an nan dan kaina ne badan sabida ku government pest da peasant ba, sai abu na karshe Comissioner Ibrahim Ibrahim” Maheer yakirashi cikin kakkausan murya yace “nabaka one hour kasaki kayayyaki na da direbobi na inba hakaba zan aika maka da yar karaman sako, your time start now! Don’t forget 1hour nabaka!” Dip Maheer yakai hannunshi yakatse wayan dake kan table ya zuki taba ya fuzar da hayakin yana huci yakalli Wike yace “what are his likes? And menene weak points nashi” wani kalan murmushi Wike yayi yace “Oga niko nasan likes nashi da weak points dinshi” yay maganan yana danna laptop nashi kafin yafito da hoton Baba dauke da Nanah a hannunshi yajuya laptop din yace “kadinga swiping zakaga sauran hotunan” hakan yasa yafara Wike dake kallonshi yace “Oga aduniyan nan babu abinda mutumin nan yakeso kaman yaran nan nashi mata guda 3, like he is obsess da yaran nan, and over protective of them, I think abinda kafiso aduniya shine weak point naka right Dan”? Gyadamai kai Dan yayi dake tsaye kaman soja yace “hakane Sir” sosai Maheer ke kallon hotunan, saida yakai wanda Baba ke rikeda hannun Yasmeen ya tsaya chak idanunshi kyam akan Yasmeen dabaisan mesa ba kawai face nata just grip his eyes, yakai kusan minti biyar yana kallon hoton, kafin ya janye idanunshi, yakalli Wike yace “nasan mutumin nan bazai taba sakin kayana ba just like that, dan haka inaso get your men ready” gyadamai kai Wike yayi, ijiye taban bakinshi yayi ahankali kan ashtray sannan yakalli Wike yace “duk inda this 3 gurls suke aduniya I want them found, but” dasauri Wike yakalleshi yace “don’t pick them up harsai 1hr dana bashi yacika, idan baisaki kayana ba Dan zai kiraku yabaka go ahead to abduct them and bring them here” dasauri Wike ya gyadamai kai yace “yes sir” yadauki laptop dinshi yajuya zai fita haryakai kofa Maheer yace “Wike” chak ya tsaya tareda juyowa yace “naam Oga” komawa yayi yashige cikin kujera tareda daura kafa daya kan daya yace “don’t hurt them!” Anatse Wike yace “yes sir” sannan yabude kofan yafice.

✨KYALKYALIN KAUNA✨

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣1️⃣

Kina neman kayan GHT irin nasu kara girman nono, katon bombom, rage kiba da sauransu ga way nakawo muku, join this group dan ganin abubuwansu.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KO6bdcXjxmh2l6pM6T0meI

Yau Juma’a kasancewan yanda Ammi ta tashi da damuwa yasa har Nanah datace sai rannan Monday zata koma school tasa Farida dasu Hassana suka wuce da ita dan yaran gidan kap dsame school suke zuwa banda Sa’a da Wanta dakuma Yasmeen dasuka gama suka shiga uni, sosai Ammi ke cikin damuwa Baba ko kiranta baiyiba tun bayan jiyan nan daya koma office da yamma wanda abu mai wuya ne zaisa Baba bazai kirata ba.
Chapter 17 · 0% Book details