Sashe 12
Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bude kofan kitchen din akayi wata babban mace dakeda dan jiki dan akalla zatai sa’an Ammi tafito dauke da tray na samosas dasuka gama soyawa, tana sanye da irin rigunan Chef din nan da aka rubuta Chef MI ajiki, gaban showglass ta tsaya tana jera samosas din daidai nan ta hango wata bakar jeep tai parking agaban wajen wani kalan murmushi tayi tace “Alhamdulillah cinikina yazo yau, nidai kosuwaye mutanen nan Allah yamusu albarka kai Alhamdulillah, aduniya ayanzu banda customers kaman su jiya hardan zazzabi nayi da basuzo ba abincin saidai narabama yara da almajirai” duk tana maganan tana jera samosas dinne a showglass tana lekan motan dataga an bude gaba as usual Dan yafito yana gyara zaman suit nashi sannan yataho yashigo shagon, murmushi Maman Intee tayi sosai ganinshi tace “Jallabai barka da rana nace jiya bakuzo kunsayi komiba” ba yabo ba fallasa yace “Oga ne yay busy bamu samu chance nacin abinci ba” gyadamai kai Maman Intee tayi tana mamakin wani kalan busy zaka shiga dazaka manta da cikinka, tace “to me za’a saka muku yau”? Anatse yace “wanda kika saba sakamana” sake gyadamai kai tayi dasauri idanda sabo harta saba gasudai customers amman baka taba ganin dariyan su ko ayi hira dasu dama Dan ne yawanci ke shigowa ko direba siyan abincin, hanyar kitchen tayi saikuma tajuyo tace “wai yallabai nace mai gidan naku bayacin abincin gargajiya ne irin su tuwo, Inayin wani tuwo da miyan kuka da wlh idan mai gidanka yaci bazai karajin sha’awan su fried rice din nan ba” shiru Dan yayi kaman mai nazari yace “Akwai tuwon akasa ne”? Dasauri tace “a’a amman idan yanaso minti sha biyar yayi yawa nagama komi” shiru yayi saikuma yace “yanzu dai samana order bari naje natambayi Oga naji koyana so” wani kalan washe baki Maman Intee tayi tabude kitchen tashiga shikuma Dan yajuya yafita, baya yaje yay knocking hakan yasa Maheer yasauke glass na motan kadan yana yatsine fuska dan rana yamai rawa, ahankali yace “Oga matan tace atambayoka ko kanason tuwo da miyan kuka that she makes the best, but it will take atleast 15mins” shiru yayi yana kallon Dan gamamakin Dan Maheer yace “inada any meeting in the next 15mins”? Dasauri Dan yace “no daganan har zuwa 1hr u are free babu any schedule” komawa yayi ya jingina da motan tareda daukan wayanshi yafara dannawa ayangance akuma gadarance kaman wanda yake ciwon magana yace “ok” juyawa Dan yayi yana murmushi Oga is full of suprises wlh, dole ma kasoshi kazauna dashi murdadden hali ne dashi at the same time kuma complicatedly sweet, komawa ciki yayi ganin babu kowa yasa yace “Hajiya” dasauri Maman Intee tafito tana kallonshi ganinta yasa Dan yace “amai” washe baki tayi tace “Aiko bazaiyi regretting cin tuwona ba” juyawa Dan yayi yakoma mota itakuma takoma ciki, Yasmeen takalla dake hada takeaways na abincin dasukai order a leda dasauri Maman Intee tace “Yasmeen yimaza hadamin special miyan kukan nan naki yar kadan ta daidai cikin mutum daya Ogansu yace amai, tayi mugun dadi Yasmeen dan Allah kicikamai nama da kifaye nikuma bari na tuka tuwon” murmushi Yasmeen tayi idan kana tareda Maman Intee dole ma kasan yanda takeji da wayan nan customer nata ita bamata taba ganinsu ba dan kullum tana cikin kitchen Baba yace shi bai yadda yarshi ta saida abinci ba kawai girke girken yakawota takoya saisa tana kitchen koda yaushe ko Maman Intee zatai aike saidai wasu students din saidai student nata Monday, Wednesday da Sunday ne suke zuwa classes Yasmeen ne ke zuwa kullum rannan dazataje FCE ne kawai bata zuwa, Yasmeen nada saurin aiki da girki kafin kaceme sanwar yar kadan na kukan yafara tashi lumshe idanu Maman Intee tayi tace “nidai yar nan har mamaki nake irin baiwan dadin abincin da Allah yama hannunki Yasmeen, jibi yanda miyan ke kamshi” murmushi Yasmeen tayi tana zuba tafasassun naman dasukeda shi na kaji, tazuba kifi, Maman Intee kuma tashiga tuka tuwo saida tagama tarufe tukunya sannan tashiga karasa parking musu order, Chinese rice, coconut rice, fridge rice, porridge na yam, duk wani abinci datake dafawa suna saya, kusan 50 take away ne dama order dasuke kullum as usual hadawa tayi tashiga fito dasu waje, sannan takoma kitchen takarasa fito da sauran shigowa Dan yayi yakwasa yafita dasu yasake dawowa yace “tuwon fa”? Murmushi tayi tace “yanzun nan zaiyi kada kadamu basaika kara shiga rana ba zansa student dina takawo muku” Gyadamata kai yayi anatse yace “nasan kudin order mu but plus tuwon nan nawa kenan everything”?Ahankali Maman Intee dake lissafi daka tace “daman normal order ku is 175k ko kowani abinci is 3500 sau hamsin takeaway hamsin, special tuwon danama Oga is 7k yakama 182k kenan” gyadamata kai yayi yajuya da ragowan abincin yafita yakai mota ya ijiye, dawowa yayi da bandir na yan 500 naira sababbi guda hudu yace “gashi asha ruwa da chanjin inji Oga” wani kalan washe baki tayi tama kasa magana sabida dadi Dan yace “ina jira a mota idan an gama a aiko mana dashi” gyadamai kai tayi tace “Allah yasaka da alkhairi Allah kara girma, atayani yima Oga godiya” badadan Baban Intee yahanata ba data fita tama Oga godiya da kanta, kwasan kudin tayi tashiga kitchen tana murmushi daidai Yasmeen na kwashe miyan awani take away dasauri Maman Intee tace “tsaya tsaya ina bansama Oga abinci a normal takeaway bari na dauko wayan nan imported take aways din kiga” fita daga kitchen din tayi tashiga tsakar gidan su zuwa dakinta tafito dawasu hadaddun take away takarbi miyan ta juye tasa man shanu itama ta kwashe tuwon tai packaging zokaji kamshi, cikeda farin ciki tace “Yasmeen taimaka mini kije waje kibasu suna cikin mota dan Allah ninece su zauna, yaron Alhajin yafita yadawo yakai sau goam saisa nace su bari dalibata zata kawo musu tuwon”, dau hijabinki kisa kiga” ahankali Yasmeen takai hannunta taja pink hijabinta dake sagale jikin kofan kitchen din tasaka ta karbi takeaways din da Maman Intee tadaura mata akan wani disposable cute tray abin looking so fancy tajuya har zata fice Maman Intee tace “tsaya nasa mishi special zobon dakika hada yasha yaji nasan wlh sai gobe yadawo still yay order abincin nan dan koni bantaba shan zobon dayakai naki dadi ba Yasmeen tunda nake aduniya” murmushi Yasmeen tayi akunyace tace “aike kika koyamin” Maman Intee dasauri tace “nasani but still nida nakoya mikin nawa baikai haka dadi ba, wanna wani sirri ne da Allah yama hannunki” murmushi takarayi maganan yamata dadi, for the first time in her life ga abinda akace ta iya! Maman Intee takawo gora daya na zobo dayay bala’in sanyi yama fara kankara amman ba sosai ba tadaura kan tray sannan tasa hannu tabudema Yasmeen kofan kitchen din tace “jeki kikai” fita tayi daga kitchen din ahankali tana tafiya, har zuwa entrance door dazai sadata da waje, gently tadaga right foot nata tafito dashi waje wani kalan sanyi taji kaman ta taka ice tundaga kan yatsan kafan nata har zuwa kai dayasa takasa motsi, ko kadan daga Dan har direba basu lurada itaba sabida waya dasuke dannawa, Maheer na baya idanunshi a lumshe ga waya a kunnenshi hakan yanuna waya yake saidai baya cewa komi wanda hakan halinshi ne, ahankali yakai hannunshi yadaura akan heart dinshi dayaji yabada wani single beat mai karfi dat is so unusual da saida yajishi har brain hakan yasa yasauke ijiyan zuciya ahankali, kusan 20secs tayi ahaka sanan ta iya tafito da second leg din nata tafara tafiya tana dumfaro motansu ahankali da bata iya ganin kowa na ciki motan baka kirin da ita, jikinta namata wani iri tsayawa tayi agaban motan tareda sauke ajiyan zuciya takai hannu kenan zatai knocking Dan yaga inuwanta hakan yasa yabude gaban motan da sauri ya mika hannunshi yakarba yace “har angama”? Batare data kalli fuskanshi ba cikin yar muryanta dakeda ratsa zuciya ahankali tace “eh!” Tareda juyawa at the same time, gently Maheer yabude idanunshi dake alumshe yana waya sabida wani kalan sweet voice daya daki dodon kunnenshi data furta “eh!” Wayan na kunnenshi yajuyar da kanshi yakalli waje ta glass din, bayan wata yarinya yagani matsakaiciya da hijabi pink har kasa ajikinta tajuya tana tafiya ahankali akuma natse takoma cikin shago, dudda baiga fuskanta ba but kalan hijabin yay kyau kodan hasken rana ya haskashine oho but sha dai yamai kyau kalan. Dan yatsine fuska yayi ahankali yace “nagaji da magana talk to you later” zare wayan yayi batare daya katse ba ya yarda wayan akan kujeran wanda hakan yazaman mishi habit, direba ya kunna motan suka bazama titi suna gudu, ahankali yasake kai hannunshi yadaura kan kirjinshi dayaji bai dawo daidai ba yanamai wani iri daya kasa tantancewa to kodai baida lafiya ne, basu wani dade ba sukakai gida sabida yanda suke gudu.
Budemai kofa akayi yafito yayi ciki Dan yabiyoshi rikeda tuwonshi a tray dakuma takeaway daya na Chinese rice for Nas, sauran takeaways kuma na duka ma’aikatan gidan nan tundaga kan sojojin su masu gadi kusan maza 49 ke rayuwa agidan idan kahada da Nas da Maheer about 50 of them kenan, a dinning yawuce ya ijiye na Nas sannan yahau stairs yay sama, gaban wani babban daki yasaya da kofan ke akulle knocking yayi ahankali, almost 3min yabata sannan yace “shigo” bude kofan Dan yayi yashiga ciki dakin kaman wani empire na sarki komi fari sai kyau kaman dakin basarake babu kowa adakin hakan yasa yagane yana bayi, ijiye komi yayi kan kujera sannan yafito.
Budemai kofa akayi yafito yayi ciki Dan yabiyoshi rikeda tuwonshi a tray dakuma takeaway daya na Chinese rice for Nas, sauran takeaways kuma na duka ma’aikatan gidan nan tundaga kan sojojin su masu gadi kusan maza 49 ke rayuwa agidan idan kahada da Nas da Maheer about 50 of them kenan, a dinning yawuce ya ijiye na Nas sannan yahau stairs yay sama, gaban wani babban daki yasaya da kofan ke akulle knocking yayi ahankali, almost 3min yabata sannan yace “shigo” bude kofan Dan yayi yashiga ciki dakin kaman wani empire na sarki komi fari sai kyau kaman dakin basarake babu kowa adakin hakan yasa yagane yana bayi, ijiye komi yayi kan kujera sannan yafito.