← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 141

Sashe 13

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Baya wani dadewa abayi wanka yayi yafito daure da towel a waist nashi sai karamin towel a hannunshi dayake tsane kanshi, kaga Maheer ahaka zaka kusa cinyeshi gawani damanmen ciki dayake dashi, gaban madubi ya tsaya yana goge kanshi da towel din ta madubi ya hango abincin yatsine fuska yayi ya ijiye karamin towel din sannan yadauki some bodyspray da cologne na maza masu tsadan gaske ya feffesa sannan ya ijiye komi yataho wajen kujeran ahankali yazauna yana kallon abincin kaman wanda ake roka da Allah da annabi yaci, da kyar yamika hannu yadauka yadaura akan cinyanshi, he’s not really a food freak abinci bai dameshi ba Sam sam, rabon dayaci abinci tun lunch na jiya da rana, bude take away yayi ahankali wani lafiyayen kamshi ne yadaki hancinshi kaman magic wani kugin yunwa cikinshi yayi, tuwo da kukan looks damn appealing to the eyes, ahankali yadauki spoon da aka nannade a ya warware, yabude tuwon yakai spoon din ya gutsuro kadan sannan yakai cikin miyan yadebo agadarance dan hakan is part of him yakai bakinshi Ya Ilahal Alameen, wani kalan kaikayi kaikayi yaji kunnenshi yafara hakan yasa ya girgiza kanshi dasauri yana hadiye abincin yasake gutsuro tuwon for the second time yakai bakin shi, abincin eatry din dama has always been nice saisa dudda wajen is not fancy bawai wani continental restaurant bane but he always choose abincin su but then again, tunda yake baitabacin abincin dayaji dandanon shi suit his palate and his stomach like this tuwo dake gabanshi ba, ijiye spoon din yayi ganin bayamai da kyau yasa hannunshi yashiga cin tuwon kaman bashiba within 5min yacinye duka uban tuwon nan tas da nama da kifin abin nabashi mamaki, kaman akaromai yakeji, zobon dake kan tray yakalla he hardly take zobo he don’t like it sabida kalan amman samin kanshi yayi da mika hannu yadauki goran bude sealed marfin yayi yakai bakinshi ya kurbi kadan kaman mai tsoron sha, lunshe idanunshi yayi dasauri Oh No! Kafin yadaga goran yakafa abaki saida ya shanye tassss sannan ya sauke goran dagakan bakinshi OMg roban zobon da takeaway ya kalla saikuma ahankali yakalli cikinshi yana mamaki shine yaci abinci haka yakuma sha zobo, it’s unbelievable.

✨KYALKYALIN KAUNA✨

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 7️⃣

Wuraren 3:30 daidai tafito daga shagon Maman Intee tana kalle kallen dan wajen gaban shagon dababu wani mota yanzu datafito ko kadan bataji komi ba keke data gani yazo zai wuce ta tare da sauri ta hanyar daga mishi hannu tashiga suka wuce radio Keken duk yacika mata kunne damai keken ya kunna, muryan Baba taji a radio kaman daga sama yana jawabi kaman jawabin dayayi ne bayan karin girman da akamai.

“Inama alumman mutanen nigeria gabaki daya alkawari cewa zanyi yaki da rashin gaskiya, zan kawo karshen barayi da yan shaye shaye, zan kawo karshen karban cin hanci da rashawa da akafi sanin polisawa da halin, zan kawo karshen miyagun abubuwa sannan zan tabbatar da tsaro da kuma gaskiya…..” wani kalan cute smile tasaki dayasa tai kaman wata Barbie doll sabida kyau tanajin wani irin farin ciki azuciyanta tana alfahari da Baba irin sosai din nan.
Har gaban gidansu Mai keken yakawota bayanshi tayi sanan tajuyo ganin motan Baba yasa tagane yana gida, ahankali tabude gate tashiga ciki da sallama su Nanah ne da Sa’a dakuma Farida ke tsakar gida kan tabarma ga abubuwa daban daban agabansu harda takalma suna gwadawa dasauri tayi cikin gidan Nanah naganinta tasaki takalminta taruga aguje ta rungumeta cikeda tsananin so dakuma shakewa tace “oyoyo Anty Yasmeen kinga Baba yasayo mana abubuwa da yawa naki nadaki wajen Ammi, itane tarike naki, nima kinga yasaya mini takalmin kwas kwas” wani kalan murmushi Yasmeen tayi tareda gyarama Nana kitson kalaban dake kanta dake lilo yana neman shiga idanunta tace “dagaske, sakeni kiga naje na amsa nima naga nawa takalmin kwas kwas din” tawuce ciki batare daya tsaya kallon nasu Farida ba, da sallama tashiga dakin Ammi, Ammi da Baba nazaune kan kujera suna magana akunyace tace “Baba sannu da zuwa” Ammi tace “sannu da zuwa, zo ga naki takalmin da hijabi da jakan Baban ku yasayo muku” dasauri takarasa gaban Ammi takarbi nata dasune suka rage a leda tana murmushi sosai sabida yanda taji dadi tace “Baba nagode Allah saka da alkhairi” juyawa tayi dasauri zata fita danta kosa taje itama tazauna kusadasu Farida tabude nata tagani kaman daga sama Baba yace “zonan” juyowa tayi da sauri tana zaro manyan idanunta masu shegen kyau da grayish kwallan idanun dake gareta, wani leda Baba yaciro daga jakan aikinshi daga ita har Ammi suka bishi da kallo dan itama Ammi batasan me aledan ba mikamata yar ledan yayi ahankali ta tsugunna ta ijiye ledan kayanta akasa sannan takarasa wajen da Baba kezaune tasa hannunta ahankali takarbi ledan jin kwaline Mai tauri tauri yasa Ammi tace “menene aciki bude mugani” kaman dama jira take Ammi tace haka dawani kalan sauri tabude ledan ganin kwalin waya na techno spark 3 yasa batasan lokacin datawani kalan kurma ihu ba tai wani uban tsalle su Farida suka shigo dagudu dan sun dauka bugunta Baba yayi, cikeda murna tace “Ammi waya, touch screen” saikuma kawai tafada jikin Ammi tafashe da kuka sosai ba kakkautawa, Ammi dariya ma abin yabata tace “kagamini shirme menene nakuka kuma, kaga kuka take Baban Nanah” juyoda kanshi Baba yayi yakalleta yanda tadaura kanta ajikin Ammi tana kuka yace “mena kuka kona karbi wayar ne”? girgiza kai tayi ahankali tana ciro kanta daga jikin Ammi takai hannunta tagoge fuskanta tass, takalli fuskan Baba dake kallonta kur batare daya kyafta idanu ba ahankali tace “Baba nagode sosai” murmushi yayi kawai tareda dauke kai, Ammi tace “tashi kije kisa a chaji, kasamata sim dinta aciki ne?” Ammi ta tambayi Baba dan karaman wayanta na hannunshi daya karba jiya, Gyadamata kai yayi hakan yasa Ammi tai murmushi sosai tace “imaza jekisa chaji to tunda ga nefa saiku shirya islamiyya kan ki dawo wayan tacika dam” murmushi tayi ta tashi tafito su Farida biyeda ita suka shiga dakin nan fa suka shiga tattaba wayan saida sukaji gyaran muryan Baba arude sukasa wayan achaji kowa yamike yashiga shirin islamiyya kafin suyi salla suwuce.
Chapter 13 · 0% Book details