← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 141

Sashe 124

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[8/15, 8:01 PM] SAFIYYA: Ammi tasan sarai Baba zai biyota bazai taba bari ta tafi ba, hakan yasa tasa keken yasha kwana yabita wata hanya dazaisa subi anguwanni, tunda ta auri Baba bata tabajin yabata mata rai kalan na yau ba at this point bawai faking nashi takeba jitake auren ma yakare tahuta she is tired, tagaji da Baba, she tired of him, he's always trying to blame her a anything, maisa yake tunanin approach nashi is right? Yasmeen batai karyaba he is really wrong, tasan yaron nan yamusu laifi amman duk Baba ne yaja, yanzu Allah yadaurama Yasmeen sonshi, is only right as a caring father ya tsaya ya saurari diyar tashi, ya saurari yaron ma but no duka baiyiba, look at all abubuwan dayake yi beating the boy, attacking him, saikace yana fada da tsaran wasanshi, har Yasmeen bai bari ba, dukanta yake, hawaye ta goge she's so bittered ahaka har sukakai anguwan su ga mamakinta motan Baba tagani yayi parking akofar gidansu yafito ya tsaya yana zare idanu yana kai koma, kana ganinshi kasan bakaramin tashin hankali yake ciki ba, hade rai tayi har sukakai kofar gida keken yayi parking, duba daya tazaro tabama mai keke ta sauko zata shige gida batare data kalli Baba ba karaf yarike mata hannu azuciye Ammi ta juyo tana kallonshi tace "wh bazance muna kofar gida ba zan kwasamaka mari idan baka saken mini hannu na ba" wani kalan kallo Baba yake mata gabanshi nafaduwa sosai baitaba ganin irin fushin nan akan fuskan Ammi ba, fizge hannunta Ammi tayi tawuce tashiga cikin gidansu inda taga Mahaifinta zaune atsakar gida kan tabarma dattijo ne ya tsufa sosai ga mahaifiyarta duk suna kallonta da alamu Baba yariga yashigo yamusu magana har ga Allah bataso tazo tatafama tsofaffin nan hankali ba but duk Baba ne yaja, ahankali tabude baki zatai magana hannu Babanta ya nuna mata babban dakinshi dake chan dayan bangaren yace "wuce kishiga ciki ki zauna mijinki yazo yayi magana dake banson kicemini wani abu, wuce kije badan taso ba ta juya ta shige dakin tabude tashiga ko minti biyu batayi da zama ciki ba Baba yabude kofan dakin yashigo tamaida kofan yarufe yajuyo yakalli Ammi dake zaune ko dagakai batayi ta kalleshi ba dasauri yazo gabanta kneeling yayi jikinshi ko'ina rawa yake yana kallonta cikin tsantsan hankali yace "dan girman Allah Maman Nana kirufamin asiri kizo mutafi gida kiyakuri" batare da Ammi tadagakai ta kalleshi ba tace "na tsani ganin ka Baban Nana, I hate halayyan ka, and I don't think zan iyacigaba da zama dakai dan dabi'unka sunsan na tsaneka gabaki daya, na bar maka yaranka duka da gidanka ka hada duka ka cinye" hannunta Baba yarike dasauri yana girgiza mata kai yace "wh wh na rantse miki kome nakeda shi aduniyan nan idan har babu ke bazan tabajin dadinshi ba, nasan inason yarana Maman Nana but idan baki tareda ni bazan ma taba samin natsuwan sonsu ba, nasan namiki laifi amman dan Allah kiyakuri" anatse Ammi tace "saikuma kayi kanka akeji idan kana tunanin hakurinka zaisa nabika kayi kuskure one thing dana sani shine bazan sake auren stubborn man arayuwana ba" dawani irin sauri Baba da gabanshi ke faduwa yace "me kike nufi da maganan nan dakikeyi, wani aure kike magana"? Cikin tsantsan rashin mutunci dan Ammi sotake ta gumamai tace "idan zan sake aure mana tunani kake narabu dakai zama zanyi? Har yanzu da kuruciyata da kyauna wani auren zan sakey..........' " Dawani irin sauri Baba yadaura hannunshi kan bakinta.Yanda Baba yadaura hannunshi kan bakinta zaka dauka zai nane bakinta ne, idanunshi sunyi jazur kaganshi saiya baka tausayi, duk yanda Ammi keji kaman ta cije hannun nashi kasawa tayi tasauke kanta ta daina kallonshi sabida kada yaga yanda yabata tausayi, gently Baba yazare hannunshi dagakan bakinta ahankali yadaura kanshi kan cinyanta kaman dan yaro, ahankali cikin lallashi sosai yace "nasan ban kyauta miki ba amman kiyakuri dan Allah I promise you zan chanza daga yanzu I will be listening to you tare zamu dinga making decision, please ki fahimce ni and look at things daga view dina, maisa babu wanda ke fahimta ta bana cikin hayyacina yaron nan yazo ya cutar damu gabaki daya jibi yanda ya maida Yasmeen, Yaya zanyi da raina ina zansa raina naji dadi"? Shiru Ammi tayi tana kallonshi saikuma chan tasauke ijiyan zuciya tace "Ibrahim" dago kanshi Baba yayi yakalli Ammi anatse Ammi tace "inaso kasani cewa ba'a zafafa tsana aduniyan nan, nasan yaron nan yamana laifi but yanzu kai laifin naka na neman ture nashi u are too harsh, you're being inconsiderate, kowa da kaddaran shi arayuwa kaje islamiyya kasan wannan, auren yaron nan da Yasmeen ka daukeshi amatsayin kaddara, ka zauna ka saurari diyarka let Yasmeen talk to you, Yasmeen ba yarinya bace, she's a woman, tasan metakeyi, she might not be brilliant amman Allah yamata nata baiwan, she's smart, soyayya is real dan haka kadena karyata nata, nima bagani ba Allah yajarabeni da son fitinannen mutum irinka dudda gaka ga halinkan nan" hannun Ammi Baba yarike gam kaman dan yaronta dake neman gafara murya chan kasa Baba yace "na tsani yaron nan ne yabata rayuwan Yasmeen, shekaru ashirin muna kiwon kamilan diyarmu rana daya yaron nan yazo ya rusa tarbiyan ya maida mana da diya bazawara, taya zan taba daina tsanan yaron nan eh"? Sosai Ammi ke kallon Baba dan from what she's seeing Allah ne ya aiko Maheer rayuwan Baba to teach him a lesson dan daga Baba har Maheer din sunada hali dayawa in common, ijiyan zuciya tasauke tace "tashi ka koma gida zan zauna anan for now nadan huta kafin nadawo gidanka" ga mamakinta hawaye tagani ya sauko daga idanun Baba yakankame hannunta arude yace "dan Allah dan Allah karkimin haka, wh wh wih kini na rantse har sau uku namiki alkawari bazan kara abinda nayibadan Allah dan Allah kirufamin asiri kizo mutafi tare pleaseeee kinji Maman Nana I am sorry" rufe idanu Ammi tayi tajuyar da kanta Baba ya bala'in bata tausayi, tashi Baba yayi dasauri yajawota ahankali zuwa jikinshi yadaura kanta asaman cikinshi yana bubbuga bayanta cikeda so yace "| know I've been hurting you kiyakuri kiyafemini yar aljanna I promise bazan karaba kinji, sorry my best" duk yanda Ammi taso kasawa tayi babu yanda tayi dole tahakura koda tazauna anan tunanin Yasmeen kadai bazai barta haka ta hakura tare suka fito Baba yakara musu wa'azi sannan sukai sallama suka tafi, wani super market Baba yakai Ammi yace kome takeso tadauka murmushi kawai tayi ta kwashi all abubuwan datakeso su atamapa da laces da turaruka yabiya kudi tsaf suka fito yasaya mata gasassun kaji suka yakoma mota yajuyo yakalleta yace "saikuma me kikeso"? Sosai Ammi ke kallonshi kafin anatse tace "inaso ka saurari everything Yasmeen has to say to you? Sit and talk to her idan Munje gida, can you do that kodako maganan mijin nata zata maka?" Gyadama Ammi kai Baba yayi yace "eh" koda sukakai gida dasauri Baba yafito yabudema Ammi kofa, fitowa tayi ahankali tawuce ciki direct dakin da Yasmeen take tayi kwance taga Yasmeen din akasa da alamu ma bacci bai dade da kwasheta ba danga ragowan hawaye afuskanta bala in tausayi Yasmeen take bata she just wish zata iya cirema yarinyar damuwanta, hannunta takai ahankali tadaura saman goshin Yasmeen din jikinta zafi dukan da Baba yamata ne, sallaman Baba yasa tadago kanta takalleshi hada idanu suka ahankali cikeda nadama yace "jikinta da zafi"? Sauke kanta Ammi tayi tareda girgixa mata kai, zuwa yayi yazauna kusada Ammi tareda dafa Ammi ahankali yace "I promise bazan kara daga hannuna natabata ba kinji" gyadamai kai Ammi tayi, anatse Baba yace "je daki bari ni natadata na kwantar da ita akan gado, jeki wanka kafin nazo" Ammi batai musu ba ta gyadamai kai tamike tafice daga dakin juyowa Baba yayi yakalli Yasmeen Allah ne kadai yasan yanda yakeson yaranshi barinma Yasmeen, ahankali yakai yatsanshi yashare hawayen dake kan fuskanta yayi shiru maisa Yasmeen bazata so mahaifinta kaman yanda shi yake sonta ba and support him? Me criminal boy din nan yamata? Maisa take sonshi? Why? Mesa takasa sadaukar da soyayyan yaron nan sabida farin cikin mahaifinta? Maisa kikeda taurin kai Yasmeen? Mamana bahaka takeba" Baba yay maganan ahankali yanasa hannu yadagota bude idanunta Yasmeen tayi ahankali ganin Baba saida tadan firgice tasake bude idanunta tarrr gabanta nafaduwa, ahankali Baba yawani kalan rungumeta tsamtsam baki yabude zaice sorry yakasa magana hawaye sun taru a idanunshi, murya chan kasa Yasmeen tace "Baba kayakuri kayafemini abinda namaka dazu, wh Baba ina sonka sosai, banda mahaifi irinka aduniya" dagota yayi daga jikinshi, ahankali yadagata suka mike tsaye da kyar ta tsaya da kyau kar Baba yagane sai yanzu taji kafanta namata nauyi duk yayi tsami, hannunta Baba yakama yazaunar da ita abakin gado yayi shiru yana mata wani kallon kallo ba wai kallon fushi ba irin kallon nan da lyaye kema yaransu dakesaka su feeling so guilty dayasa kawai Yasmeen taji she's feeling extremely guilty, iyayefa iyaye ne kuma sune sukasan kan yaransu. Anatse Baba ya nuna kanshi yana kallon kwayan idanunta calmly yace "Fateema kin zabi yaron nan sama da mahaifinki ko"? Dasauri Yasmeen ta girgizamai kai tabude baki zatai magana Baba yace "kul bafada nazo miki ba nazo nabaki hakuri ne" yadan sauke ijiyan zuciya, yakalleta yace "Fateema nayi Babban kuskure yau har ina dukanki duka abubuwan nan ina neman gafara agareki, kinsan d'a dan halas wanda ka haifa ka haifu shine kakeda iko dashi, shine wanda zaka iya daga hannu ka hukunta kacemai yayi yayi yabari yabari, yara nagari sune wayanda sukasan cewa fushin Allah nadaga fushin iyaye sannan yardan Allah nadaga cikin yardan iyaye, Fateema cikin yarana ku uku na fifita ki kan all of them amman yau kin bude baki agaban kowa kincema ni mahaifinki I am wrong!" Dasauri Yasmeen tabude baki zatai magana Baba ya girgiza mata kai yayi dan murmushi yace "baki kuskure ba l mahaifinki am wrong Yasmeen, ke Yasmeen y'ata you are right" yayi murmushi tareda kai hannunshi yashare hawayen dake zubowa daga idanun Yasmeen yayi murmushi yace "| promise bazan kara saki kuka ba dan haka wipe your tears Fateema, matsalan shine I expected so much from you Dan nadauka ke diya ce wacce zata cire iyayenta daga
Chapter 124 · 0% Book details