Sashe 24
Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Tun wajajen 4 da ita da Farida suka tashi kusan atare dakin Farida tabi da kallo sannan takalli Yasmeen, cikin sanyin murya tace “Anty Yasmeen har yanzu muna nan wajen”? Gyadama Farida kai Yasmeen tayi ahankali, dawowa kusada Yasmeen Farida tayi cikin wani kalan siga na hopelessness tasa kanta akirjin Yasmeen tai lamoo ahankali cikin wata kalan raunanniyan murya dake cikeda damuwa sosai tace “Anty Yasmeen tsoro nakeji sosai, ji nake ajikina kaman kashe mu zasuy….” Dawani kalan sauri Yasmeen tadagota tareda kai yatsanta kan lips nata rai abace tace “shush, don’t say that” takai yatsunta dasauri tashare hawayen daya gangaro dagakan idanun Faridan datakoma kaman wacce tai ciwo na shekaru dari tace “babu abinda zan bari yasameku sai inda karfina yakare, i will protect you and Nanah with my life, babu abinda zai sami kannina karkiji tsoro kinji, zamu koma gida I promise you, nasan duk inda Baba yake yana iya yinshi mukoma gida, we are all going home kinji Fariri” Gyadamata kai Farida tayi saikawai tasake shigewa jikin Yasmeen kankameta sosai tayi tana kuka ahankali mara sauti, duk yanda kuka kecinta saitaji ita takasa tahau bubbuga bayan Faridan ahankali ga jikinta yay zafi sosai kanaji kasan zazzabi ya shigeta, sun dade ahaka tacirota daga jikinta tace “zomuje muyi salla” daga Faridan tayi itama ta mike tsaye cikinta nawani kalan murdawa amman ta daure, bayi suka shiga Farida tafara fitsari tayi tsarki itama tayi sannan kowacce tai alwala bayan sun dirje bakinsu da hannu fitowa sukayi, Farida takalleta tace “dame zaki sallan Nanah tai fitsarin kwance a hijabinki damuka lullube dashi” ahankali tashiga warware kullin datama dan kwalinta awuya ta sake maida wani tace “da wannan zanyi ke kiyi da karamin dakikasa” sannan ta kabbarta sallan Farida ma ta kabbarta sukai salla sun dade kowanne addu’a yake Allah ya tsira dasu, pillow Nanah tayi da cinyan Yasmeen atare suka shiga karatun Al Qur’ani ahankali suratul Mulk sai wuraren 6 Nanah tafarka da lafiyayyen kuka kaman ana yankata dasauri daga Yasmeen har Farida sukai kanta hannunta Yasmeen tadaura akanta tana daukanta jikinta zafi itama damuwa sosai Yasmeen tayi tace “Nanah zazzabi kikeyi” cikin kuka da shagwaba irin na yara ta ture Yasmeeen tana sake ballewa dawani kalan mahaukacin ihu tace “Ammiiiiii, Ammmiiiiiii naaa” rasa yanda Yasmeen zatasa kanta yasa ta tsugunna agabanta tareda juyamata baya tace “Oya to hau baboo muje na kaiki wajen Ammi, Farida dauko kayanta abayi nasa mata mutafi” hawa bayan Yasmeen Nana tayi da sauri itakuma Farida tawuce bayi fitowa tayi takalli Yasmeen tace “kayan basu busheba kaman yanzu kika wanke Ma” ihuuu Nana ta tsala tace “ni ahaka zansa wajen Ammi zani” dasauri Farida takoma bayin takawo kayan karba Yasmeen tayi tana sauko da ita daga bayanta ga jikin Nanah zafi rau kaman wuta tace “Nanah kayan nan zasu kara miki zazzabi” fizge wandon kayan makarantan tayi cikeda rigima irin na yara tashiga sawa, tasaka rigan kan singlet na Farida dake jike da fitsari ajikinta itakuma Farida tawuce tadauki hijabi din Yasmeen takai bayi ta dauraye ta shanya aruwa tadawo dakin tana kallon yanda Yasmeen ke jijjiga Nanah dake kuka sosai abayanta tana kiran Ammi ita bama Nanah kebata tausayi ba Yasmeen kebata tausayi ita kadaine bataci komiba cikinsu tun jiya wani kalan mahaukacin bugo kofan dakinsu akayi dayasa dukansu suka firgita dagudu Farida tai tsalle daganan gaban bayi zuwa bayan Yasmeen itakuma Nanah ta dirko daga bayan Yasmeen din taboye abayanta itama kaman Farida tana rusa uban kuka, hakanan Yasmeen taji kirjinta nawani kalan extraordinary bugawa takalli kofan lips nata har rawa suke takai hannayenta tana kara kankame su Farida dasuka boye abayanta, bude kofan akayi wasu maza biyu da fuskansu ke arufe ga bindigogi ahannunsu suka shigo dawani lafiyayyen royal chair kaman irin kujeran sarkin nan suka ijiye kujeran nesa kadan dasu Yasmeen but kujeran na facing nasu, dayan yace “gyara zaman kujeran kada mubata ma Oga rai this early morning” gyara zaman kujeran sukayi suka juya suka fita dasauri batare dasun kalli su Yasmeen ba, sake kankame kanne ta Yasmeen tayi tana karanto duk wani addu’a data iya sabida yanda gabanta kewani kalan mahaukacin fadi daidai lokacin aka kara bude kofan wasu kattin maza wanda jikinsu kadai tagani tagane security ne su dudda fuskokinsu arufe but suna sanye da suit suma ga bindigogi a hannunsu sunyi charko charko sun kame jikin kofan daidai lokacin wani kafa dake sanye cikin black wando dayasha guga da black covershoe na Gucci dake kyalli yashigo dakin, dawani kalan sauri Yasmeen ta lumshe idanunta sabida wani kalan arnen sanyi dataji tanaji dahar saida hakoranta suka hade sukai kara kaman vibration grrrr!.
Kaman wani sarki yawani kalan tako yana tafiya dai dai yataho ya zauna akan kujeran da aka ijiyemai yay crossing kafa daya akan daya idanunshi sanye cikin wani baki kirin glass na police dabaka iya ganin idanunshi jikinshi danye da suit dayamai bala’in kyau yazauna ajikinshi kaman dan shi akai suit aduniya, tsayawa Wike, Nas da Dan duk sukayi abayan kujeran dayake zaune duka fuskokinsu arufe banda Wike duk suna kallonsu Yasmeen banda shi dahar yanzu bai daga idanunshi yadaura akansu saima zuba hannuwanshi dayayi saman hannun kujeran yay crossing legs nashi ta hanyar daura kafa daya akan daya.
Kaman wani sarki yawani kalan tako yana tafiya dai dai yataho ya zauna akan kujeran da aka ijiyemai yay crossing kafa daya akan daya idanunshi sanye cikin wani baki kirin glass na police dabaka iya ganin idanunshi jikinshi danye da suit dayamai bala’in kyau yazauna ajikinshi kaman dan shi akai suit aduniya, tsayawa Wike, Nas da Dan duk sukayi abayan kujeran dayake zaune duka fuskokinsu arufe banda Wike duk suna kallonsu Yasmeen banda shi dahar yanzu bai daga idanunshi yadaura akansu saima zuba hannuwanshi dayayi saman hannun kujeran yay crossing legs nashi ta hanyar daura kafa daya akan daya.