Sashe 127
Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsinewa kowani wanzaminema daya maka kaciya agidan yari da aka haifeka, ya feke ka da kyau, ya sulleyeta, shigayar abu sai shegen masifaffiyan dadi, shege dan iskan tijararen yaro kawai mai bura kaman doya" daya daga cikin security dasukazo yace "haka jiya yawuni akan wata yarinya datazo ma Hajiya" zaro idanu Hajiya tayi takalli security dayayi magana sauran security suka kalleshi suma irin mehaka kake fada, dasauri Hajiya tace "bawan Allah fadamin Maiya faru zan kara muku kudi wh kada kumai fada kubarshi dan girman Allah yafadamini yaro nane Pablo, my sugar boy" adan tsorace yana kallonsu yace "wata tazo jiya dayace matarshi ne suka tafi private room, wih Hajiya yanda yakecin yarinyar nan saida gabana yatashi danni ke gadin wajen jiya, tun safe datazo har yamma yisuke, kinji karan da dakin keyi kaman ana yaki ga gurnani dashima keyi kaman wani kura, amman ke sugar mommy shi ya akayi kika bari yafara son wata itama daga gani takasa hakura tabiyoshi gidan yari yamata aiko ya iya aiki" Yanda Hajiya ke kuka kaman wawiya wih jin Maheer yaci Yasmeen har ma anajinshi tana tunayanda karan cinta ke cika falon sama idan yanayi kishi kaman zai kasheta, wato yana nan gidan yari ita tanachan tana murna tarabasu ashe agidan yari ma cin abinshi yake dan iska jarababben jaro. Komawa dakinshi Maheer yayi yay kwanciyan shi akan gado tareda fuzar da iska, yarasa mesa gabanshi keta faduwa yakasa samin natsuwa aranshi sabida Yasmeen, alalace alalace ranan yawuni yakasa cin abinci saidai ruwa ruwa, dare yazo bai runtsa ba, washe gari yasha Lipton yana zaune shi kadai around 10 nasafe wasu security guda biyu sukazo da yan sanda biyu aka bude dakin hakan yasa yadago kanshi, Obama yagani dawani dan sanda, Obama yace "let's go yaune zaman kotun ku a shari'a court" hakanan Maheer jiyayi gabanshi yafadi ahankali yataso yafito yanama Obama dake rike da handcuff wani kallo, aka samai handcuffs din ahannunshi sannan suke wuce Obama yace "you seems to be enjoying new home dinka Mr Pablo Escobar" kallonshi Maheer yayi baicemai komiba yadauke kai ahaka suka fita bayan wani prison van aka sashi aka kulle sannan akaja motan, motocin yan sanda na gabansu da bayansu. ** 16:36 Wuraren 11 sukakai kotu ga yan media cike gaban kotun aka zagaye Maheer ana jejjefamai tambaya yan sanda naturesu aka jashi aka wuce dashi cikin kotu, yana shiga kotu yaga su Baba zaune duka family ga Yasmeen zaune kusada Baba tana sanye da maroon hijabi kanta akasa, dayan bangaren kuma su Baba ne da Hamad da Malah duk suna kallonshi dakuma mutane da dama dasuka cika kotun dabai sansu ba, dauke kanshi yayi yamaida kan Yasmeen da kanta ke kasa sai kallonta yake har aka wuce dashi inda zai zauna bata dago kanta ba, ya zauna kusada Ahmad lawyer shi Alkali na shigowa saida yay settling down sannan mai magana yatashi yace "yau an taru akotun nan mai albarka dan sauraron karan da Commissioner na Police Malam Ibrahim Ibrahim ya shigar a kotun nan kan wani kasurgumin danta'adda da akafi sani da Pablo Escobar wato Maheer mai harkan miyagun kwayoyi ya auremai diya yana neman kotu data raba auren dake tsakanin Pablo da diyarshi Fateema" yajuya yabama Alkali takardun, karban takardun alkali yayi ya dudduba na kusan minti biyu sannan ya ijiye komi yadago kanshi yace "mahaifin yarinyar daya shigo da kara yafito" mikewa tsaye Baba yayi dayaci manyan kaya ya kafa hula yafito yaje ya tsaya Alkali ya kalli Baba yace "kasan menene aure?" Anatse Baba yace "eh nasani" "kasan hukunci aure"? "Eh nasani" Baba yabada amsa with full confidence, Alkali yace "menene dalilin ka nasaka wannan karan maisa bakabar diyarka tasa karan dakanta ba"? Dasauri Baba yace "nine mahaifin Fateema, nasan menene alkahiri agareta menene shairi gashi gashi, 16:36 nasan menene guba arayuwanta nasan menene abu mai kyau........" Baba yabada labari daga farko har karshe yanda Maheer yashigo rayuwansu ya aure diyarsu Alkali duk ya saurareshi baiyi interupting ba, yakarake da "akanwani dalili zata zauna da auren wanda aka yanke ma hukuncin kisa agidan yari?" 16:36 Sosai Alkali ke kallon Baba kaman maison karanta wani abu game da Baba sannan yace "jeka zauna" wucewa Baba yayi yaje yazauna ranshi fess, anatse Alkali yace "Fateema tafito" dago kanta Yasmeen tayi ahankali gabanta na faduwa jikinta yahau rawa da sauri Baba dake kusada ita yadafata yana kallon kwayan idanunta yamata whispering akunne "jeki karkiji tsoro duka abinda nafada miki zaki fadi kinji"? Gyadama Baba kai Yasmeen tayi ahankali sannan tamike tsaye kanta akasa tawuce taje ta tsaya Maheer sai kallonta yake kaman zai hadiyeta da idanu amman taki yarda ta kalli ko inda yake, saida akasa ta rantse sannan anatse Alkali yace "ya sunanki? Shekarunki nawa? Introduce kanki" Anatse Yasmeen tace "sunana Fateema Ibrahim, shakarana 20yr, ina NCE 1 a FCE inda nake karanta Islamic studies Education, sannan ina aikin catering" 16:36 kallonta Alkali yayi in the eyes yace "kimanin wata nawa kenan dakikasan mijinki Maheer daga lokacin dayay kidnapping naki zuwa yanzu kusan wata nawa kenan?" Ahankali Yasmeen tace "kusan wata hudu kenan zuwa biyar" rubutu Alkali yayi yace "kimanin tsawon lokutan nan yataba cutar 16:37 dake daidai da sau daya? Mari, duka, zagi Kodai wani abu na cutarwa yataba miki?" Girgiza kai Yasmeen tayi ahankali tace "a'a baitaba cutar dani ba" rubutawa alkali yayi sannan yace "da gaske threatening naki yayi ya aureki?" 16:37 Shiru Yasmeen tayi kanta akasa takasa magana, babu alamun wasa Alkali yace "bani amsa kina batamin lokaci"? Dago idanunta Yasmeen tayi ahankali takalli Baba da idanu yamata magana hakan yasa ahankali takalli Alkali tace "eh" lumshe idanu Maheer yayi ahankali, duk Alkali na lura da komi dake faruwa cikin kotunshi, yace "meya cemiki?" 16:37 Hawaye ne suka zubo daga idanun Yasmeen ahankali tace "yace idan ban aureshi ba saiya kashe Mamana da Baba na da duka family mu" Alkali yayi rubutu sannan yakalleta yace "bayan aure yataba tursasa ki kinyi wani abu? Ya kula da ke da so da girmamawa koko ya wulakanta ki yaci miki mutunci"? 16:37 Sake kai hannunta tayi ta share kwallan daya zubo mata sannan tabude baki zatai magana Alkali yakira sunanta Fateema! Dasauri takalli Alkali, Maheer yanuna mata da yatsa dake azaune yace "kalli mijinki Maheer kibani amsan tambayata" ko kadan Yasmeen bataso kallon Maheer ba, jyan zuciya tasauke sannan tasauke idanunta kanshi ahankali kwayan idanunsu suka hadu idanunshi sunyi jaaa looking weak, fragile, scared, and very very sad, 16:38 dasauri takai hannunta biyu duka tadaura kan fuskanta tadan fashe da kuka tace "dan Allah Alkali karaba auren mu kawai ni abinda nakeso kenan banson wayan nan tambayoyin, ni bana sonshi araba auren mu, ya sakeni" wani kalan washe baki Baba yayi Yasmeen tagama biyanshi duniya da lahira yau, ahankall Maheer 16:38 yasauke kanshi kasa jikinshi yayi wani kalan mugun sanyi for the first time arayuwanshi gabaki daya yau saiyaji yabama kanshi tausayi sosai, Alkali yadade yana rubuce rubuce sannan yadago kanshi yakalli Yasmeen yace "tafi kije ki zauna" yakalli Maheer alamun shima yazo hakan yasa Maheer yatashi ahankali jinshi yake kaman zai fadi jikinshi babu karfi ko kadan yawuce ya tsaya shima yayi rantsuwa sannan Alkali yace "maisa kabiyo ta basaja ka auri Fateema"?. Anatse Maheer yana kallon Alkali yace "sabida ina sonta!" Alkali ya gyara zaman glass din idanun kan idanunshi yana kallon Maheer yace "sabida kana sonta saisa zakace mata saita aureka koka kashe iyayenta kayi threatening yarinyar ka tsorata ta ka aureta" dan ijiyan zuciya Maheer yasauke yace "idan da naso alokacin Alkali zan iya kidnapping Fateema na dauketa babu wanda zai kara ganinta!" Yay maganan yana kallon Baba dake kallonshi Maheer yace "amman banyi hakaba, sabida soyayyan danake mata was true, ni karan kaina bantaba sanin zanso diyar wanda ya kwacemini kayana ba, diyar wanda ke nemana ya kulle ni ba, bantaba son wata aduniya Sai Fateema! Nasan waye mahaifinta inda ace nazo a criminal dina kozan mutu bazai taba bani aurenta ba kumani sonta nake da aure ba da fasikanci ba saisa nazo a basaja ya dauki auren diyarshi da kanshi yabani, inda nazo a criminal bazai taba bani aurenta ba!" Haba zokaci kananun magana kus kus kus a kotu yana kallo wasu na cewa hakane, wasu ma cewa soyayya batasan kowa ba kokai boka ne ta tashi kamaka kamaka zatayi, saida akai order sannna akai shiru, Alkali dake kallon Maheer yace "iyaye nada ikon zabama yaransu mazaje nagari, kowa yasan cewa kai kana harkan miyagun kwayoyi tabbas babu uba nagari dazaiso yahada aure dakai" Baba har wani gyara zama yayi yana murmushi Alkalin nan na faranta mai rai, juyowa Maheer yayi yakalli alkali in the eyes yace "sana'ar mutum, aikin da mutum keyi baya tantance kai nagari ne kokai ba nagari bane, zuciya itace komi na mutum, zuciya is what defines humans, amatsayin mu na mutane bazamu taba iya cewa wannan mutumin arziki bane sabida yana aikin kwarai wannan shaidan ne sabida yana aiki marakyau agaban mu, Allah kadaine yasan komi, akwai wacce ta taba kallona dudda ina saida kayan shaye shaye da sauransu tacemin you are a good man Maheer!" Yadanyi shiru tareda yin murmushi Yasmeen taji jikinta yay sanyi dan tasan ita yake nufi, anatse Maheer yace "itace mutum na farko dana taba haduwa da ita arayuwana da bata kalleni amatsayin drug dealer ba she looked at me for me, ni, asalina, Maheer and that person is my wife! Fateema!" Gangarowa Hawaye sukayi daga idanun Yasmeen dasauri ta sharesu da bayan hannu, anatse Maheer ya sauke ijiyan zuciya ya kalli Alkali yace "yallabai I'm not trying to be rude, but akwai abinda ake cema kaddaran rayuwa" yasakeyin shiru tareda lumshe idanu yace "bakowa aka haifa da silver spoon abaki ba, and bakowani yaro bane is as lucky as matata Fateema da Allah yabata iyaye that can go to any limit to protect and guide her sannan su zaba mata what's best for her!" Maheer yadan fuzar da iska yadan dakata da magana dan he's getting too emotional yau yana soso inda kemai ciwo wani bangare na rayuwanshi da bayaso yayi magana akai, ahankall Hamad ya share hawaye yana kallon Maheer kotun akai shiru ana kallonshi hatta shi Baba for the first time ever sai kawai yaji wani iri aranshi da maganan da Maheer yayi