← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 141

Sashe 71

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wani kalan rawa jikin Hajiya keyi wlh kaganta zaka iya dauka da gasken gaske ta samu cutan farfadiya ne, ga iPad din dake hannunta data kunna da bama takanshi takeba tunda taji muryan Yasmeen, jikinta ko'ina na bari bar bar bar tana kallon wayan dayake kasa ya tsatsage, wani mugun kallo Maheer yamata kafin ya fito yazo har gabanta tsungunawa yayi kasa hannunshi yadauki wayan yakalli screen din sabon number shi yaga ta kira wayan dake hannun Yasmeen ga Yasmeen akan layin, ko dar Maheer baiji ba dan shi idan akwai abinda baidashi a duniyan nan shine tsoro yakai wayan kunnenshi daidai Yasmeen nakara cewa "Hello" ahankali, har cikin tsakiyan kirjinshi yaji muryanta baisan lokacin daya lumshe idanunsa ba, cikeda so da kulawa da kuma tattausan murya ta yanda kana gani kasan da abu mai mahimmanci yake magana yace "I'll call you back" yazare wayan daga kunnenshi tareda katsewa sannan ya mike tsaye yajuyo yakalli Hajiya dake wani irin kallanshi jikinta na rawa, hannunshi yakai yakarbe iPad dinshi dake hannunta sannan ya juya yawuce closet abinshi Hajiya na binshi da idanu, duka hannayenta Hajiya tasa ta mammari kanta kafin ta wuce bayinshi da gudu tabude pampoo ta tara ruwa tana watsawa a fuskanta tana wani irin sauke ajiyan zuciya kaman wadda take shirin suma. Takai kusan 2mins tana haka sannan tajita tadawo daidai tafito daga bayin tai closet dinshi dagudu , bude kofan tayi tashiga daidai ya gama saka wando yana saka singlet kallo daya yamata yadauke kai yacigaba da abinda yake, cikeda tashin hankali Hajiya tace " wacece wacce tadauki number nan Dana kira Pablo?" Shiru ya mata baice kalaba yadauki T-shirt dinshi fari yana sakawa, wani irin bakin kishi ne ya turnuketa tace "Pablo who is dat gurl daka kira around 5 na asuba yanzun nan kuma Kane cemata u will call her back, wacece?" Juyawa yayi yadauki turarukanshi yana fesawa one by one kaman bazaiyi magana ba sai kuma yajuya yadan kalleta kafin ya dauke kai yace "you don't have to know wacece and this should be the last time da zaki kara taba min waya" karasa shigewa cikin closet din tayi tazo inda Maheer yake tsaye idanunta sunyi jazur tace "Pablo dawa kake magana haka? Koni baka 10min kana waya dani, wacece it's?" Shiru yamata daidai yagama fesa turare juyawa yayi zuwa wajen takalman shi yaciro wani flat shoe yazuba akasa yasa zai wuce dasauri Hajiya tasha gabanshi yanda take jin kaman zata zare yasa ta wani kalan fashe da kuka gwanin ban tausayi tace "Pablo budurwa kayi eh? I thought nine komi baka, nine rayuwanka, Pablo kasan yanda na tsani naga any mace atare dakai that's the reason har yau har gobe bamu taba daukan ma'aikata mata ba, ban isheka ba Pablo mezakayi da wata, babu wacce zata taba sonka kaman ni, Pablo dan ALLAH ka rufa min asiri my heart cannot take it naga kana magana da wata dan ALLAH, kaji tausayina wlh Maheer zan iya mutuwa idan kafara son wata sama dani aduniya kaji my baby" dan yatsina fuska Maheer yayi kaman wani abu ya shigeshi instead of yaji tausayin Hajiya yanda yakeji da idan tana kuka jiyayi he's feeling irritated yatsina fuska yayi strictly yace "tashi agabana zan fits" yanda gaban Hajiya ke fadi zaka dauka zuciyanta is about to fail ne ganin yanda ko tausayinta ma Maheer baijiba kaman yanda yakeyi idan tana kuka ada, girgizamai kai tayi tace "kozan matsa saika fadamin wacece kake waya da ita" "is none of your business maryam! Allow me to live my life!" Maheer yayi maganan ranshi a bace, cikin bala'in zafin zuciya yace "tashi agabana" adan tsorace ta matsa daga gabanshi tana wani irin nishi wucewa yayi ya fice abinshi yay hangar kofa daidai yasa hannu zai bude kofan dakinshi yafita yaji karan faduwan abu dimmmm! Chak ya tsaya kafin ya juyo da sauri yakalli kofan dakin closet din Wanda half dinshi yakenan abude kafafun Hajiya ya hango kwance a kasa suna shaking sosai, dawani kalan sauri Maheer yay closet din yabude kofa ya shiga Hajiya ya gani kwance akasa idanunta sun kakkafe tana struggling tayi numfashi dawani kalan sauri yay wajenta tsugunawa yayi yadagota da sauri yama rasa mezaiyi ahankali ya jijjigata yace "maryam maryam" tashi yayi da sauri yawuce yafita daga dakin ruwa yadebo yazo ya kwara mata still taki dawowa she's having heart attack idan baiyi rushing nata to hospital ba zata iya mutuwa, tashi yayi dasauri ya dauketa yasauka da ita kasa wajen motanta yaje sai lokacin yama tuna key, ajiyeta yayi kan kujera yawuce ya koma cikin gida zuwa dakinta key motanta yadauka yasauko yadauketa yasa ciki yakoma gaba yaja motan da mugun gudu, yana kaita asibitin su aka wuce da ita emergency tsayawa yayi tareda dafa kanshi kawai yayi shiru he don't even know what to do again.
Chapter 71 · 0% Book details