← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 141

Sashe 9

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan sau uku Sa’a takaranta mata page 10 din kafin tabata handout din tace “to hada bakin ki karanta naji, kinga kun kusan fara first semester exam gashi bakince malamai kusan 4 ke muku course din ba kuma kowanne da nashi Yasmeen yaya zakiyi wannan na mutum dayane cikinsu yanzu kike page 10, wannan page 10 din nan kadai zai iya daukanki 10days kafin ki gama iyawa ki gama gane spelling da komi wai karatun nan dole ne, ki hakura ki barshi, karatu is not for u Allah bai baki kwakwalwan bane ba kawai, ki sami Baba ki sanar dashi kada kiji tsoro wlh” mayun gray eyes nata Yasmeen tazuba ma Sa’a tanajin wani abu nataso mata daurewa tayi ahankali tace “nidai in karanta kiji mini”? Ijiyan zuciya Sa’a tasauke zuciyanta namata badadi sabida yanda taga Yasmeen na wahala da karatu tace “karanta naji to tunda ke Allah yamiki bakin zurfin ciki” anatse Yasmeen tafara karatun, yanda take hada words da kyar tana fadi zaka dauka yar primary 1 ce, layi biyu tayi masu kyau takakare at the 3rd line wajen kalman Jahillya period, tashi Sa’a kawai tayi tace “nima zanje nai wanka inada lectures 11 gwarake Baban ki yanzu zai wuce dake ya kaiki ni saidai nahau mota, better think about abinda nafada miki and meet Baba da maganan” binta da kallo Yasmeen tayi harta fice daga dakin kafin ahankali tadawo da kanta takalli littafin idanunta kan kalman data kasa fadi, yatsanta tadaura kan Ja din ahankali tace “ga…..no ja is JAAAA” tai shiru tana kallon Hi tace “Hi, kaman hi din hello kenan yauwa ai nasan hi” shiru tayi tana kallon LI, itafa duk words dazata gani ta iya karantawa to tazauna ta haddace spelling din ne tasan yanda ake kiran word din, irin su Apple, cup, house, happy, da sauran kalamai da makaranta yasa ta zauna ta koyi spelling din ta haddace other than that ko she yanzu karubuta mata inhar bata taba zama da takoyi kalman ta iya shi ba to kafin ta iya pronouncing she din nan aiki ne babba agareta.
Labulen dakin aka daga hakan yasa tajuyo dasauri Baba ne yayi wani irin kyau yasa goggagun uniform, yana kallonta yace “da hijabi mutafi” gyadamai kai tayi tamike tawuce sip wani pink gogaggen hijabi tadauka tasaka dake kaimata har kasa tadauki jakan zuwa aiki da flat takalminta najiya tasaka sanan tafito, su Ammi dake tsakar gida sukace “adawo lafiya” gyadamusu kai tayi Nana tabiyota har gate tace “Anty Yasmeen yauma ki kara kawomini tsaraba” wani kalan murmushi Yasmeen tayi sannan ta duko hancinta taja tace “Nanani na ta iya kwadayi ko shikenan zan kawomiki” washe baki Nana tayi tana tsalle tareda mata bye bye ta kwala ihu tace “Baba bye bye” bye Baba yamata yana murmushi shima.

Har gaban shagon Maman Intee ya ijiyeta sannan yaciro 1k a aljihun shi yabata yace “gashi idan kin tashi kikaga babu keke ki koma ki zauna call me da wayan Maman Intee zanzo na daukeki kada ki kara takowa daganan har gida is risky kinji” gyadamai kai tayi ahankali tace “to Baba” tasa hannu zata bude kofar kaman daga sama taji Baba yace “me da me kuke bukata”? Dasauri tajuyo ta kalleshi tana zaro manyan fararen idanunta masu bala’in kyau, maimaita tambayan Baba yayi yace “medame kuke bukata keda yan uwanki”? Ahankali tace “ai Baba munada komi kasaya mana last month” takalmin kafanta yakalla yace “baki bukatan takalmi” murmushi tayi akunyace tace “eh inaso Baba” ahankali yace “dame kuma” kanta tasauke akasa cikeda ladabi tace “inaso na dinga hijabi sabo wayan nan sun tsufa wasu iron ya konamin, Ya Sa’a kuma ita jakane da takalmi da turare, Farida ma haka, sai Nana ita ribbon takeso da dankunne” jinjina kai yayi yace “shikenan tafi” gyadamai kai tayi cikin cool voice nata tace “Baba Allah ya tsareka yakara daukakaka Allah bada sa’a yakawo rabo Mai albarka” murmushi yayi yace “Ameen diyar Baba kema Allah miki albarka” murmushi tayi sosai tace “Ameen” sannan tabude kofan motan ahankali tafice tawuce ciki, saida Baba yaga shiganta sannan yajuya motan yawuce tareda ciro numbershi yay dialing number Ammi, wayan na gab da katsewa tadauka, strictly yace “yaran nan sun tafi school”? Ahankali tace “Farida ta tafi” “Nanah fa” Baba yay maganan bawasa, bayabo ba fallasa Ammi tace “naga yau Thursday danace ne kawai abari monday sai takoma gabaki daya tunda bataje tun ranan monday ba” shiru yayi kaman bazaice komiba saikuma ahankali yace “banson kina mini ganganci da karatun yarana, sabida kinga ina rigasu fita shine zaki dinga barinsu bazasu makaranta ba, Allah kaimu gobe I will personally take them to school” cikin kunkuni Ammi tace “kanada lokaci ne ai saisa” cikin fushi Baba yace “me kikace” dasauri tace “ni bada kai nai magana ba” dan murmushi yayi, cikeda son su shirya danshi baiso yana fada da matarshi yace “inda dani kike dana juyo motar nan back nadawo gida nabaki hukunci mai kyau” kaman jira Ammi take tace “bani kama mugunta jiya ba” dan murmushi yayi yana shiga cikin police headquarter nasu da aka budemai gate yace “haka akema mata mai tsiwa” dan murmushi kadan Ammi tayi dayaji sautin murmushin hakan yasa yaji hankalinshi ya kwanta sosai ahankali yace “ina sonki sosai Maryam kinsan da haka ko”? Gyadamai kai Ammi tayi kaman yana gabanta jiki asanyaye tace “nasani” ahankali yace “haka kuma inason yaran dakika haifamin aduniyan nan sosai Maryam” murya chan kasa tace “I know” kashe motan Baba yayi yace “dan haka inaso kome kowani decision zan dauka akansu ne supporting me okay, banso muna fada akan yaran nan” ahankali tace “shikenan bazan karaba” murya chan kasa Baba yace “kada ki kara kiran Yasmeen da dakikiya” tasan maganan nan yafi komi tabama Baba rai hakan yasa tace “kuskurene I promise bazan karaba Baban Nanah” murya chan kasa yace “good! Kemin list na abubuwan dakukeso all ki aikamin tawaya, bari naje na zama CP Commissioner Ibrahim Ibrahim mijin Maryam koba hakaba” kwashewa da dariya Ammi tayi ta wayan tace “hakane bari naje na kunna news na kalla” dan dariya yayi yace “to na barki lafiya” ya katse wayan yana murmushi feeling so happy and at ease nothing beats a happy family, his whole entire family is his everything, he literally lives for them now he can go and collect stars nashi cus he know cewa he deserves it, he’s such a dedicated hardworker both in his field and in this house yay maganan yana fitowa daga cikin motanshi.

EXCLUSIVE IS 5k
GGM IS 1k
Kindly pay into 3107021073 Aisha Muhammad first bank
✨KYALKYALIN KAUNA✨

EPISODE 5️⃣

✍🏻M SHAKUR

Saukowa yayi daga stairs ranshi duk abace daidai gaban office dinshi ya tsaya batare dayama security wani kyakkyawan kallo ba yace “tell my driver to get the car ready zan fita yanzu” yana maganan yabude office nashi ya shiga, security daya yabiyoshi cikin office din, wasu keys yadauka a drawer da wayanshi yawuce akufule yace “get the coke let’s go” daukan cocaine nakan table dinshi security yayi yakashe wutan office din sannan yafito daga office din yabi bayan Maheer dake tafiya kaman sarki yashiga lift fita sukayi daga club din already wata arniyan bulletproof Chevrolet Suburbans jeep na kampanin Inkas baka na gaban entrance din danshi kwata kwata baya hawa motan daba bulletproof ba for security, ga wasu bodyguards dake sanye da suit su hudu tsaye gaban motan suna ganin Maheer budemai bayan motan akayi kaman wani gwamna yafito hakan yasa yashiga dasauri ya zauna aka maida kofan aka rufe shikuma security ya tsaya kikam yana jiran Maheer da coke a hannu, kusan 1min Maheer yadauka kafin asauke glass din bayan leko da kanshi Maheer yayi hannunshi rikeda Cuba Aliados cigar wanda kudin shi kadai ya ishi mutum yasai manyan filaye kusan guda goma dan irin tulikin designers taban nan ne da turawa kesha mai Aromas na creamy oak, leather, fresh brewed coffee, tobacco, earth and sweet bread emanate from the wrapper, along with a small amount of citrus peel buso da hayakin yayi awaje ahankali yace “you see those two guy over there” yama security pointing gaban wani Brabus jeep dawasu samari biyu ke tsaye suna magana yace “give it to them” cikeda girmamawa yace “yes sir” ahankali yakoma cikin motan tareda jinginar da bayanshi ajikin motan yana lumshe ido yana huro hayakin taban, almost 2min yayi ahaka kafin murya chan kasa yace “what says the time Dan”? PA dinshi dake gaba kusada direban ne shima yana sanye da bakin suit yakalli agogon hannunshi calmly yace “is 3:45AM Sir” ahankali yace “and what is my schedule”? Wani iPad bodyguard din yadauka tareda dannawa sannan Anatse yace “kanada meeting da wannan senator by 4:15AM” wani kalan gajeren tsaki yaja har lokacin bai bude idanunshi ba, kaman wanda magana kema wahala yace “then what”? Bodyguard dake kallon pad din yace “1hr dama kace zaka bashi, immediately after that kuma kanada zoom meeting da head na distribution department namu na Lagos dakuma Delta, sunce akwai shortage na staff dan yanzu end users sun soma yawa” kaman wanda zaiyi bacci yace “can I cancel the meeting Dan”? Dasauri bodyguard kuma PA din daya kirada Dan yace “no sir you can’t, meeting din is very important unless zakai flying gobe kaje duka state din kai magana dasu” yatsine fuska Maheer yayi yace “naaah I can’t” dan ijiyan zuciya yasauke yace “I guess I will take the meeting then, let’s go” yay maganan yana zaro taban daga bakinshi daya gamasha anan kasan mota ya yar ko ajikinshi idanunshi a lumshe kusan tafiyan 40minutes sukayi, sannan suka yanki wani daji almost 20min drive sukayi kafin su kai wani babban gida gari guda Mai bala’in kyau, gate wani soja yabude musu sukaja motan ciki, wasu motoci guda biyu wanda suke pake abangaren wajen parking na baki yasa yagane senator yazo.
Chapter 9 · 0% Book details