← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 141

Sashe 118

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

miliyan goma goma su uku bisa ga tsorata damuwa da kunci firgice da emotional stress dayasa yaran suka shiga, kotu tazo karshe" alkali shiga, kotu tazo karshe" alkali yabuga ganga, Hamad ya rungume Baba gamgam yasaka fuskanshi akirjin Baba hot tears na saukomai jin an yankema Maheer hukuncin kisa, Malah ma idanunshi sukai jazur zuciyanshi kaman zata fito, Baba yataso har zuwa gaban Maheer da ake sama ankwa a hannu za'a wuce dashi yakalleshi yay murmushi yace "only death shine abinda wanda ya wulakanta rayuwan diyata yay deserving, our case bai kare anan ba kajira sammacin sakin y'ata daga shari'a court!" Dawani kalan sauri Maheer yakalli Baba gabanshi yawani kalan mugun fadi dum!. [8/13, 10:56 AM] SAFIYYA: Tunda abin nan yafaru Baba baitabajin joy, wato tsantsan dadi da satisfaction aranshi ba irin yanzu ganin fear karara akan idanun Maheer wucewa yayi yana murmushi zuciyanshi fara kal yatafi wajen su Ammi da Baffa da duk ke tsaye suna kallon Baba, Hamad bakin ciki yasa yajuya fuuuu yafice daga kotun Maheer dake kallon Baba aka karasa saka mishi ankwa aka wuce dashi aka sashi a motan dazai transporting nashi to kuje prison Abuja. Suna kaiwa prison din aka fito dashi daga mota aka kaishi wani office aka bashi kayan yan prison riga da wando yasaka aka karbi komi nashi aka kaishi wajen hoto aka mimmishi hoto saiga Prison Warden nasu yazo mai suna Emaka Philip Magana, yana ganin Maheer yayi wani dariya yace "welcome home Pablo Escobar, na tabbata u will sure have a good time anan, is home Handsome guy" kallonshi Maheer yayi daga sama zuwa kasa yay shiru aka bashi takalmi da socks yazauna yasaka sannan security suka rikeshi Warden yace "lemme do you the honor dole nakaika dakinka dakaina yau munada babban bako in our luxury home" yay gaba ana biyo da Maheer abaya, suna shiga bangaren da inmate suke aka fara ihu ana jijiga kofofin dakinsu na karfe ana. "Pablo Pablo Pablo!" Warden yajuyo yakalli Maheer dake biye dashi abaya yace "Woww nadade banga wanda inmate sukama wannan great welcoming party din nan ba duk sun ganka a tV news, you're a celebrity" saikuma Warden ya tsaya yadaga murya yana tafi kaman agbero yace "let's welcome the famous Pablo Escobar, an kama mana drug kingpin" haba zokaji ihu da buge bugun karafunan kofa, Warden yace "and he's here for life atafa mishi" zokaji tafi da dariya da ihu duka Maheer duka yabisu da kallo kafin Warden yacigaba da tafiya har zuwa wani daki C-40 aka bude bunk hudu ne adakin, ga mutane uku cikin dakin Warden yace "say hello to Rommie ku babban kaya nakawo muku fa Pablo Escobar dakanshi" tashi yan dakin sukayi kagansu irin yan daban nanne duk suka kalli Maheer sukace "yataho mana da eh ya ne"? Warden yace "ba eh ya ne anan kuma kunsani" yakalli Maheer yace "shiga" ciki Maheer yashiga ahankali sannan yajuyo yakalli Warden in the eyes shima warden yakalleshi na kusan 5secs sannan yay murmushi yanuna bunk din sama dayake empty yace "ga gadon ka nan, by 3:30 zaku fito aci abinci masu salla suyi, akwai ayyuka kaman aiki a library, clinic, wanke bayi, aikin kitchen, mechanic, walda, laundry da sauransu idan kafito za'a kawoka office dina ka zabi one, and be watchful sabida anmaka great welcome din nan baya nufin ana sonka celebrity a prison means yanzu haka akwai huge bounty akanka so be smart and be vigilant" yay maganan yajuya yafice aka kullo kofan dakin da key. Bin dakin Maheer yayi da kallo yayi shiru inmate din sai kallonshi suke daya daga cikinsu yace "Oga yau da gobe ne zaka saba da dakin" ijiyan zuciya Maheer yasauke yataho ahankali yahau bunk nashi na sama ya kwanta ahankali yana yatsine fuska dan jikinshi duka ciwo sukemai dan ciwuka ne ajikinshi sosai, ilyan zuciya yasauke tareda lumshe idanu Yasmeen kawai yake gani Yasmeen ce his biggest matsala yanzu, kawai dan shi namiji ne kuma yanada dauriya da yanayin dazai shiga zaimafi na Yasmeen sau dubu, yayi so deep a thought aka bude kofa yaji hayaniya bunkie shi yataso yace "muje break muyi salla" kallonshi Maheer yayi ga tabon salla agoshi yaron saukowa yayi suka fice suka jera shida yaron sai kallon Maheer ake wasu some na hararanshi ahaka sukaje wajen alwala yi sukayi yau salla sannan suka tafi dinning abincin da ake rabawa ya kalla a tray wasu teba da miyan agushi da nama yatsine fuska yayi yajuya zai fita daga layin dasauri wani yarikemai hannu yace "dan Allah Pablo idan bazaka ci ba ka karba kabani" bin wanda tarikemai hannu Maheer yayi da kallo dasauri ya fizge hannunshi yajuya dasauri karban abincin yayi yajuyo yabashi yawuce yaje yazauna yay shiru akahau dariya hakan yasa yadago kanshi daidai nan wasu security sukazo let's go, tashi Maheer yayi yabisu abaya har zuwa office sun Prison Warden. Bude kofa sukayi Maheer yashiga suka jawo kofa suka rufe, Warden na zaune kan kujeran shi ga taba a hannunshi ya kunna yarike yana kallon Maheer din daya shigo, Maheer yadan tabe baki yakaraso gaban table din instead of yazauna akan kujera zama yayi kan table din yamika hannunshi cikeda iskanci ya karbe taban dake hannun warden yakai bakinshi yazuka sosai sanan yacire tareda juyowa yabuso hayakin saitin fuskan Warden dake kallonshi irin kallon we we dinnan sannan Maheer ya ijiye karan taban akan ash tray tunawa da Yasmeen, yasauka dagakan table din yazauna kan kujera yadaga kafafunshi yadaura kan table din yana karkada kafa yana kallon Warden dayay wani dariya yace "wai kasan dead sentence ne akan ka kuwa shegen yaro amman ko ajikinka" wani kallo Maheer yamai, cikin murya irin na criminals din nan yace "I need security, I need a phone, I need good food, sannan ina bukatan comfortable single room, ina bukatan VIP treatment name your prize" wani kalan murmushi yana kallon Maheer din yace "Pablo, Pablo, trust me bazan baka VIP treatment da araha ba dan kai babban kaya ne all eyes are on you, bakaramin dadi naji ba da aka kawomini kai gidana" shiru Maheer yayi yana kallonshi batare dayace komiba, Warden yace "all eyes are on you for now bazaka iya accessing single room ba sai nan da kwana biyu, but waya, abinci mai kyau, security da sauransu bakada matsala awannan, all the guards are my boys babu wanda zai takuraka rest assure, u can make call agaban kowa bazasu ce komi ba katashi biyan kudi harda nasu zaka biya, a dollars nake karban payment" lumshe idanu Maheer yayi yana kallonshi alamun yana jiran price, washe baki Warden yayi yace "zaka biya $100k" babu ko gezau Maheer yace "I will arrange it bani waya" hannun Warden har rawa yake yadauki wayanshi yabama Maheer yace "yi amfani da wanan kafin anjima akawo maka sabuwa da SIM card naka" karban wayan Maheer yayi yasaka number Malah aciki, yay dialing ringing daya Malah ya dauka shir kadai da Maheer yayi yasa Malah yace "Oga it's you" anatse Maheer yace "code Z-0-0-M-7" anatse Malah yace "delivery address Oga" zare wayan Maheer yayi daga kunne yabama Warden yace "delivery address" hannun warden har rawa yake yakarbi wayan yabada address nashi sannan Ya katse wayan take yanke yakira yasa aka kawoma Maheer lafiyayyen abinci tsakuran abincin kawai yayi shima just to get energy ne but he's not enjoying anything yaci, sai bayan yayi har isha'i yakoma dakinshi da wayanshi sabuwa gal Nokia karama rakani toilet da agidan yaro tafi Iphone tsada kwanciya yayi akan gado yayi dialing number wayan daya bama Yasmeen amman shiru bata shiga ijiyan zuciya yasauke yayi shiruu tareda juyawa yakifa cikinshi sabida ciwo dayaji yafara yadan lashe lips nashi dan abin namai kaman suna saman kan boobs din Yasmeen, sosai yake kokarin koran imagination din dayakeji amman yakasa wani mugun tashi gabanshi yayi yadan saki malalacin kara what's wrong with him haka? Jikinshi baisan yana prison bane? Wannan wani kalan bakin bala'i ne, yaj tsaki yakai hannunshi takasa yakama gabanshi yarike gam ko zata kwanta, yadinga juye juye yarasa inda zaisa kanshi kaman wanda akama baki bala in sha awa yakeji kaman zaici kanshi da kanshi Allah yasa wutan dakin akashe dan duk wanda yaganshi zaiga yanda gaban wandonshi ya bala'in tashi.Wasa wasa yau satin Maheer daya a prison! Ya bala'in rame kuma abu biyu keta raman dashi tunanin Yasmeen da mugun sha'awa dake haddasamai ciwon ciki, dan saida yakai kanshi clinic na prison din dakanshi, Dr daya dubashi saida Maheer yabashi tausayi allura yamai yabashi wani magani kati daya yace "idan yataso maka kadinga sha, but maisa bazaka kira iyalinka suzo ba, kanada right din nan, as a prisoner idan kanason kahadu da iyalinka akwai family room dazakaje kai booking karubuta date, idan ranan yazo I think kaman ko 3hrs ne ko 2hrs ne but nasan u are entitle to that kaga saika ragema kanka damuwa kafin kasami wata matsala" dan lumshe idanu Maheer yayi yatashi dagakan gadon yace "thanks" sannan yawuce yafita daga dakin ahankali Dr yabishi da kallo ga yaro so young bright and handsome gashi lafiyayye yabata rayuwanshi yay end up agidan yari. Yasmeen na kwance ita kadai adakin da Baba yasa aka gyara mata anyi arranging gadon dakinta da aka kwaso daga gidanta awajen da kayayyakin ta na sawa sauran kayanta ankai store din gidan da Baffa ke ijiye kayan gona ankai kayan gonan kasuwa an jera duka kayanta tass awajen. Tana kwance kaman marainiya ita kadai ta lumshe idanunta sun kumbura sosai tanaji dazu su Baba na hira an yankema Maheer hukuncin kisa, taji Baba kuma na fadin zasu shiga kotun shari'a ashirin ga wata dan karba mata saki, Baba sai murna yake, sabida kawai ita musulma ce amman jitayi kaman ta kashe kanta kawai tahuta but bazata iyaba, gidan gabaki daya babu mai mata maganan Maheer harsu Farida kowa ya tsaneshi baason tanama maganan shi Baba yayi forbidding nata, hannu Ammi dataji akan fuskanta yasa tabude idanunta ahankali dasaukai jajir takalli Ammi cikin wani irin murya kaman na wacce kwakwalwanta yajuya tace "Ammi wai dagaske an yankema Maheer dina hukunci kisa"? Bakaramin tausayi Yasmeen kebama Ammi ba, ahankali Ammi ta gyadamata kai alamun eh, dawani kalan sauri Yasmeen tajuyar da kanta zuwa dayan gefen ta taushe bakinta tana kuka, ahankali Ammi ta kwanta
Chapter 118 · 0% Book details