← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 141

Sashe 70

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yazo club dinnan dan yayi aiki ne amma wlh babu abinda yayi, mails din da yakamata yay responding to suma ya kasa, Hajiya na fita ya sake dauko iPad din ya kunna kawai Yasmeen yake kallo, he watched her all through the night kaman ya sami wani TV show without doing anything, 5 daidai ya dauki wayanshi yayi dialing number shi Wanda yake wayan days barma yasmeen din yay dialing yana kallonta.
Yasmeen na cikin barci taji vibration na waya, ahankali ta bude idanunta wayan ta kalla sai kuma ta tashi zaune a hankali addu'an bacci ta fara karantawa sannan ta mika hannunta tadauki wayan dake kan side drawer ta kalla ganin number da akai saving da Maheer ke kira dan yanzu takoyi spelling na sunanshi duk inda tagani zata iya karantawa katsewa wayan yayi dasauri Maheer ya sake dialing yana kallonta murya chan kasa yace "pick up baby" kaman taji meyace daukan wayan tayi ta kai kunnenta batare da tayi magana ba ta daure fuska, wani irin sweet smile Maheer yayi yace "good morning to you too" turomai baki tayi kaman yana gabanta, cikeda da tsokana yace "fushi kike dani amarya ta, aiki fa mijinki yaje" murya can kasa Yasmeen tace "aikin aikin shaidanu ne na yan wuta" shiru yayi baice komiba, murya chan kasa tace "bana son ALLAH ya konaka dan ALLAH ka daina kaji" sosai yake kallon fuskanta damuwa ya gani akai, shiru ya sakeyi yana kallonta kaman bazai magana ba sai kuma chan yace "zakimin addu'a to?" Dasauri tace "zan maka" ahankali yace "why"? Shiru tayi ta kasa magana hakan yasa yace " nakira natasheki kiyi sallah ne" murya chan kasa tace "kaima kaje kayi" gyada mata kai yayi kafin ahankali yace "okay zanyi" shiru tayi batai magana ba kaman abu takeson tace tsareta yayi da idanu cikeda taushin murya yace "menene kike son fada"? "Yaushe zaka dawo"? Dawani irin sauri takai hannunta ta daura akan bakinta dan wlh bata san lokacin da maganan ya fito ba, mirmushi kadan Maheer yayi yace " kina son nadawo ne?" Gyadamai kai tayi amman awaya sai tace "ni meruwana dakai" abin ba karamin dariya ya bashi ba, shiru yayi yana kallonta she's so cute , harta cire rai zai magana yace "sai next weekend zan dawo" zaro idanu tayi sosai ahankali yace "ranar Friday zansa Dan yazo ya kaiki school I think Saturday zanzo, Sunday da night sai na tafi" sosai taji kuka yazo mata amma daurewa tayi tace "toh" tacire wayan daga kunnenta da Sauri kife kanta tayi akan kafanta tahau kuka Maheer na kallonta feeling so bad daga tashinta ya sata kuka, almost 5min tayi tana kuka kafin ta dago kanta hannunta tasa tashare fuskanta tass sannan ta wuce bayi ahankali shima Maheer ya tashi daga kan kujeran ya wuce sama bathroom na office din ya dauro alwala. Yana idar da sallah ya tashi yafito daga club din yana tafiya ahankali, Dan na ganinshi yay gaba da sauri dan zuwa daukan mota, Maheer na fitowa Dan na parking a kofar club din shiga cikin motar Maheer yayi yazauna yana danna iPad din yabude video ganin Yasmeen bata cikin dakinta yasa dasauri yafita daga folder yashiga asalin babban folder inda kowani bangare , a parlor ya ganta ta zauna tana sanye da hijab har kasa murya chan kasa Maheer yace "my wife is lonely" dasauri Dan dake tuki yace "na'am sir menace?" Shiru Maheer yayi baice komi ba sai chan yace "idan ka ajiyeni a palace go home zan maka transfer kudi inaso kama wife dina shopping" dasauri Dan yace "but akwai kudi a hannuna" yatsina fuska Maheer yayi yace "don't use that money zan baka wani ATM card kayi cefanen dashi" gyadamai kai Dan yayi yace "yes sir" wuraren 8 suka kai palace hakanan Maheer jiyayi kawai ranshi yabaci daga shigowa gidan parking Dan yayi ya fito tareda budemai kofa, kusan 10min Maheer yayi kafin yafito daga Moran ahankali yabi gidan da kallo jiyayi yafi son dayan gidan anytime yake chan yafijin peace da farin ciki kodan agidan ana jin kiran sallah ne oho nan ko cikin dajin babu ta inda zaiji kiran sallah, wallet dinshi yaciro daga aljihu yazaro wani ATM na zenith Bank yace "pin din is 0090, buy everything" gyadamai kai Dan yayi yajuya yatafi shikuma yashiga cikin gida yabi parlor da kallonta babu kowa ciki tsaftsaf ba datti tunda yake bai taba jin this feeling dayakeji idan yashigo gidan nan ba sai yau, daurewa yayi yacigaba da tafiya yahau stairs yay sama ko kallonta dakin Hajiya baiyiba yawuce dakinshi, ahankali yabude kofan ya tsaya Jim yana kallon dakin jin wani kunci na zuwan mishi yakai kusan 2min tsaye bakin kofan kawai bayama son iskan gidan sannan yashiga ciki, ijiye iPad din yayi akan gado da wayanshi yacire takalmi yawuce bayi.
Tunda ya shigo gidan Hajiya dake tsaye jikin window taganoshi agabanta yay magana da Dan dudda bata bata iya jiyosu sosai take kallon Maheer din ta window, abinda kasani tun yana 8yrs dole kagane wani abu, hakanan idanunta kemata kaman something seems off about Maheer tarasa gane menene, ganin ya shigo yasa tawuce closet nata wani turare tadauko daga wani kwali tabude turaren gawata yar paper atsakiyanta da akai rubutu ciki, feffesa wa tayi sannan ta kalli kanta a mudubi tana sanye dawata yar gajeran Riga da kyar rigan yawuce ass dinta ga manyan nonuwanta baje baje ana gani baza gashinta tayi tasa slippers tafito tana murmushi harta kosa taganshi, ahankali tabude kofan dakinshi ta shiga baya ciki jin karan ruwa yasa tagane yana wanka, karasawa gaban gadon shi tayi tana kallon sabon IPad din data gani a hannunshi dazu a club yana ganinta yatura a drawer, zama tayi abakin gadon tadauki iPad din tana kallo wannan sabo ne fil, business iPad dinshi a hannun PA dinshi Dan yake zama wannan wannene na menene? Maheer datasan ko wayanshi babu yanda zaiyine yake dauka dan baison waya mezaiyi dawata iPad, danna iPad din tayi ganin akashe yasa tashiga kunnawa tadauki dayan wayan kuma tabude tashiga dube duben message da gallery bataga komiba dasauri tafito tashiga calls wani number tagani dabatasan nawaye ba basuna akai kuma Maheer ne ya kira Number around 5 na asuba, dawani kalan sauri ta danna number dan ta duba history yaune yataba kiran number kuma sunyi 10:45minutes suna waya, faduwa gabanta yashiga yi wannan layin ma Maheer daga ita sai su Nas da Dan keda number sune kawai yake waya dasu ko customers ta wayanshi dake hannun Dan ake kira, hannunta har rawa yake da gudu tayi dialing number takai kunnenta ringing wayan yashiga yi wayan na gab da katsewa Yasmeen ta dauka cikiin yar kankanuwan shagwaba tace "Hello" wani kalan sakin wayan Hajiya tayi akasa tasbagen firgicewa datayi kaman mai tabin hankali daidai Maheer na bude kofan bathroom yana fitowa daga wanka.
EPISODE
Chapter 70 · 0% Book details