← Book details Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 141

Sashe 68

Kyalkyalin Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tundaga kafanta har zuwa cikinta • zuwa kirjinta da kanshi ke wajen wasa • wasa ga mamakinta bacci mai nauyin gaske ne yasake kwasheshi ahaka dan tanajin yanda yake sauke iiyan zuciya akirjinta, itama wani barawon baccin ne yasake saceta. Vibration na wayanshi ne yatadashi bude idanunshi yayi ahankali yakalli yanda ya rirrike Yasmeen kanshi ke kiriinta ahankali batare daya saketa ba yakai hannunshi yadauki wayanshi dan yasan Hamad ne shine da Dan da Baba saikuma Yasmeen sukasan this number, kai wayan kunnenshi yay batare dayay magana ba, & Hamad yace "to dan iska al saika saki yar mutane tazo tama yan uwanta sallama zasu tafi kai wh ma Maheer baka da kunya, ko wankan safe bakaiba imagine pi ne ajikinka kawai ka dau......... " katse wayan Maheer yayi ya jefar yakai hannunshi ya kunna wutan dakin, hasken da Yasmeen tagani cikin bacci yasa ta yatsine fuska zata koma tashige cikin jikin Maheer yaja hancinta yace "wake up Clingy gurl" ahankali Yasmeen tabude idanunta ganin Maheer na gab da ita yasa dasauri takoma baya tana sauke kanta kasa, sauka yay dagakan gadon yace "come down ana ¡ranki" 3:37 PM sai alokacin ma ta tuna da yan gidansu dasauri tasauka dagakan gadon, gyalenta ta dauka ta daura akai bamata tsaya tayafa dakyauba tasaka slippers dinta dasauri tai hanyar kofa tama manta da bayan riganta dayake abude, karat Maheer yarike hannunta hakan yasa tajuye atsorace, wani shegen kallo yamata yace "where do you think u are going to ahaka?" 3:38 PM Shiru tayi takasa magana, ahankali yadan duko saitin fuskanta runtse idanunta tayi dasauri sabida vanda gabanta ke faduwa, hannunshi yakai bayanta yaja zip don riganta back up sannan yadago gyalenta ya yafamata har goshinta, kafin yadan gyara zaman riganshi daduk ta yamutse yasa slippers dinshi yarike wayanshi a hannu yawuce wajen kofa yabude key yakalleta yace "let's go". Bude kofan Maheer yayi yana kallonta, ahankali ta tashi tawuce tagabanshi tafita daga dakin dasauri tai hanyar kitchen din tasa hannu tabude kofan tashige tamaida tarufe duk yana kallonta sannan shima yafito yaja kofan yawuce yana tafiya ahankali yana leken side din Yasmeen. Falonta tashiga ganin babu kowa an gyara ko'ina na kamshi yasa tai wajen kofa da sauri jin hayaniya a tsakar gidan bude kofan tayi tafita duk aka juyo ana kallonta wlh kaman kasa zai sage tashige takeji karasa sauka tayi kanta akasa taje inda Mama ke tsaye tama kasa magana hakan yasa Mama cikeda wayewa takai hannunta tadaura kan goshinta tace "sannu Yasmeen ya jikin" jin babu zafi jikinta yasa Mama tasauke hannunta kasa, ahankali Yasmeen batare data iya kallon Mama ba tace "dasauki Mama" Maman Intee tace "sannu Yasmeen kinji" gyadama Maman Intee kai tayi daidai motocin abokanan Hamad na zuwa duk sukai parking agabansu, Mama tace "too Yasmeen lokacin tafiyan mu yayi ki kyautatawa mijinki yi nay bari na bari, Allah ubangiji yamiki albarka Allah yama auranku albarka" hawaye Yasmeen taji yacicciko a idanunta Farida tazo dasauri ta rungumeta sukahau kuka dukansu biyun da kyar akaja Farida Yasmeen naji nagani suka shishiga mota sukabar gidan tafashe da kuka sosai takasa komawa ciki. Kusan 5min tana tsaye awajen tana kuka taji anyi gyaran murya dasauri tadago idanunta takalli saitin inda taji gyaran murya, hada idanu tayi da Maheer dake saman bene rike da goran ruwa a hannunshi yana kallonta, anatse yanuna mata kofa flat dinsu yace "go inside" hararanshi tayi cikeda tsiwa tareda dauke kai zaro idanu Maheer yayi vace "na sauko na sameki anan" sake dago kanta tayi ta ballamai harara sannan tajuya tawuce ahankali ta tafi flat nasu tawuce sama alwala tayi tai salla sannan kawai ta kwanta kan tabarman dan babu abinda kemata dadi. Tana waien har akai isha'i ta idar tai shafa'i da wuturi tana kara tuna abubuwan da Ammi takoya mata wanda number shine rike addu'a, addu'a tayi sosai last addu'an datayi shine Allah ka shiryar da mijina saikuma ahakali tace "Pablo" kaman an tsunguleta ta tashi dagakan dadduman dadduma ta linke ga ijive tacire hijabin tacire rigan dake jikinta ta linke ta maida a wardrobe sannan tawuce bayi tana kallon yanda aka jera mata abubuwan ga turarukan jiki da aka hadamata musamman su wayanda tana gama wanka zata fesa ne kafin ruwan jikinta ma yabushe, wanka tayi tadade sosai karkashin shower tana wanka kodan gidansu da bucket suke wanka oho ga ruwan na zafi tana gamawa tazo oho ga ruwan na zafi tana gamawa tazo ta feffesa turarukan sannan tadauki towel tadaura takalli kanta amadubi gashin kanta duk yay lema lema sabida shower ahankali tasa hannunta tadauki combo tashiga takewa tana tuna abinda Maheer yamata dazu adakin da yanda yamata allura runtse idanunta tayi da karfi tanajin was abubuwa namata tafiya ajiki kuna nawani kalan kamata, tass ta combing kan ya keanta tasaka ribbon tai parking ta dunkule bakin gashin bakaramin kyau tayiba bude kofan bayin tayi tafito tawuce sip tabude wani dan gown tadauka na bacci that is simple and decent red ta saka ya tsayamata a guiwa sannan tazo tazauna gaban madubi mai tasha sannan tafesa duk turarukan da mussamman suna akace tadinga amfani dasu da night zokaji yanda dakin ke kamshi tashi tayi tawuce bayi ta ijiye towel din da yacire tadawo zama tayi abakin gado tai shiruuu shikenan yanzu agidan nan zata dinga rayuwa ta bar gidansu kenan? Wai da gaske yanzu • tadawo matan Pablo? How? Shikenan tamaza matarshi, hawaye ne suka gangaro mata a idanu dasauri tasa hannu tashare so kawai take taji muryan Ammi dana Nana tai kewansu sai yanzu ma take tuna ita tun jiya biki batasan inda sayanta yake ba ko tabarshi agidansu ne oho, tana zaune nan bakin gado jingina kanta tayi tai shiru gashi batajin bacci ko kadan, kamshin turaren Maheer ne taji yadaki hancinta dasauri tajuyo tana kallon ko'ina adakin gabanta na faduwa tazubama kofa idanu, kusan 2min tana kallon kofan kafin taji antaba koan daga waje dasauri tasauke kanta daga kofan gabanta na mugun faduwa, ahankali aka bude kofan Maheer ne vana shirve cikin bakin suit yana zuba ban kamshi yazuba mata idanu, ahankali yadanyi gyaran murya hakan yasa tadago idanunta kaman munafuka ta kalleshi, hada idanu sukayi shima yana kallonta, sake dauke kanta tayi dasauri, shiru yayi yana kallonta da ko'ina na dakin kafin ahankali yace "zan tafi aiki" dasauri Yasmeen tajuyo da kanta takalleshi kaman yanda yake kallonta wani abu taji yazo mata wuya, ahankali kaman yar little girl tace "wani aiki?" Wani matsiyacin kallo yamata yajuya zai wuce saikuma yajuyo yakalleta yace "drug dealing" was kalan hawaye yaga sun cika mata idanu dasauri yadauke kanshi yajuya tareda jamata kofa yawuce dasauri sauri yasauka kasa yanaji kaman karya tafi at the same time tana kara reminding kanshi yariga ya aureta yanzu he can always come back anytime yakeso yaganta his business needs him, harya bude kofa yafita yakalli wayan dake hannunshi saikuma ahankali yajuya yakoma dakin sama yawuce wanna karan direct yabude kotan dakinta tana zaune yanda yabarta dakinta tana zaune yanda yabarta hananyenta nakan fuskanta tana share hawaye ganinshi dasauri tadauke kai cikeda fushi ta tashi zata shiga bathroom dawani irin sauri yakama hannunta fizgota yayi tafado jikinshi yakai duka hannayenshi ya tallabo fuskanta yana kallon idanunta dahar sunyi ja ahankali yace "why are you crying yanzu"? Hararanshi tayi zata fizge kanta tace "me ruwanka dani"? Softly yace "I have every ruwa dake" sata yayi ajikinshi yafara tafiya da ita har zuwa bakin gadon zama yayi yazaunar da ita ahankali, hannunshi yakai ya goge fuskanta yana kallon yanda take kallonshi, wayanshi yakama hannunta yasa aciki murya chan kasa yace "be using this uhn" yay shiru yana kallonta yanda taki kallonshi vanajin dadin kamshin datakeyi, almost 10 min yayi ahaka sannan ahankali yamike tsaye yawuce fuuu yafita Yasmeen tabishi da kallo wani hawayen a fitowa ko kadan bataso yatafi ficewa yayi yashiga mota yana kal Idon Hamad dake balcony asama na kallonshi kaman ya sauko yarufe shi da duka Dan yaja motan suka fita daga gidan. Da mamaki Nas da Wike ke kallon Maheer daya shigo club din kaman daga sama aka jehoshi Dan biyedashi as usual, da gudu Nas yazo wajenshi wani irin rungume Maheer yayi sosai yace "ai nadauka those Iranians sun cine mana kai" dan yatsine fuska Maheer yayi daidai Wike yazo shima cikeda girmamawa yace "welcome back Sir" gyadamusu kai yayi kawai batare dayay magana ba yay hanyar office suka bishi abaya kaman bodyguards nashi har zuwa office nashi, shiga ciki yayi komi a gyare dan kullum sai an gyara ya zauna anatse yakalli Dan yace "get the club Manager" yakalli Nas yace "munada shipment dazai iso from Iran in 2days, natura maka mail kan new border mu how is everything going?" Dasauri Nas yace "very smooth Sir" gyadamai kai Maheer yayi yakalli Wike yace "bangaren ka fa"? Anatse yace "nima bangarena komi lafiya lau saidai Sir one of our drivers is missing head driver yasanar damu su duk suna lagos yanzu haka banda shi, kana tunanin CP ne yadauke shi" anatse Maheer yace "shine" dasauri Wike yace "Sir wai yaya zamuyi da CP nan ne"? Ahankali Maheer dake kokarin kunna desktop yace "I will take care of him" dasauri Nas yace "to idan direban yay magana fa"?Ahankali Maheer yace "the only thing daya sani is inda suke dauko kaya da inda suke kaiwa. wanda yanzu duka an chanza ma location ko yaje bazai sami komi awajen ba, anywho zai gaji ya sakeshi ne dan aboye yasace shi and he can't get any vital info daga d boy" daidai Dan yashigo tareda Manager, Maheer yace "me da me bamu da shi a supply room I need list kaje kayi ka kawo mini" gyadamai kai Manager yayi yace "okay sir" yajuya yatafi sannan Maheer yakalli su Nas daketa kallonshi yace "get back to work" dukansu juvawa sukayi suka tafi varage saura Dan kadai a office din, ahankali Maheer yace "give me that new iPad, dakuma wayana ka kunna akwai charge"? Dasauri Dan yace "yes ina kunnawa ma aka hau kiranka" dan tsaki 23 Maheer yay dan yasan waye ke kiranshi daga kunna wayan after kaman 1month plus dayake akashe harta kira, karban wata sabon iPad yayi ya kunna yakarbi wayanshi dako kallonshi baiyiba ya ijiye kan table din sannan yace "you can go" wucewa Dan
Chapter 68 · 0% Book details