← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 66

Sashe 7

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta meda nunfashi ta dai'dai sannan ta nufi wani bag irin na boxing din na ta dunkule hannun ta, ta fara kai mishi bugu da duk karfin ta , bugun shi ta ke da hannu da kafa duka sawa ta ke
Ga Dukan allamu ta san abun da ta ke yi dan yanayin jikin ta ya na nuna ta na yawwan motsa jiki , ga tumbinta a shafe kamar ba ta saka mishi abinci sai dan neman Shape kamar ita ta yi kan ta

Duk da hakan motsa jiki ya na da dadi gaskia , ya na rage hatsarin kamuwa da wasu cututuka , ya na kara karfin kwakwolwar dan in ka na motsa jiki a lokacin ji ka ke duk wata damuwar ta ka ta gushe , bare in ka na boxing sai ka ga kamar mutumin da ka ke jin haushi ka ke bugu hakan na rage zafin zuciya kar ka je ka buge shi watarana 😂

Sai da ta dauki yanzu ma wajen 30 minutes ta na hakan kafin ta bari ta tsaya ta na meda nunfashi
Da ga haka ta juyo ta fara takawa ta fice room din
Maimakon ta shiga bedroom din ta sai ta sauko stair

Parlourn din kassa ta sauko , kai tsaye ta nufi dining room ta shiga kitchen
Ta nufi fridge ta bude ta dauki gorar ruwa guda mai sanyi sannan ta fito

Cikin parlourn ta dawo ta nufi doguwar sofa ta Haye ta zauna sannan ta bude gorar ruwan ta kafa a baki ta fara sha
Sai da ta sha wajen rabin ruwan sannan ta ciro ta da ga bakin ta , ta rufe ta ta tila tsakiyar falon

Ta na tila ta , ta jiyo sallamar momy ta shigo cikin gidan
A hankali ta kai kallon ta wajen kofar ta na amsa sallamar ta kafin ta kauda kan ta

Momy na ganin ta ta ce " yau yar gym ce kenan , na zata kin hakura kin daina , wajen sati biyu yanzu ba ki shiga gym ba "
Ta kai karshen ta na karasowa cikin parlourn ta zauna saman sofar da ke fuskantar ta Safa

Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " dan hutu ne na ke , yanzu kuma na koma "
Gyada kan ta momy ta yi kafin ta ce " ya yi kyau , ya kamata ki ci gaba , kin San motsa jiki ya na rage damuwa "

" momy ni fa ba ban da damuwa "
" na ji malama ba ki fada min ya meeting din ku ta kasance ? "

Gyara zaman ta Safa ta yi ta daura kafafun ta saman sofar sannan ta ce " ba wani abu babban, kawai dai shirin da na ke yi on live , zan ci gaba da yi a cikin tashar su , bayan haka babu wani babban "

Gyada kan ta momy ta yi kafin ta ce " masha Allah , ya yi kyau , yanzu yaushe za ki fara , kuma me za ki kawowa wannan karan , dan na ji fa an ce ki na da mabiya sosai "

Yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Friday zan fara , zan so na yi magana da Doctor Badariya Moussa wannan karan , kin San gynecologist ce "

Murmushi momy ta yi kafin ta ce " wow kennan a kan ciwon mata za ki yi magana wannan karan , gaskia ya yi kyau , na san idan ki ka yi magana a kan ciwon mata za ki kara samun mabiya "

Mikewa zaune Safa ta yi ta na kallon momy ta ce " yawwa momy akwai wani ciwo da na ke son mu tatauna a kai da ita , yayon fitsari "

Ai momy ba ta san lokacin da ta bushe da dariya
Sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce " ba yayon fitsari ba , yoyon fitsari ta ke , wai ke har yanzu haoussar ki ba ta zo dai'dai ba "

Shagwabe fuska Safa ta yi ta ce " okay na ji , ni yanzu magana za ki yi min a kan ta "

" Banda abin ki Safa ni ba likita ba ce , amma ina yawwan jin sunnan wannan cutar musaman a kawuyuka ta fi yawaita a cen , ta na samuwa ne lokacin haihuwa , sai ki ga macen ta dinga fitsari ba tare da ta sani ba , wani lokacin duk ahalin ta kawurace mata su ke yi saboda wai ta na warin fitsari , idan kuma ta na auren mijin da bai san Allah ba sai ki ga ya tsane ta har ya sake ta saboda wannan cutar "

" no momy kawai saboda wannan cutar , ai ta na da magani ko ? Maimakon kawurace mata kamata ya yi su dinga janyo ta a jiki , har Allah ya sa ta samu sauki , wannan kawuracewar zai sa ta samu troubles a kwakwolwar ta "

Jinjina kan momy ta yi kafin ta ce " kin san in mutun bai yi karatu ba , jahilci ya sa ya yi komai ma , ba ki san mata nawa ne su ka baro gida jen su ba kawai saboda wannan cutar , yanzu su na yawo saman titi da jinjiri a hannu in kuma ba ki yi sa'a ba yaron ya mutu , kin san ma fi yawan cin ma su kamuwa da wannan cutar raping din su a ke yi , ba su duba abun da ya faru da wadanan yan matan sai dai cutar da ke damun su "

" gaskia abun nan bai yi ba " Safa ta fada ta na mikewa tsaye

Ita ma momy mikewa tsaye ta yi ta na fadin " yanzu kin san inda za ki samu contact din Doctor din "

" in mun koma school , zan tambayi Haoua , ta ce min ta taba zuwa Hospital din da ta ke aiki so bayan mun sauka na je na gan ta na yi mata magana "

To kawai momy ta fada kafin su fara takawa a tare su ka Haye stair kowace ta nufi bedroom din ta dan lokacin sallar magriba ya yi
Momy ita ta shiga bedroom din na farko , Safa kuma ta wuce nata

Monday 📚

Zaune Safa ta ke cikin library ya na school din su
Ta na sanye cikin wani skert navy blue ya dan wuce guyiwa , da T-shirt Sky blue mai ratsin white da ga gaba , ta yi Rowling veil din ta white colour , ta na sanye da sneakers white colour su ma ta yi kyau over

Rike ta ke da wani book ta na karantawa cikin konciyar hankali
Ta na a haka ta jiyo sallamar wasu yan mata guda biyu su na rike da bags din su
Guda na sanye da atamfa mai kyau yellow mai zanen flower bakake
An yi mata dinkin Skert da riga , ta saka wani dan karamin hijab zuwa kirji black colour

Dayar kuma ta na sanye da wata Abaya Red colour mai kyau ta yi Rowling veil din ta a kai
Dukan su dai ba laifi su na da kyau kuma su na da dan haske amma da ga gani kassan ba na su ba ne duka sun hada da blicing

Ba tare da ta dago kan ta ba , ta amsa musu sallamar su
Chair su ka janyo su ka zazauna sannan me sanye da atamfar ta ce " Pretty na ga videos din ki jinya , gaskia na ji dadi , yanzu tafiya za ki yi ki bar mu "

Murmushi Safa ta yi kafin ta ce " no ba zan bar ku ba , ba gashi na dawo ba "
Mai sanye da abayar ce ta karbe zancen da cewa " haka dai ki ka ce , yanzu fada min yaushe za ki fara shirin na ki "

Ajiye books din hannun ta ta yi kafin ta kale ta ta ce " dama ke na ke jira ki zo , Hospital din da doctor Badariya Moussa ke aiki na ke son ki kaini idan mun sauka "

" okay ba matsala " ta fada ta na murmushi , kennan wannan ita ce Haoua da ta ke wa momy maganar ta

Kallon mai sanye da atamfa Safa ta yi kafin ta ce " Djami ko za ki biyo mu mu tafi tare , da ga nan sai mu je ko da sayan ice cream ne "

Murmushi Djamila ta yi kafin ta ce " yes of course ina zuwa mana "

Ta na gama fadar haka wani saurayi ya yi musu sallama

Safa na ganin shi ta dauki books din ta ta ci gaba da karantawa ba tare da ta amsa mishi sallamar shi ba

Haoua da Djamila ne su ka amsa mishi sallamar shi kafin Haoua ta ce " Mansour ya ka ke kwana biyu na bar ganin ka cikin school din nan "

Dan murmushi saurayin da ta kira da Mansour yayi kafin ya ce " Wlh wani aiki ne , na tafi Lagos , jiya na dawo "
Hannun shi ya daura saman kafadar Djamila ya na fadin " Baby ko zan iya ganin ki minti daya "

Murmushi ta yi ta na jinjina mishi kai kafin ta kali Haoua ta ce " ina zuwa "
Da to ta amsa mata , sannan Djamila ta mike ta riko hannun Mansour su ka fice libraryn ba ki daya

Su na fita Safa ta sauko da book din ta ta ja dan siririn tsaki ta na kallon Haoua ta ce " why wannan yaron ke zowa inda muke , in magana ya ke son yi mata ba zai iya bari su hadu cen gidan su ba "

Yar karamar dariya Haoua ta yi kafin ta ce " haba ke ma pretty , Boyfriend din ta ne fa , kuma kin san ya kai kudin tambayar auren ta , so ki daina takura wa kan ki a kan su please , Idan Djamila ta ji wannan maganar ba za ta ji dadi ba "
Chapter 7 · 0% Book details