← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 66

Sashe 19

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kan ta Safa ta yi kafin ta ce " Doctor zan so ki yi wa ma su kallon mu dan bayani a kan ki "

" Assalam alaikum ma su kallon mu , da farko dai suna na Doctor Badariya Moussa , kwarariyar Gynecologist a babban public Hospital da ke kaduna "

Jinjina kan ta Safa ta yi kafin ta ce " mun gode doctor , a yau zan so mu tatauna a kan cutar da ta shafi mata , wadda a ke kira da yoyon fitsari , obsterical fistula , zan so ki yi ma na Karin bayani a kai "

" Da farko , wannan cutar ta na daya da ga cikin lesions ma su tsanani , ma su hatsari da za a iya kamuwa da ita lokacin haihuwa , kamar barkewa ce a ke samu tsakanin Vagina da Bubble lokacin haihuwa in naguda ta yi tsanani , idan kuma ba a samu kulawa cikin sauri kuma mai inganci , hakan na haifar da fitar fitsari ta vagina ba tare da sani macen ba , wajen dubu dari biyar na mata da yan mata su na fama da wannan cutar musaman a Africa dan ta fi yawanci a nan , kuma ko wace shekara sai mun samu irin wannan case din "

Katse Safa ta yi da cewa " amma Doctor har yanzu ba a samowa wannan cutar magani ba , ko dai maganin ne bai iso ba a nan wajajen mu "

Girgiza kai kadan doctor ta yi kafin ta ce " ko daya , wannan cutar ta na da magani , kuma ko nan a Nigeria mu na da shi "

" To Doctor me ya sa ba a anfani da shi , sai dai a bar mata su na fama da wannan ciwon duk da ba kashewa ya ke ba "

Dan karamin murmushi doctor ta yi kafin ta ce " Rashin bacewar wannan cutar ya na nuna gazawar health system din mu musaman na nan Nigeria , Ba su dauki ciwon mace ba da wani mahimanci , examples cikin Hospital din da na ke aiki , ni kadai ce Gynecologist , ta ya za a iya eraducted wannan ciwon , idan ba mu ba shi mahimanci ba , wani abun takaicin kuma matan da su ka kamu da wannan cutar su na cikin depression da talauci ko abincin su gagarar su ya ke "

" doctor ban gane ba ina familyn su , ina mazajen su ? "

" duk sun guje su , duk yawwancin matan da ki ke gani a kan hanya dauke da dan karamin yaro duk yawwancin wa an da su ka kamu da irin wannan cutar ce , familyn su duk sun guje su saboda warin fitsarin da su ke yi , idan macen mai aure ce , auren har rabuwa ya ke yi "

Cike da takaici Safa ta ce " ai ba laifin su ba ne , kamata ya yi a janyo a jiki "

Da sauri doctor ta katse ta da cewa " yawwa kin fada dai'dai , ma su wadanan cutar kamata ya yi a dinga janyo su a jiki , ko dan rage musu radadin abun da su ke ciki , yanzu akwai wata association UNFPA , wannan association ta na bayar da gudun mawa wajen bawa matan da su ka kamu da wannan cutar abinci da magugunan da za su bukata , ta na forming din su ta yadda za a rigafi wannan ciwon da kuma traitement din ta , ta kuma karfafa maternal health service , musaman abun da ya safi wannan cutar "

" amma kuma har yanzu akwai ta ? Ko an samu canji ? "

" eh to an samu canji amma mu na nan dai , wa a dan ya kamata su yi wani abu a kai sam ba su damu ba , amma ba yadda mu ka iya dole mu yi aiki da abun da gare mu "

Yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Allah ya sa mu dace to , Allah ya buda idanun su kan abun da ya safi al'umar su "

" Amine suma amine " Doctor ta fada cikin sanyi

Dawo da kallon ta Safa ta yi kan camera kafin ta ce " to ma su kallon mu , a nan mu ka kawo karshen shirin mu na abikiyar hira , Tare da Doctor Badariya Moussa , Doctor mun gode da lokacin ki da ki ka bu " ta kai karshen ta na dawo da kallon ta kan doctor

Murmushi doctor ta yi kafin ta ce " ni ce da godiya "

Murmushi Safa ta yi kafin ta kali camera ta ce " Sai mun hade da ku a sati mai zuwa in Allah ya kai mu "

Ta na gama fadar haka mai kula da camera ya daga murya ya ce " Cut ! "

Ya na gama fadar hakan wajen duk ya dauki clapping
Ita dai Safa ta tsaya ta na kallon su ta rasa me su ke yi wa clap haka

Sai da su ka Kamala sannan Mutalab ya ce " ni dama na san ba zan yi nadamar daukar ki da na yi ba "

Saukowa Safa da Doctor su ka yi a tare su ka karaso wajen da su Mutalab ke tsaye ta na dan murmushi

Wanda ke kula da cameras ne ya ce " Gaskia dauka ta yi , shiri ya yi kyau , ko irin wannan nervosity da sabin shiga gaban camera ke yi , ba ki nuna ba , amma kin saba shiga gaban camera ko ? "

Girgiza mishi kai Safa kawai ta yi ta na dan murmushi

" Miss Safa zan so na yi magana da ke a office din na yanzu kafin ku tafi " Mutalab ya fada ya na juyawa ya bar wajen

Ya na barin wajen Nabil da Yasmina su ka karaso , Yasmina ta riga shi cewa " Gaskia Sister shirin ki ya yi kyau da fatan haka za ki ci gaba da wayar da kan mu , musaman abun da ya shafi lafyar mu "

Ita dai Safa ta kasa cewa komai sai dai dan karamin murmushin da ta ke yi

Sai da su ka gama yaba ta , kowa da irin tsokanar da ya ke yi mata , ita dai murmushi kawai ta ke yi
Da ga haka ta wuce office din Mutalab
( ni dai ban san abun da su ka tatauna a kai ba 😴😴 )

▪AFTER SOME HOURS

▪ Safa 💋

Zaune ta ke cikin parlourn din gidan su , ta na kallon Tv ta na ma Snoopy wassa

Kamar da ga sama momy ta shigo parlourn babu ko sallama
Da sauri Safa ta mike ta na kallon ta a rude ta ce " momy lafya kin shigo babu ko sallama ? Wa ke kore da ke ? "

Zama momy ta yi saman sofa ta ajiye bag din ta gefe sai faman huci ta ke kamar wadda ta yi gudu
Ita dai Safa da kallo kawai ta ke bin
[27/08 à 10:43] MEERAH🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 💋❤

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

👇👇👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

P A G E 11 🥀 ❤

Sai da ta gama hucin ta sannan ta kali Safa cike da bacin rai ta ce " wai kin san abun da wacen mara mutuncin ya kire ni ya fada min ? "

Girgiza mata kai Safa ta yi allamun a'a

Murmushi takaici momy ta yi kafin ta ce " wai so ya ke ya aura miki Sami "
Tsaki Safa ta yi kafin ta kauda kan ta gefe cikin ko in kula ta ce " and so what dan ya ce hakan , cika baki ne kawai "

" Safa kin san abun da ki ke fada wai , ce miki na yi aura miki Sami ya ke son yi , za ki ce min h..... "

Cikin nitsuwa Safa ta katse ta da cewa " momy wlh ke fa ki ka damu da maganar wannan mutun , ba shi da iko a kan rayuwa ta , shaidar shi guda ya ce ni ɗiyar yayan shi ce , idan na kai wannan gaban kotu cewa zai yi ni ɗiyar matar shi ce kawai ba shi da hakin aurar da ni , wlh momy babu wanda ya isa cikin duniyar nan ya saka ni abun da ban yi niya ba bayan Daddy da momy , ko ke kin ci darajar sunan momy da na ke kiran ki da shi " ta na gama fadar hakan ta tashi ta nufi stair da sauri ta Haye

Ta na hawa Snoopy ya tashi da gudu ya bi bayan ta
Ita dai momy da kallo ta raka ta har sai da ta Haye sannan ta juyo ta na sauke ajiyar zuciya dan ta san halin Safa duk in ta ce ba ta san abu ko sama da kassa za ta hade ba za ta so shi ba , shi ya sa ta ke bin ta ta lalama in ta ce da karfi za ta bin ta za a yi kayan kunya

▪WASHE GARI MISALIN KARFE 10 NA SAFE

▪ABUJA ( GIDAN SU TWINKLE )

Zaune duk mutanan gidan su ke cikin parlour har da Daddy
Kallon Sami Daddy ya yi kafin ya ce " kai Sami na yi magana da Aziza a kan auren ka da wannan yarinyar , ta ce ita ba ta yarda ba , dan haka ni ba zan matsa mata ba dama ba son auren na ke ba , dan haka ka nemi wata yarinyar daban "

Da sauri Sami ya katse shi da cewa " haba Daddy , kai fa ka ke da iko da ita ba aunty ba , why za ka hana ni auren ta , i really love her "
Chapter 19 · 0% Book details