← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 66

Sashe 15

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kadan Haoua ta yi dan ta san duk duniya babu wanda ke yi mata irin wannan abun sai mutun guda

A hankali ta mike ta juyo ,
Sai dai ta na juyowa ta ga Safa har ta kai bakin kofar library din ta fice

Nan take murmushi da ke kan fuskar ta ya bace ta koma ta zauna
Ta kai hannu ta bude box ta sama

Nan ta ga wani kyakyawan cake , pink colour mai bala'in kyau , ko ni sai da na hadiye yawu , da ga sama an rubuta HAPPY BIRTHDAY MY HAOUA da chocolate

Haoua na ganin shi ta dago kai ta kali Djamila ta ce " Djamila don Allah ki je ki ba wa Safa hakuri , wlh ba laifin ta ba ne "

Da sauri Djamila ta katse ta da cewa " to laifin wanene , dama Mansour ya jima ya na fada min , in rabu da ita ba mutuniyar kirki ba ce amma na ki yarda da shi "

Cikin bacin rai Haoua ta ce " ke Djamila kin san abun da ki ke fada kuwa , shekara uku yanzu mu na tare da Safa dai'dai da rana guda ba ta taba fada mana wata bakar magana ba , saboda wani sakaran banza cen za ki watsa mata kassa a ido , me Safa a ba ta yi ma na ba , kar ki manta har shopping ta ke daukar mu ta kai mu mu zabi kayan da mu ke so sannan ta biya da kudin ta , duk wasu bukatun mu ita ke biya ma na su , har kudin karatun mu ita fa ke biyan su "

" ya isa don Allah Haoua , cewa fa ta yi ta na son saurayin da zan auren , bayan kuma ta san mu na tare ni da shi "

" ke dai wlh an yi sakara ma in ce , duba ki gani har Abbas , saurayin da ya fi ko wane kyau da kudi a cikin university din nan , ya ce ya na son Safa amma ta share shi , samari nawa cikin university din nan su ka ce su na son ta amma ta ki kula su , sai wani sakare banza cen "

Da sauri Djamila ta katse ta da cewa " Haoua ki daina ce mishi sakare "

Mikewa tsaye Haoua ta yi ta bugi table din tsakiyar su da hannu ta har sai da hankalin sauran daliban ya dawo kan su , ta ce " na fada sakare mara mutunci , kin san dalilin da yi wa Safa wannan kazafin , Ganin shi ta yi restaurant din da mu ka je shan ice cream ranar nan ya na tare da wata yar iskar yarinya su ka shigo restaurant din ya na rike da kugun ta , lokacin da su ka yi ido hudu da Safa sai su ka juya da sauri ya bar wajen dan kar ki gan shi , ko jiya abun da ya sa Safa ta dake shi , cewa ya yi ya na son ta har ya yi kokarin ya taba ta shi ne ta dake shi , amma da ya ke ke idon ki ya rufe ba ki ganin komai sai shi ba ki tsaya ki iya tantance mai fadar gaskia da karya , wlh kin ba ni kunya Djamila , wlh idan ba ki je kin ba wa Safa hakuri ba , ki cire ni da ga cikin layin aminan ki "

Ta na gama fadar hakan ta dauki bag din ta ta saka , ta dauki box din nan da Safa ta ajiye mata , ta bar wajen , ta fice libraryn baki daya
Ta bar Djamila nan zaune sai faman muzurai ta ke yi da ido

Sai da ta dauki wajen good 30 minutes a haka , har sai da ta rage ita kadai cikin library din sannan ta tashi ta dauki jakar ta jiki ba kwari ta fito library din

Sai tunanin kalaman Haoua ta ke cikin zuciyar ta , ta rasa wa za ta kamawa , ba karya ta san Safa ba ta taba yi magana da wani saurayi cikin school din nan ba , ko gaishe ta su ka yi sai dai ta daga musu hannu , ta ya za a yi ta ce ta na son Mansour mutumin da sai ta saye shi , shi da ahalin na shi baki daya , ita sai yanzu ta fara tantama a kan abun da Mansour ya fada mata

Cikin harabar school din ta fito , ta samu wani bancin karkashin wata bishiya ta zauna ta dafe kan ta da duk hannayan ta biyu

Ta na a haka ta jiyo Muryar Mansour ya na fadin " kin ji tsoro ne ? "

A razane ta dago kai a tunanin ta shi ne
Sai ta ga Safa tsaye gaban ta , ta na rike da wayar

Ta na shirin magana Safa ta daga mata hannu alamun ta tsaya
Ba musu ta yi shiru ta na sauraron recording din maganar da ta yi da Mansour ba tare da ya sani ba

Duk abun da ya fada ma Safa sai da Djamila ta ji , nan take ta ji zuciyar ta ta yi mata nauyi , idanun ta su ka kawo ruwa

Lips din ta na kerma ta bude baki ta na shirin magana , Safa ta juya ta bar mata wajen
Ita dai Djamila ta kassa motsawa jin abun da kunnuwan ta su ka jiyo mata sam ta kassa yarda

Safa kuma ta na barin wajen kai tsaye parking space ta koma , ta shiga motar ta

Ta na shiga Haoua ta ce " ya kin saka mata ta ji "

Kallon ta Safa ta yi kafin ta ce " e ta ji ya , kin san kin ka shawara me kyau , ko ni da farko na yi tunanin na yi recording maganar da zai yi , dan na san dole zai zuwa ya yi min maganar ganin shi da na yi a restaurant "

Jinjina kan ta Haoua ta yi kafin ta ce " gaskia kan ki na ja " ta kai karshen ta na yar dariya
Hararrar ta Safa ta yi kafin ta ce " ba ni son wannan maganar ta ku ta haoussawa "

" na ji shikenan , yanzu minene shirin da za mu yi mishi " Haoua ta fada

Kallon gaban ta Safa ta yi kamar mai tunanin wani abu ta ce " Haoua ina ji a jiki na akwai wani abu a kassa tsakanin Djami da wannan sakaran, wanda ba ta fada mana ba , ko kuma ta fada mana amma ba ta fadi gaskia Dukan ta ba "

Cike da shakku Haoua ta ce " wane abu ki ke magana a kai "

" ban sani ba , amma ya kamata mu tambaye ta , kin san fa kafin mu dawo Nigeria da zama karatun JARIDA na fara yi , da ga kalaman mutun ina iya ganewa in karya ya ke ko gaskia "

" no really ? " Haoua ta fada ta na zaro idanu

Jinjina mata kai Safa ta yi kafin ta ce " really , ke ni fa akwai magaganun da ku ka sha yi min , cikin raina na san da karya ce amma na kyale ku " ta kai karshen ta na juyowa ta kali Haoua

Yar karamar dariya Haoua ta yi kafin ta ce " To sannun ki , kin sani kuma sai ki yi shiru , ya yi kyau , nan gaba sai na daina yin magana gaban ki "

Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " hmmm , na san ba za ki iya ba , amma kin san wani abu a duk lokacin da ki ka ce min tsakanin ki da Allah ku ke tare da ni , ko so daya ban taba jin karya ba ce "

Murmushi ita ma Haoua ta yi kafin ta ce " an yi sa'a, na dauko ita ma karyar ce za ki cewa "

Girgiza mata kai Safa ta yi kafin ta ce " no , wannan ita ka dai ce kalmar da ke sa zuciya ta ta yi sanyi a kowa ne lokaci , har na rage rashin yardar da na ke yi wa mutane , shi ya sa ba zan so abun da ya same ku ba ke da Djami , saboda ku kadai abokai na, na gaskiya "

Riko hannun ta Haoua ta yi cikin sanyin murya ta ce " mun gode da irin wannan soyayyar da ki ke nuna mana , don Allah abun da Djamila ta yi miki kar ki rike shi a rai "

Katse ta Safa ta yi da cewa " ni dama ban rike ta a rai ba , inda na rike ta da ba zan dawo school din nan , amma kin ga gani , yanzu tashi mu je wajen ta akwai tambayar da ke son yi mata "

Da sauri Haoua ta rungume ta ta na fadin " Allah ya bar mana ke har abada "
Dan karamin murmushi Safa ta yi ta rungume Haoua ita ma , sa ga nan su ka raba jikin su

Su ka fito motar a tare su ka nufi inda Safa ta baro Djamila
Ta na nan inda ta ke ko motsi ba ta yi ba , sai faman zaro idanu ta ke hawaye na zubar mata

GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE⚘❤

GA ACCOUNT ADRESS 👇👇👇👇

8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

KO KUMA TA CREADIT DA TA WADANAN NUMBER 👇👇👇

Zain (Airtel)
08081129487.

Mtn
07067953066.

NAIRA 200 NE ONLY

SANNAN KU TURA SHAIDAR TURA KUDIN A WANNAN NUMBER ( +22795577612 )

🩷✨✌️
[23/08 à 22:14] MEERAH🪷🩷

:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘👑

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

🌲🌲DASHEN ALLAH WRITER'S ASSICIATION 🌲🌲

( D.A.W.A ) 🌲🌲

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 9 🥀 ❤
Chapter 15 · 0% Book details