← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 66

Sashe 14

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da a ka dauki lokaci kafin a amsa mata sallamar ta cikin wata zazzakar Sexy voice cike da nitsuwa , da ga jin wanda ya amsa sallamar nan ba ya son yawwan magana

Dan karamin murmushi ta yi jin wannan Muryar ta shi ba karya ta yi mata dadi
Cen kuma sai ta ce " Mister Musadeeq lafya ka kira ni "

Yanzu ma sai da a ka dauki wajen good five minutes kafin a ce " please yi magana da turanci ba na jin haoussa " ya fada da turanci

Dan zaro idanu Safa ta yi cike da mamaki ta ce " ba ka jin haoussa amma ka a yi amsa sallama ? "

Shiru ba a amsa mata ba
" da kai na ke magana " ta sake fada jin an yi mata shiru

Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " ni musulmi ne shi ya sa "
" ahhh , kenan kai balarabe ne " ta fada cikin zolaya
" cikaken bahaoushe ne ni " ya ba ta amsa cikin sanyi

Dan zaro idanu Safa ta yi ta na fadin " what ? Bahaoushe fa kuma ba ka iya haoussa ba , no gaskia ba zai yi yu ba , ban yarda da hakan ba "

Shiru ya yi bai ce mata komai ba , ita ma ba ta ce mishi komai ba har sai da su ka dauki wajen ten minutes a haka kafin ta jiyo sexy voice din shi ya na fadin " ban taso cikin haoussawa ba "

" Duk da haka nan mom and Dad din ka su na jin haoussa , why ba su koya maka ba " ta kai karshen ta na sauko da kafafun ta kassa ta mike zaune

Yanzu ma sai da ya dauki lokaci kafin ya amsa mata da cewa " sun so su koya min , amma na ki "

" Why ? "
" zan kira ki an jima " ya na gama fadar haka ya katse kiran ba tare da ya jira amsar ta ba
Kallon screen din ta yi , ba ta san lokacin da wani cool murmushi ya subce mata ba , ko ba komi ya iya magana , kuma ya na da nitsuwa
A hankali ta koma jikin sofar ta konta , ta na jin yanayi mai dadi na ziyartar ta lokaci guda a haka har lokacin sallat ya yi ta tashi ta koma bedroom din ta
[21/08 à 22:40] null:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫

( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🪷🩷

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION
( D.A.W.A )

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 8 🥀 ❤

▪ABUJA ( KUJE PRISON )

▪MARWAN🪷

zaune ya ke saman wani banci cikin harabar prison din , ya daga kai sama ya lumshe idanu , ya saki wani cool murmushi

Ya na a haka Bachir ya yi mishi sallama ya na fadin ya yi bako
Ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " Bachir , na fada maka in dai wacen mutumin ne , ku daina barin shi ya na shigowa "

" No Sir ba shi ba ne , ina ga wanda ka ce zai fitar da kai da ga gidan nan ne "

Murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya sauko da kan shi slowly ya bude idanun shi ya kali Bachir ya ce " no ba shi ba ne "

Ya kai karshen ya mike tsaye ya fara takawa ya yi gaba , da sauri shi ma Bachir ya juya ya bi bayan shi su ka nufi dakin da a ke kawo ziyara

Bakin shi dauke da sallama cen kassan makoshi ya shigo dakin , ya nufi chair ya zauna ya jingina a bayan ta ya saka hannayan shi a aljihu ya na sakin wani makirin murmushi , ya na kallon wanda ya zo ganin shi

Wani cool murmushi Sami ya saki kafin ya ce " Bro ya ka ke ? "

" kamar yadda ka ga ni ban mutu ba " ya fada a takaice

Kara fadada murmushin Sami ya yi ya na fadin " haba bro , da ga tambaya "

" to ina lafya , shikenan ? "

" haka ya kamata ka ce "

" na ji fada min , me ya kawo wa je na yau , ko ka zo ne ka yi min dariya kamar yadda ka saba " ya kai karshen ya na daga mishi gera guda

A tare su ka bushe da dariya kafin Sami ya ce " kai bro wai har yanzu ba za ka daina wannan tsagar da ka ke ba ? "

Tsagaita dariyar shi Marwan ya yi kafin ya ce " To ya ka ke so na yi , kun kawo ni gidan tantirai dole na koyi tsaga , yanzu fada min ya su momy su ke ? "

Murmushi mai dan sauti Sami ya yi kafin ya ce " su na nan lafya , ka San wani abu ma ? "
Girgiza mishi kai Marwan ya yi allamun a'a
" kawo kunnen ka ka ji " ya fada ya dan gusowa

Ba musu shi ma Marwan ya matso ya mika mishi kunne shi sannan Sami ya rada mishi wani abu

Ban san abun da ya fada mishi ba , kawai sai ganin shi na yi ya saki wani cool murmushi har sai da ya lumshe idanun shi slowly ya bude su

Komawa su ka yi su ka zauna saman chair din su , su na kallon juna an rasa me cewa wani abu
Sai cen kuma Marwan ya ce " wlh Sami ka cika dan sa ido "

Dariya sami ya yi ya na mikewa tsaye ya ce " dole na sa ido mana , mu na nan sake da ba ki , sai dai kawai mu ji an kawo mana katin aure , ni zan tafi sai na dawo " ya kai karshen ya na barin dakin

Dan karamin murmushi Marwan ya yi kafin ya juyo ya kali Bachir ya ce " wlh kayi hankali da yaron nan mugun sa ido gare shi " ya kai karshen ya na mikewa tsaye ya fara takawa ya bar dakin

Bin bayan shi Bachir ya yi ya na yar dariya , ya rasa dalilin da kullum ya ke bala'in son Marwan kamar yan uwan shi na jini

▪UK ( LONDRES )

▪Misalin karfe 10 na dare

wani tanpasheshen parlour ne mai bala'in girma da kyau , Parlourn ya na da bala'in haske duk da cikin dare ne
Wani Chandelier ne fari kal mai bala'in kyau ga haske kuma sai ka rantse da Allah da rana ne
Komai na cikin parlourn da ga Red sai white colour ne , gaskia ya hadu iya haduwa dan da ga gani ba kananan kudade a ka kashe cikin gidan ba ki daya

A hankali ya ke tako stair din , ya na sanye da kayan barci ash colour masu bala'in kyau da laushi

Takowa ya ke yi a hankali kamar an yi mishi dole , da ga gani ka san cikin magagin barci ya ke
Kitchen ya shiga, ya nufi fridge ya bude ya dauki gorar ruwa guda daya sannan ya fito kitchen

A parlour ya tsaya ya zauna saman lamusasun sofas din nan sannan ya bude gorar ruwan ya kai baki

Ya na tsaka da shan ruwan ya jiyo wayar shi na ringing

Sai da ya ida shan ruwan shi sannan ya sauko da gorar ruwan ya rufe ya ajiye kassa geffen shi sannan ya kai hannu cikin aljihun shi ya fido wayar

Bai tsaya dubawa ya dauki kiran ya kai a kunne ya na murmushi ya ce " hello "

Sai da a ka dauki lokaci kafin ya jiyo wata zazzakar murya a na fadin " Yanzu zan shiga jirgi zuwa korea , ka shirya nan da three days zan dawo , ran monday za mu tafi Nigeria "

Kara fadada murmushin shi Amar ya yi kafin ya ce " Da gaske ka ke Ass...... "
Bai karasa maganar shi ba ya ji kiran ya tsinke

Sauko da wayar ya yi ya na dan murmushi ya ce " kai dai ka sa ni ba , dai ka yarda mu je ba , za ka ga abun da zan yi maka "
Ya na gama fadar haka ya mike ya nufi stair ya Haye

▪NIGERIA ( KADUNA )

Wednesday : 10Am

▪Safa 💋

A hankali ta ke tako stair din gidan , kan ta a sunkuye ta na latsa wayar ta
Ta na sanye cikin wando palazzo Red colour da shirt mai dogayen hannu white colour , ta saka dan karamin hijab zuwa kirji shi ma red colour , ta saka wasu sneakers a kafafun ta farare kal kamar ba a taka kassa da su , ita dai duk kayan da za ta saka sai ta yi musu dress code ba ta iya sa kaya barkatai ba haka tai ta harhada colours

Sai da ta sauko stair din ta nufi table din tsakiyar parlour ta dauki yar jakar ta da ke sama
Ta bude ta saka Wayar ta a ciki , sannan ta rataya jakar , ta dauki key din motar ta sannan ta juya ta fice parlourn

Kai tsaye parking space ta nufa , ta shiga motar ta , ta kunna ta ta bar gidan da gudu

Cikin abun da bai fi five minutes ba ta iso university din su
Ko da ta shigo ba ta wani shiga class ba , kai tsaye library ta wuce , dan ita dama wajen Haoua ta zo ba yin lectures ba

Kamar ko ta sani ta na shigowa library din ta hango su zaune ita da Djamila ko wace ta na rike da book's din ta ta na karantawa

Su na a haka hawa ta ga an ajiye mata wasu box guda biyu a gaban ta duk farare amma ta sama ta fi dan girma
Chapter 14 · 0% Book details