← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 66

Sashe 6

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

" na yi kewar ki ni ma momy " Safa ta fada hawaye na zubar mata
Raba jikin su matar nan ta yi da na Safa kafin ta juya ta kali yarinyar nan ta ce " Noor kawo wa sister din ki ruwa mana "

Har Noor ta juya ta nufi dining room Farida ta taro ta da cewa " ke malama tsaya nan ba gidan ciyar da marayu ba ne "

Murmushi takaici Safa ta yi kafin ta ce " no momy ni ba na bukatar komi, na zo ne kawai don na gan ki , tun na gan ki yanzu zan koma "

Ba ta gama rufe bakin ta ba Fadila ta ce " haii barka to malama sai a fice mana da ga gida " ta kai karshen ta na shirin sa hannu ta tura Safa

Da sauri Snoopy ya shiga tsakiyar su ya na kallon Fadila ya yi mata wani irin haushi har sai da ta saki kara ta yi baya da gudu

Da sauri Safa ta ce " kai Snoopy ya isa haka "
Wani dan karamin haushi ya yi kafin ya girgije ya koma bayan Safa ya tsaya
" momy ni na tafi amma zan dawo " ta kai karshen ta na rungumar macen

Sannan ta sake ta ta rungume Noor ta na fadin " mun yi waya kin ji ko "
Ta na gama fadar haka ta raba jikin su ta juya da sauri ta fice parlourn Snoopy na biye da bayan ta
Ta fita wasu hawaye masu zafi su ka zubo wa matar da Safa ta kira da momy
Fadila da Farida na ganin haka su ka kali juna sannan su ka bushe da dariya

Kallon su momy ta yi kafin ta ce " why za ku yi mata haka , kanwar ku ce ita ma sannan cikin gidan mahaifin ta ta ke , kar ku manta lokacin da ya k...."

Da sauri Fadila ta katse ta da cewa " ke Twinkle ki shiga tayi tayin ki , wlh kin ci darajar ki na matar Daddy da sai na yi miki dan bazan duka "

Hararrar ta Noor ta yi kafin ta ce " ke da dan karamin kare ya bawa tsoro yanzu shi ne za ki wani ce ki ma mutun dan banzan duka , ko kunya ba ki ji "

Mikewa tsaye Fadila ta yi ta na kallon Noor ta ce " ke yar samudawa, ki fita da ga ido kin ji ni ko , in ba haka ba gidan zai yi mana kadan "

Juyo wa da kyau Noor ta yi ta na kallon ta cikin ido ta ce " takamar ki daya ki ce ki na cikin gidan uban ki , kar ki manta ni ma uba na ne , wlh in ki ka ce za ki taba ni sai na yi miki Dukan mutuwa dan ba karfi na ki ka fi ba "

Da sauri Twinkle ta riko hannun ta ta na fadin " ke Noor rabu da ita wuce mu tafi "
Kwace hannun ta Noor ta yi ta na fadin " momy ki kyale ni na gwada mata na fi ta jin abun da ta ke takama "
" don Allah noor wuce mu tafi " ta fada ta na marairaice fuska dan ba ta son tashin hankali , ba dan ta so ba su ka juya ita da TWINKLE su ka haye stair
Su na barin wajen Fadila ta ja tsaki ta koma ta zauna ta na fadin " aikin banza "

Share fisabillilah 🙏🤌❤️
💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫

( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑❤✌

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com
/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 4 🥀 ❤

Safa 💋

Ta na baro parlourn wasu hawaye masu zafi su ka zubo mata
Da gudu ta nufi karamar gate za ta barin gidan
Har ta karaso bakin kofar , wani saurayi ya turo ta ya shigo
Cak ta tsaya ta na kallon shi , dan tsoro har wata yar kerma ta ke

Saurayin ya na da dan tsayi fari ne amma ba kwarai ba , ya na da murdaden jiki amma ba sosai ba cen , ya tara dan neman gashi ya zubo mishi har saman shoulder , ya na da kontancen saje mai kyau ya hadu dai dai gorgaudo , ya na sanye da wando jeans navy blue , da shirt fara mai dogayen hannu a shekaru zai kai 31 years haka

Ya na ganin Safa ya matse fuska ya tako ya tsaya gaban ta cikin tsare gida ya ce " me ki ke yi nan ? "
Safa ba ta ce komai ba sai faman muzurai ta ke da idanu ta na kallon shi

Ganin yadda ta ke kallon shi ba ta bashi amsa ba hakan ya bata mishi rai har ya daka mata tsawa
Da sauri Snoopy ya shiga tsakanin su ya na yi mishi haushi da karfi ya na gurnani
" kai malam yi min shiru , ba ki iya tafowa ke kadai sai kin tafo da wannan dabbar ta ki , ai dama ku na kama " ya fada

Dan sunkuyar da kai Safa ta yi ta daga kafa za ta raba ta geffen shi
Da sauri ya riko hannun ta ya medo ta baya har sai da ta nemi faduwa ya ce " ba ki ba ni amsar tambaya ta ba , me ki ke yi a nan ? "

Cen kassa kassa ta ce mishi " good morning Sami , wajen momy na na zo "
Dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " Safa , cikin gidan nan ba ki da wata momy , don Allah ki manta da ita , na san ki na yawwan zowa nan , kin san idan Daddy ya gan ki wlh ba za ki ji da sauki ba , idan ki na son magana da ita ki kira ta a waya , kar ki yi tunanin dan ba ni son ki na fada miki hakan , a'a saboda tsaro ne na san duk ranar da Daddy ya kama ki hmmm , za ki iya tafiyar ki "

Jinjina mishi kai ta yi kafin ta fara takawa ta bi ta geffen shi ta wuce
Har ta kai bakin kofa ta jiyo Muryar shi ya na fadin " na ga videos din da ki ka saki yanzu da jimawa , congratulations Allah ya bada sa'a "

Da sauri ta juyo ta kaleshi ta na zaro idanu
Daga mata gera guda ya yi kafin ya ce " me ki ke tunani , tun kafin ki kai wannan lokacin na ke bibiyar ki dukanin account din ki na san da su , kuma na san abun da ki ke yi a ciki , i'm really happy for you , kar ki yi tunanin saboda abun da ya faru zan juya miki baya ni ma , babu yanda zan yi ne kawai , ki kula min da kan ki , idan na samu dama na je cen gidan ku " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi cikin gidan

Safa kuma da kallo ta raka shi har sai da ya shiga cikin gidan sannan ta sa kafa ta fice gidan zuciyar ta duk ba dadi

Motar ta ta nufa ta budewa Snoopy wajen shi ya shiga sannan ta zagayo ta bude kofar driver ta shiga

Ko da ta shiga ba ta tada motar kai tsaye ba , sai da ta hada kan ta da steering motar ta na fadin " why Daddy ? Why za ka tafi ka barni , ina matukar kewar ka Daddy , na san duk inda ka ke a yanzu ka na tunanin mu , duk da na san ba za ka iya dawowa ba " ta kai karshen kuka na kubce mata

Marairaice kukan shi Snoopy ya yi ya na konto da kan shi saman shoulder din ta
Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " shikenan na ji , tashi mu tafiyar mu "
Ta fada ta na dago kan ta , ta kai hannu a ciro handkerchief ta goge hawayen ta sannan ta tada motar su ka bar wajen

Kaduna ( G.R.A )

Misalin karfe 5 na yamma Safa ta dawo cikin gidan su
Ta isko gidan babu kowa sai balki da ke aikin ta , ba ta tsaya batta lokaci ba ta wuce bedroom din ta , ta shiga toilet ta yi wanka ta dauro Alwalla

Sannan ta fito ta shiga dressing room ta shiryo cikin wata gown mara nauyi ta sanyo hijabin ta sannan ta fito ta nufi wajen da sallayar ta ta ke ta gabatar da sallar Azahar sa la'asar da ba ta samu ta yi ba saboda hanya

Bayan ta Kamala sallar ta , ta tashi ta koma cikin dressing room
Jim kadan ta fito sanye da wasu tracksuit ma su bala'in kyau pink colour , rigar mai dogayen hannu ce amma ba ta ida rufe cibi ba , kafafun ta sanye da sneakers pink colour su ma ta na sanye da wasu gloves bakake a hannu

Kai tsaye bedroom din ta fito , ta na gyara gloves din hannun ta
Bedroom din da ke geffen nata ta shiga , wani babban Gym ne dauke da kayan motsa jiki kala kala masu kyau kamar sabi

Wajen wani treadmill ta nufa , ta Haye sannan ta yi wasu yan dane dane machine ta kama
Sannu sannu ta fara tafiya saman shi kafin ta kara karfin tafiyar ta ta har ya kai ta fara gudu kamar za ta tashi sama
Ta dauki wajen good 30 minutes ta na wannan gudun babu ko gajiya kafin ta fara ragewa har machine din ta tsaya , sannan ta sauka ta koma gefe ta na meda nunfashi , zufa na karayo mata kamar wadda a ka watsa ma ruwa
Chapter 6 · 0% Book details