← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 66

Sashe 53

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin sigar rarrashi His excellency ya ce mata " Haba My Twinkle ba abun da su ka yi min wassa ne fa na ke mata , kamar dai ba ki san halin yarinyar ki ba da son karawa miya gishiri , ai a haka na gani kuma na ce ina so , My first lady "

" His excellency na ce maka ka daina kira na da Twinkle , kai fa ka sauya min sunan nan kuma yanzu shi ne za ka ci gaba da kira na da hakan ni gaskia ba na so " ta na gama fadar haka ta mike ta fara takawa ta nufi stair ta Haye 

da kallo ya rakata har sai da ta Haye sannan ya juyo ya kali Safa ya ce " momyn ki rigima gare ta wlh , ni ban ma san ya a ka yi na fada soyayyar ta ba da wasu kananan idanun ta kamar na yan china "

wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Daddy , momy fa ta fi ka kyau "

" oun na sani , ai kyawon ta ya na daya da ga cikin dalili na na auren ta "

" Da gaske Daddy ? Fadamin yadda a ka yi ku ka hadu da momy "

wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " shikenan bari na ba ki labari , a lokacin ina da shekara 28 haka ina a aiki a matsayin doctor , to sai mu ka tafi china wajen wani karin karatu , duk cikin Nigeria mu hudu ne kawai mu ka samu wannan damar , bayan mu je China , mun dan yi kwana biyu haka mun huta sai a ka dauke mu a ka kai mu wani babban Hospital wanda za mu fara aiki a cen , a ranar kuma momyn ta shigo Hospital din sun kawo mahaifin su ba shi da lafiya , Ta na sauke idanu sama na ta ji babu wanda ta ke so sama da ni "

ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Twinkle ta katse shi da cewa " I know , I have a good memory , but i don't think haka abun ya faru kamar yadda ka ke fada "

a hankali His excellency ya dago kai ya kale ta ta na sauko stair a hankali har ta karaso cikin parlourn ta dawo geffen shi ta zauna 

murmushi mai dan sauti His excellency ya yi kafin ya ce " ki bari na gama ba ta nawa labarin sai ki ba ta naki "

" okay ci gaba " ta fada ta na daura kafa daya bisa daya ta zuba mishi ido

dawo da kallon shi ya yi kan Safa ya ce " ki na ji ko , Ta na sauke idanu sama na ta ji babu wanda ta ke so a duniya sama da ni , ni kuma a lokacin ban lura da ita ba ina kan aiki na , kuma cikin wani ikon Allah duk doctors din da ke cikin Hospital din , ni ne a ka bawa damar kula da mahaifin ta , sannu sannu na fara duba shi har mu ka share wajen one week ina tare da su amma ko so guda gaisuwa ba ta taba shiga tsakani na da ita , a haka har a la sallame su , kwana biyu bayan an sallama me su , na je wani Mall yin shopping , a nan na sake haduwa da ita , ita ta fara yi min magana ta gaishe ni ta ce min ita ce yarinyar majinyacin nan da na yi wa,magani , na ce mata eh na gane ta , da ga nan ta shiga yi min godiya na ran mahaifin ta da na ceto , na nuna mata ba komai duk cikin aiki na ne , a haka mu ka ci gaba da yin shopping din a tare mu na tafe ta na yi min hira a kan ta , bayan mun Kamala mu ka je reception na ce ta bari zan biya amma fir ta ki ta ce ita za ta biya saboda irin al'herin da na yi mata ba za ta iya bari na biya ba , haka mu ka shiga jayaya da ita har dai na hakura na bari ta biya , da ga haka mu ka baro Mall din amma kafin nan sai da ta karbi number ta , ta ce min za ta dinga kira na mu gaisa , da ga haka mu ka yi sallama , sannu sannu mu ka fara sanin juna ta na sake min , mu na wassa da dariya , mu na haduwa bayan na sauka da ga aiki , mu tafi shan coffee ko shan ice cream  , wani lokaci  ma mu tafi kallon film har soyayya ta shiga tsakanin mu , soyayya mai karfi yadda ko kwana ba ma iya yi ba mu ga juna ba , a haka har na Kamala aiki na a China , na komo Nigeria ko bankwana ban yi mata ba , amma tun bayan dawowa ta ba abun da na ke tunani sai ita na kassa barci , na kassa cin abincin har jinya na yi a Asibiti , family na ba rokon da ba su yi min ba na fada musu abun da ke damu na amma fir na ki yarda , a haka har na share wajen two months , a cikin na ukun na yanke shawarar komawa China dan na gan ta , sai dai ko da na koma china na neme ta na rasa , ashe bayan komawa ta Nigeria ita da familyn ta sun koma UK da zama , babu yadda na iya na kama hanya na dawo Nigeria inda na sake kontawa sabon ciwon , na rashin ta a kusa da ni , dan duk duniya ita kadai ce macen da na taba fadawa kalmar so yanzu kuma ga shi mun rabu , sannu sannu har sai da na share one year a haka , a cikin shekarar ba yin da ahali na ba su yi da ni ba a kan na yi aure ko zan samu saukin abun da na ke ji duk da ba su san abun da ke damu na ba , amma na ce ba na so saboda mace guda na ajiye wa gurbin mata a waje na kuma bayan ita babu wadda zan bawa , kawai watarana na je Hospital sai secretary di ta ta ce min na yi bakuwa , amma ta ce ta tafi an jima ta dawo , kawai na ce mata okay , after some hours ta dawo ta ce min guest di ta ta dawo kuma ta na son gani na yanzu , da ya ke a lokacin saura 30 minutes na sauka sai na ce mata kawai ta shigo , ba musu ta je ta ce ma bakuwar na ce za ta iya shiga , Jim kadan na ga an turo kofar office di na a shigo , lokacin da ta shigo kai na ya na sunkuye na ce mata ta zauna , ba musu ta karaso ta zauna ta na kallo na da murmushi a fuskar ta , sai na tambaye ta abun da ya kawo ta waje na sannan na dago kai , ina ganin ta na ji zuciya ta ta buga da karfi tamkar a mafarki haka na ke ganin ta wani kyawatencen murmushi ta sakin min ta daga min hannu ta ce HI , mamaki ne ya hana ni magana kawai na tsaya ina kallon ta babu ko kiftawa , ganin yadda na tsare ta da idanu ya sa ta cewa DEAR BA KA GANE NI BA ? ban san lokacin da wasu hawaye su ka zubo min ba , da gudu na tashi na je na rungume ta cikin fitar hayaci kamar wani ya ce zai kwace min ita , kin san abun da ya faru , ashe lokacin da na dawo da ga China bayan na je neman ta a lokacin ita ma ta je nema na kawai dai mun yi crossing ne ,
inin ranar a tare mu ka share shi , amma na fada mata ba zan iya ci gaba da soyayya da ita saboda ita ba musulma ba ce , ni duk na manta da wannan tun farkon soyayyar mu sai a lokacin , ta yi kuka kamar za ta hadiye ran ta , amma haka na danne mu ka rabu da juna , a tunani na ta koma UK a ranar ashe ba ta koma ba , washe gari early ina shigowa office ita ce guest na farko da ta zo waje na , na roke ta ta tafi saboda ba za mu iya kasance wa a tare ba tun farko laifi na ne da na manta ita ba musulma ba ce , haka ta dinga yi min magayi ta na kuka a kan kar na rabu da ita , har ta ba ni labarin auren da a ka yi kokarin yi mata bayan komawar su UK amma ta cere , har ciwon zuciya ya kamata ta shiga doguwar suma na sati biyu , ba za ta iya jure rayuwa babu ni ba , duk da ni ma ba zan iya rayuwa babu ita ba amma haka na danne zuciya ta na ce mata ta yi hakuri ba zan iya zama da ita ba , da ga haka na tashi zan bar mata office din saboda ba zan iya jure ganin hawayen ta ba , har na kai bakin kofar na jiyo Muryar ta ta na cewa ta yarda za ta karbi addini na , in har ta hakan ne kadai za mu iya kasancewa a tare na takaice miki labarin , momyn ki ta karbi kalmar shahada a ka daura mana aure , da farko familyn mu sun ki yarda saboda launin fatar mu , amma da mu ka nuna musu mu na son junan mu su ka yarda da auren mu , amma duk wannan abun familyn momyn ki ba su San cewa ita musulma ce a yanzu kuma na sauya mata suna na saka mata MRS MARWA ABDOUL KARIM , My Twinkle , My first lady , the love of My life " ya kai karshen ya juyawa ya kali Twinkle 
Chapter 53 · 0% Book details