← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 66

Sashe 58

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

girgiza mata kai Safa ta yi kamar za ta yi kuka ta ce " no , ni ki fara ba wa baby na abinci "

wani dan karamin murmushi Aziza ta saki kafin ta ce " shikenan kar ki damu , na sayo mishi meat , Idan mun je cen sai mu saya mishi abincin dog "

cikin nitsuwa Safa ta katse ta da cewa " Idan mun je ina Aunty ?  "

cak Aziza ta tsaya ta na zaro idanu , murya har kerma ta ke ta ce " no ina nufin idan mun dawo da ga dauko chocolate din ki , sai mu biya Mall mu sayo mishi "

wani dan karamin murmushi Safa ta sakin mata kafin ta ce " okay " a takaice 

" shikenan yanzu sauke shi kassa " Aziza ta fada , ta na ajiye ledar hannun ta kassa wajen kafafun Safa

ba musu ta sauke Snoopy kassa wajen Ledar ta ne ce mishi " baby , ga abinci ka ci please "

a hankali Snoopy ya daga kafa ya nufi ledar , jikin shi har kerma ya ke
ba karya fa ya na jin yunwa , dan tun safe Safa ba ta ba shi komai ba sai faman wassan da su ka sha

a hankali ya sa hancin shi cikin ledar ya na shinshina
wani dan karamin haushi ya yi kafin ya fara cin naman nan
Safa na ganin Haka ta saki wani murmushi mai dan sauti

Ita ma Aziza murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce ma Safa " Shikenan tun da ya ci , yanzu karbi ice cream din ki sha tun ba ta narke ba "

ba musu Safa ta kai hannu ta karbi ice cream din nan ta karbi yar spoon din ta fara shan ice cream din nan ta na murmushi

Aziza kuma sai kallon ta , ta ke ta na murmushi , ta rasa dalilin da ya sa ta ke mugun son Safa haka , har cikin ran ta  ta ke son ta , a ranar da ta shigo duniya a ranar ta dawo Nigeria , ta na ganin ta ta ji babu abun da ta ke so a duniya kamar Safa
ba rokon da ba ta yi wa His excellency ba ya bar mata ita , ko da ta dawo nan Nigeria da zama ne , amma ya ce ba zai iya raba Twinkle da yarinyar ta ba
ba dan ta so ba ta hakura ta koma RUSSIA , amma kullum ta na tunanin Safa , ga shi ba ta taba yin aure ba , ko wani boyfriend ba ta da shi bare ta yi tunanin aure
ita a rayuwar ta auren ne ma duk a ba ta so , dan ta sha samun tambayar aure sau dayawa amma ta ki yarda , kuma ba ta taba damuwa da cewa ba ta da baby ko guda , ko Marwan da ta tafi da shi , sai da His excellency ya matsa mata a kan ta tafi da shi sannan ta yarda
ba dan haka ba , ba wani kula da yaro a tsarin rayuwar ta , ta fi son ta yi rayuwar ta ita kadai ta na sha'anin yadda ta so
dalilin da ya sa ma ta gudu RUSSIA saboda kar su takura mata a gidan su

amma ta na sauke idanu saman Safa ta ji dama a ce babyn ta ce , dalilin da ya sa ta roki His excellency ya bar mata Safa amma ya kassa , ya na ganin kamar ba zai kyautawa Twinkle ba idan ya dauki yarinyar ta guda ya bawa sister din shi
ga shi Marwan ma a wajen Aziza ya ke , kenan ya raba ta da duk yaran ta

sai da Safa ta Kamala Shan Ice cream din ta sannan ta kali Aziza ta ce " Aunty bowl din fa ? "

wani cool murmushi Aziza ta sakin mata kafin ta kai hannu ta zuge glass din da ke geffen Safa ta karbi bowl din ta tila sannan ta meda glass din ta tada motar su ka bar wajen ta na tafiya a hankali

ba su yi five minutes da barin wajen ba , kawai Safa ta konta jikin Sofar ta lumshe idanun ta , ba jimawa barci ya yi gaba da ita

Aziza na sane amma ba ta ce komai ba , ta ci gaba da tukin ta , har sai da su ka karaso Airport , ta yi parking din motar ta , ta sauko
ta bude gidan baya ta fiddo wata babbar bag irin wadda a ke saka kaya
ta ratayo ta a saman shoulder din ta
sannan ta zagayo geffen Safa , ta bude kofar ta sa hannu guda ta dauki Safa ta daura ta saman shoulder din ta
sannan da gudan ta dauki Snoopy da ke Faman barci shi ma
ta nufi hall din Airport din nan ta shiga da su a haka

ta na shiga ko , jirgin da zai tafi UK ya fara shirye shiryen tashi
kai tsaye wajen Reception ta na nufa Already ta riga da ta saya musu ticket
[22/09 à 15:01] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
                        ( YAR JARIDA )

🌸💖 ( A heart touching love story & destiny ) 💖🌸

STORY & WRITTEN BY : MEERAH  👑🌸

【THE ROYALTY LOVE 🕊🌸💕】

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 :FREE BOOK

❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤ : PAID BOOK

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP POSTING ROOM

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/BBWVomizhgVKzcxJo4XRpG

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite

               BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

___________________________________________

LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN , COMPLETE KUMA 400

GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE ⚘❤
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
👇👇👇👇
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
👇👇👇👇👇
Zain (Airtel)
08081129487 

sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753

     ___________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊____________________

              { PAGE 29 🥀 ❤ }

Already ta Riga da ta saya musu Ticket , ta na isa ta gwada musu ticket din
nan take su ka isa da ita wajen Jirgin , daya da ga cikin Server ta karbi bag din ta da Snoopy ta ce ba za ta iya shiga jirgin da dog ba , akwai wajen da a ka tanada specially saboda pet

ba musu Aziza ta ba ta Snoopy ta shiga cikin jirgin da Safa da ke faman barci ba ta ma san inda kan ta ya ke ba

after one hour sun Kamala duk wani shirye shiryen da za su yi jirgin su ya daga ya nufi Hanyar UK

    ▪GIDAN HIS EXCELLENCY

Misalin one hour bayan Fitar su Safa , Ali ya shigo cikin parlourn babu ko sallama kamar a koro shi
a rude Twinkle ta mike ta na fadin " babban yaya , lafiya dai ? ka yi irin wannan shigowar babu ko sallama ? "

cikin tashin hankali ya ke ce mata " Babu lafiya Twinkle , maza taho mu tafi " ya fada ya na riko hannun ta ya ja ta su ka nufi hanyar fita parlourn 

a rude Twinkle ke ce mishi " babban yaya me ya faru ne wai , ku tsaya na dauko veil di na mana "

bai saurare ta ba ya ja ta su ka bar gidan da sauri sauri sai tambayar shi ta ke me ya faru amma bai ce mata komai ba , har sai da su ka fito gidan
nan ta ga motar shi ya yi parking din ta bakin kofar gidan

kai tsaye wajen mai zaman banza ya bude mata ya ce ta shiga 
kin shiga ta yi ta na cewa " Babban yaya wai me ya faru , ka fada min abun da ke faruwa , wani abu ya samu His excellency ? " ta fada idanun ta na kawo ruwa lokaci guda 

da sauri ya ce mata " Twinkle ki shiga motar nan , zan fada miki abun da ke faruwa "

ba musu ta shiga cikin motar ta sa belt
da sauri ya zagayo wajen driver ya shiga ya tada motar ya yi baya da ita ya juya ya bar wajen da mugun gudu

su na barin wajen Twinkle ta juyo ta kale shi ta ce " Babban yaya wai me ya faru ? "

ba ta gama rufe bakin ta ba ya ce " ki yi hakuri Twinkle gidana zan kai ki yanzu , akwai matsala , ban san yadda a ka yi ba su ka san Marwan ya dawo garin nan ba , har ya na shirin komawa , yanzu haka da ga mosque na ke , an kama his excellency da Marwan wai su na neman guduwa , Na kira Aziza na ce mata ta bar garin da Safa har mu warware wannan case din , ke kuma zan boye ki a gida na "

har Twinkle ta bude baki za ta yi magana ta ji wata razananiyar kara kamar tashi bomb da ga bayan su har sai da ta saki kara ta toshe kunnuwan ta
a razane ta dago ta juya ta ga ashe gidan su ne Bomb ta tashi da shi

wata irin razananiyar kara ce ta saki , nan take jinin ta ya hau ta sulale jikin sofar ta suma 

Ali na ganin ta suma ya saki wani kyawatencen murmushi , ya rage gudun da ya ke , ya fara tukin shi cikin konciyar hankali

               ▪AFTER TEN MINUTES 

a hankali Twinkle ta ware idanun ta , ta na karanto kalmar shahada a hankali
slowly ta mike zaune ta na bin parlourn da kallo
cen ta ga Ali zaune saman Sofa ya yi tagumi ga damuwa nan konce saman face din shi

a dubu dari Twinkle ta mike ta na fadin " babban yaya ina his excellency ya ke ? ina Marwan ? ina yaro na ya ke ? " ta kai karshen ta na sakin kuka 
Chapter 58 · 0% Book details