← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 66

Sashe 57

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

a dubu dari Sami ya dago kai ya na cewa " why , no gaskiya ni UK zan koma , ya ka ke so ka tsayar min da karatu na lokaci guda haka , why Daddy ? "

cikin ba da umarni Ali ya ce mishi " ba shawarar ka na ke nema ba , Umarni na ke ba ka , dan haka tashi ka koma bedroom din ka babu inda za ka je "

cikin bacin rai Sami ya mike ya na fadin " sorry dad ni gaskiya ina son na je na ga Marwan " ya fada ya na kokarin takawa 

cikin tsawa Ali ya ce mishi " Sami ka koma bedroom din ka na ce "
cak Sami ya tsaya ya na kallon shi,  irin kallon nan na takaici kafin ya juya ya koma ya Haye stair
da kallo Ali ya raka shi har sai da ya Haye sannan ya saki wani dan karamin tsaki ya kauda kai gefe

         ▪GIDAN HIS EXCELLENCY

zaune Safa ta ke cikin parlourn Gidan su , Snoopy na zaune saman Cinyoyin ta , sai wassa ta ke yi mishi
ta na a haka Twinkle ta sauko Stair ta na fadin " Safa lokacin Sallat ya yi ko ba ki gani ba ? "

" na gani momy " ta fada ba tare da ta kale ta ba
" me ki ke jira tom , ajiye Snoopy ki tashi ki je ki yi " ta fada ta na karasowa cikin parlourn

" okay momy " ta fada ta na ajiye Snoopy Saman sofa ta sauko da gudu ta nufi Corridor din kassan Stair ta shige 

da kallo Twinkle ta raka ta har sai da ta shiga sannan ta saki wani murmushi mai dan sauti ta na girgiza kai ta ce " wannan yarinyar " ta kai karshen ta na zama Geffen Snoopy ta daura hannun saman kan shi ta na shafawa

ta na a haka Aziza ta turo kofar parlourn ta shigo ta na sallama
Twinkle na ganin ta ta saki wani kyawatencen murmushi ta mike ta na cewa " hmmm ni har na fara fushi na zata kin manta da mu "

wani kyawatencen murmushi ita ma Aziza ta saki ta nufi Twinkle ta rungume ta ta na fadin " Sorry Sister , na biya wajen Yah Ali ne , hope na same ku lafiya ? "

a hankali Twinkle ta raba jikin ta da na Aziza ta na cewa " lafiya lau ya ki ke ? ya hanya ? "
da ga haka su ka nufi Sofa su ka zauna a tare sannan Twinkle ta shiga kwallawa Maid kira 

da gudu wata Maid ta fito da ga dining room ta nufi su Twinkle ta runsuna ta gaishe da Aziza cikin girmamawa sannan ta ce " madam ku na bukatar wani abu ? "

" yeah kawo wa bakuwar mu abun tabawa " Twinkle ta fada 

" okay " Maid din nan ta fada ta na dan runsunawa kafin ta mike ta juya ta koma kitchen

ta na shiga Twinkle ta juyo ta kali Aziza ta ce " Sai dai fa ki yi hakuri dan uwan na ki sun tafi mosque tare da Marwan "

murmushi mai dan sauti Aziza ta yi kafin ta ce " ba komai , ai ni dama ba shi na zo gani ba , wajen yarinya ta na zo , ina ta ke ma ban gan ta ba ? "

murmushi mai dan sauti ita ma Twinkle ta yi kafin ta ce " ta na sallat bari na je na kira miki ita "
ta fada ta na kokarin tashi , sai ga Safa ta fito da ga cikin corridor din da gudu

cak ta tsaya ta na kallon Aziza ta na zaro idanu
wata yar karamar kara ta saki kafin ta nufi Aziza da gudu ta fada jikin ta ta na dariya

ita ma yar karamar dariya Aziza ta yi kafin ta sa hannu ta dauki Safa ta daura ta saman cinyar ta , ta ce " My daughter , na yi kewar ki over "

" Ni ma na yi kewar ki sosai Aunty na " Safa ta fada ta na rungume ta

" Shikenan , kin san wani abu ? na kawo miki tsaraba , har da chocolate , amma gaskiya ki yi hakuri na manta ta a gida , sai dai gobe idan na dawo na biyo miki da ita " ta fada dan ta san halin Safa da mugun son Sugar specially Chocolate da ice cream shi ya sa ta ce mata hakan da ta yarda ta biyo ta cikin ruwan sanyi 

nan take ko Safa ta sakin mata kukan Shagwaba ta na cewa " Ni gaskiya Aunty mu je yanzu mu dauko chocolate di ta "

cikin sigar rarrashi Aziza ta ce mata " ki yi hakuri my daughter ba ki ga dare ya yi ba "

ai ko wannan karan kukan gaske Safa ta saka mata , hawaye na zubo mata bibiyu ta na wuntsila kafafu 

" Aziza ke ma kin san halin yarinyar ki da son chocolate dama ba ki yi mata maganar ba " Twinkle ta fada cikin sanyin murya 

" Ki yi hakuri Sister wlh mantawa na yi , kuma a tunani chocolate din su na cikin mota ta wlh shi ya sa na fada mata , ki yi hakuri kin ji my daughter ? gobe zan kawo miki chocolate din ki " Aziza ta fada cikin Sigar rarrashi

amma ina Safa ko jin ta ba ta yi sai ma kara sautin kukan ta da ta ke yi
wani dogon nunfashi Twinkle ta ja kafin ta ce " kin ga Aziza , tashi ku je ku dauko chocolate din , idan ba haka ba wlh ba za mu yi barci ba , zan fadawa His excellency "

gyada mata kai Aziza ta yi kafin ta kali Safa ta ce mata " shikenan , shikenan , tashi mu je mu dauko chocolate din "

nan take Safa ta yi tsit kamar ba ita ba ce me yin kuka yanzu , da sauri ta diro da ga saman cinyar Aziza ta na janhannun ta ta na cewa " tashi mu tafi Aunty "

wata yar karamar dariya Aziza da Twinkle su ka yi a tare kafin ta mike tsaye ta kali Twinkle ta ce " sister ba za mu jima ba yanzu za mu dawo "
da to kawai Twinkle ta amsa musu , da ga haka su ka fara takawa su ka nufi hanyar fita parlourn

har sun kai bakin kofar Safa ta saki hannun Aziza ta dawo da gudu cikin parlourn ta Haye sofar da Twinkle ke zaune ta kai dan bakin ta saman kumatun ta , ta manna mata kiss sannan ta ce mata "  i love you momy "

da ga haka ta diro da ga saman sofar ta nufi Snoopy da ke faman barcin shi ta sa hannayan ta biyu ta dauke shi kamar baby ta nufi Aziza ta na cewa " Aunty mu tafi "

dan karamin murmushi Aziza ta saki kafin ta bude kofar da gudu Safa ta yi waje , sannan ita ma Aziza ta bi bayan ta  su ka bar parlourn
da kallo Twinkle ta raka su har sai da su ka fita sannan ta saki wani cool murmushi ta kai hannu saman table din tsakiya ta dauki wayar ta , ta fara latsawa

bangaran Safa kuma kai tsaye Hanyar parking space su ka nufa
su na tafe Safa na jujuyawa ta na wassan nin ta
Aziza kuma na kallon ta , ta na sakin wani kyawatencen murmushi 

sai da su ka iso parking space sannan Aziza ta budewa Safa bangaran me zaman banza ta na cewa " wannan babyn da ga ina ? "

shiga cikin motar Safa ta yi ta zauna sannan Aziza ta rufe mata kofar
ta zagayo wajen driver ta bude kofa ta shiga ta tada motar 
sai da su ka baro parking space sannan Safa ta juya ta kale ta , ta ce " Aunty , Sunan shi Snoopy , he is my baby " ta kai karshen ta na rungume Snoopy tsam a jikin ta

wata yar karamar dariya Aziza ta yi kafin ta ce " yi a hankali kar ki ji mishi ciwo mana "

a hankali Safa ta saki Snoopy ta daura saman cinyar ta , ta na cewa " baby za ka sha chocolate ? "

wani dan marairaicin haushi ya yi mata ya na komawa ya dunkule waje guda allamun barci ya ke ji

ta na ganin haka Safa ta marairaice fuska ta kali Aziza ta ce " Aunty me ya same shi ? "

" ina ga yunwa ya ke ji , Kin ba shi abincin ? " ta tambaye ba tare da ta janye kallon ta da ga saman hanyar su ba

girgiza mata kai Safa ta yi ta na cewa " No , Aunty mu biya restaurant mu saya mishi abincin kar wani abu ya samu baby na " ta kai karshen ta na marairaice fuska 

wata yar karamar dariya Aziza ta yi dai'dai lokacin da ta yi parking cikin wani Restaurant
a hankali ta juyo ta kali Safa ta ce mata " shikenan ki zauna ki jira ni kar ki fito "
da to kawai Safa ta amsa mata

a hankali Aziza ta juya ta bude kofar motar ta , ta fito sannan ta rufe motar ta saka mata key yadda Babu wanda zai iya bude ta

da ga Haka ta daga kafa ta shiga cikin Restaurant din
Safa na kallon ta , har sai da ta shiga cikin restaurant din sannan ta sunkuyo ta kali Snoopy ta fara shafar shi

jim kadan Aziza ta fito da ga cikin restaurant din rike da wata yar karamar leda , sai wani dan bowl a hannun ta allamun na Ice cream  ne

kai tsaye motar ta , ta nufa ta sa key ta bude ta , sannan ta bude kofar driver ta shiga ta na fadin " Dubi na sayo miki Ice cream "
Chapter 57 · 0% Book details