← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 66

Sashe 61

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri Marwan ya katse shi da cewa " ka ga Sasha ka fita da ga harka ta da ta cake di na wlh , tsaya ma tukunna sai yanzu ka tuno da ni , ka san tsawan shekara nawa na yi ina jiran ka , duk wasu hujoji da zai nuna ba ni da laifi sai da Sami ya tara su , zai meda karar a kotu dan ya fitar da ni da ga nan amma na hana shi kawai saboda kai , why za ka dauki lokaci haka ? ni fa duk duniya bayan Allah da kai kadai na dogara dan barin gidan nan , amma ka share ni , dan haka ka kyale ni na ci cake di na malam " ya kai karshen ya na cika spoon din shi da cake ya kai baki ya na hararrar Assad ta wutsiyar ido

kallon shi da kyau Assad ya yi , sai da ya ga ya gama cinye cake din bakin shi , sannan ya mike da ga saman chair din shi ya rungume Marwan ya na fadin " na yi kewar over , ko wace safiya da tunanin ka na ke tashi , wannan karan shi ne na uku ina zuwa Nigeria neman ka , amma sai yanzu na samo ka , i'm sorry , I'm sorry na bar ka a wajen nan tsawan shekaru "

wani dan karamin murmushi Marwan ya yi kafin ya rungume Assad ya ce " ni ma yi kewar ka over "

ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Safa ta na kuka
da sauri Ya raba jikin shi da na Assad ya na kallon ta ya ce " sister why did you cry ? please stop , i don't like that "

girgiza mishi kai Safa ta yi ta na fadin " No , I can't , ba zan iya ba , matar da na dauki tsawan shekaru ina kiran ta fa momy , ita ce ta raba ni da Komai nawa , why za ta min haka ? me Daddy ya yi mata , da za ta yi mishi irin wannan abun ? duk saboda abun duniya " ba ta kai karshen maganar ta ba saboda kukan da ya fi karfin ta

da sauri Amar ya matso kussan ta , ya kai hannu ya janyo ta jikin shi ya na dan bubuga bayan ta ya na cewa " please stop crying , ba fa dan ki na da doctor a gida ba , za ki yi zaune ki na irin wannan kukan , Idan wani abu ya same ki ba zan ji dadi ba " ya fada cikin sanyin murya

Assad bai bi ta kan su ba ya juyo ya kali Marwan ya ce mishi " don't worry , gobe zan fitar da kai da ga nan "

girgiza mishi kai Marwan ya yi ya na cewa " no Sasha , ba na son ka yi anfani da matsayin ka dan fitar da ni da ga wajen nan , ina son mu bi tsarin dokar da su ka juya mana , akwai duk wasu bayanai da za ka bukata wajen Sami , wajen Puppy ma ba za a rasa ba , ka meda karar kotu , ka wanke suna na , da na Daddy , ta haka kawai na ke son fita da ga nan "

" kar ka damu na ce maka gobe za ka fita da ga wajen nan , ai kai ma ka san RUSSIA ba ta da ido a kan Nigeria , ta yadda ka fada ta hakan zan fitar da kai gobe , dan da na yi kwakwaran bincike a kan case din ka , kafin na taho nan "

wata yar karamar dariya Marwan ya yi ya na cewa " shi ya sa na ce kamar Robot ka ke , akwai kwakwolwa mutumin nawa " ya fada cikin zolaya

dan karamin tsaki Assad ya yi , ya na shirin magana Bashir ya matso kussan Marwan ya ce " Sir ya kamata ku duba abun da ke faruwa gaban ku " ya fada kassa kassa

a tare Marwan da Assad su ka juya ,
a tare su ka zaro idanu , Assad sai da ya ji zuciyar shi ta buga , ya na kallon Amar da Safa su na kissing din junan su cikin konciyar hankali idanu a lumshe da allamun sun manta da mutane a wajen

ba shiri Marwan ya juyo ya kali Assad , irin kallon nan na ina son karin bayani
gyada mishi kai Assad ya yi , kafin ya juya ya ce " Kai Amar , ba ka ga da mutane a wajen ba ? "

ba shiri Amar da Safa su ka ware idanun su a tare , sai cikin na juna ko
da sauri ya dauke hannun shi da ga saman kumatun ta , ya zame bakin shi da ga cikin nata ya mike da sauri ya fice dakin

ya na fita Safa ta dan sunkuyar da kai ta ce " I'm sorry Aryan "
wani kyawatencen murmushi Marwan ya saki ya na cewa " Sister do you love Him ? "
a hankali ta gyada mishi kai allamun eh 
" Tashi ku je to "

da sauri ta dago kai har ta bude baki za ta yi magana ya daga mata hannu ya na cewa " na yi farin cikin hakan , na san duk duniya ba za ki samu wanda zai so ki tsakani da Allah kamar Amar , zan dauki wannan Albishir a matsayin birthday gift di na , dan haka ki kontar da hankalin ki , ki tashi ki je ki na bukatar ki huta , sannan please idan kin je , kar ki nunawa wannan matar kin zo gani na , har na fadi miki abun da ya faru , ki gwada mata kamar ba abun da ya faru ta haka ne kawai za mu iya kama ta , idan ki gwada mata wani canji har ta fara zargin ki , za ta yi kokarin daukar mataki a kai har ta cutar da ke "

da sauri ta tasso da ga saman chair din ta , ta nufi Marwan ta rungume shi ta na kuka ta ce " ni ba zan iya komawa wajen wacen matar ma , a nan zan zauna tare da kai "

cikin sigar rarrashi ya ce mata " please , ki tafi kin ji , gobe Sasha zai fitar da ni da ga nan , da ga nan ba wanda zai sake raba ni da ke , rabuwar kwana guda ce za mu yi kin ji ko ? "

a hankali ta dago da ga jikin shi ta kai hannu ta fara goge hawayen ta ta na cewa " da gaske gode za ka fito ? "

gyada mata kai ya yi ya na murmushi ba tare da ya ce komai ba
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " shikenan , zan jira ka gobe , zan shirya maka party na murnar dawowa gida "

a hankali ya kai hannun shi saman kumatun ta ya ce " na gode sister , yanzu juya ku tafi na san doctor ya na cen ya na jiran ki ya Kamala aikin da ya fara " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda 

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta sunkuyo ta manna mishi kiss saman kumatu ta na cewa " I love you My Aryan "

" I love you my Puppy "

a hankali ta juya ta fara takawa har ta kai bakin kofar ta tsaya ta juyo
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi ta daga mishi hannu ta na cewa " See you tomorrow "
murmushi kawai ya yi mata bai ce komai ba , da ga haka ta sa kafa ta fice

ta na fita shi ma Assad ya mike ya na cewa " i'm going too , gobe zan dawo "

" tsaya ina son na yi maka tambaya guda " Marwan ya fada

ba tare da ya zauna ba Assad ya ce mishi " ina sauraron ka "

wani kyawatencen murmushi ya saki kafin ya ce " where is my Rahaf ? why ba ka zo da ita ba ni ma na ga nawa babyn na san dai yanzu ta girma ko ? "

wani siririn tsaki Assad ya ja kafin ya fara takawa ya nufi kofar fita
wata yar karamar dariya Marwan ya yi ya na cewa " kai dawo ba ka ba ni amsa ta ba "
ko sannu Assad bai ce mishi ba ya sa kafa ya ficewar shi 

ya na fita Marwan ya saki wata yar karamar dariya Sannan ya juya ya kali Bashir ya ce " Bash , zo mu ci cake , rabo na da cake yanzu wajen shekara 15 , gaskiya lokaci na gudu , tsaya ma shekaru na nawa , dan ni fa gaskiya na manta , kar a je na tsufa ban sani ba "

wata yar karamar dariya Bashir ya yi kafin ya ce " no , na gode sir , ku a ka kawo wa dan hakan ku ci abun ku kawai "

tsuke gera Marwan ya yi ya na cewa " Bash , ka fa sani ba na son wannan abun , dan haka ka zo mu ci wannan cake din , ya na dadi wlh " ya kai karshen ya na sakin gerar shi

dan karamin murmushi Bashir ya yi kafin ya tako a hankali ya nufi chair din da Assad ya tashi a kai , ya zauna sannan ya kai hannu ya dauki spoon guda
ya saka cikin cake din ya gunto kadan sannan ya kai saitin bakin Marwan 

hararrar shi Marwan ya yi ya na fadin " ba na son shirme "
wata yar karamar dariya Bashir ya yi kafin ya ce " please sir , ka karba , it's your birthday "

wani dan karamin murmushi Marwan ya yi kafin ya bude baki ya karbi spoon din
" Sir zan iya yi maka wata tambaya ? "
gyada mishi kai Marwan ya yi ba tare da ya ce komai ba 
Chapter 61 · 0% Book details