← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 66

Sashe 25

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta mike ta koma geffen shi ta zauna ta na kallon shi ta ce " Sami , ni fa ban iya boye boye ba , zan fada maka gaskia , i don't love you , ba dan wani abu ba da sai in ce na tsane ka baki daya , amma ba zan iya canja matsayin ka a waje na , na cewa kai sibling di na ne , ba na tunanin aure na iya shiga tsakanin mu , ko ya na shiga ni ba zan yarda ba saboda ba ni son ka , familyn ka sun kuntata min tun ina karama kuma har yanzu su na kan yi , ba zan iya shiga ahalin da ba su so na , na san watarana za su iya kashe ni , dan haka gwara ka cire wannan shirmen da ka ke kira da so da ga cikin zuciyar ka dan ni ban san shi ba , ko na fara jin shi ba na fatan na fara a kan ka " ta kai karshen ta na yar karamar dariya

Wani cool murmushi ya yi kafin ya ce " Safa you know you're extraordinary , na san abun da mu ka yi miki bai dace ba , kuma har yanzu ina bakin cikin hakan, amma ba yadda zan yi dole na saka ido na kalla , ko ba komai na gode da har yanzu ki na kallo na a matsayin dan uwan ki , na so allakar mu ta wuce haka , amma ba zan matsa miki ba a kan abun da ba ki so , ba zan so na kara miki wani bakin cikin ba , ki ji kin tsane ni baki daya , zan yi kokari wajen ganin na gyara abun da ke tsakanin ki da family na , saboda ke ma ki na ciki , amma zan so na yi miki tambaya guda in kin yarda "

A hankali ta gyada mishi kai allamun e

Mika mata hannun shi ya yi ya saki wani cool murmushi cikin sanyin murya ya ce " can i be your friend's ? "

Kallon hannun shi Safa ta yi kafin ta dago kai slowly ta kali cikin idanun shi , ba karya wannan karan shi ne na farko da ta ga sincerity din shi a ciki
Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta riko hannun shi ta na fadin " no you can not be my friend "

Dan zaro idanu ya yi ya na kallon ya ce " why ? "
Hararrar wassa ta yi mishi kafin ta janye hannun ta da ga cikin na shi ta ce " saboda yau na samo abun da na rasa da jimawa "
Cike da rudu ya ce mata " wane abu kuma ? "

Bai gama rufe bakin shi ba ta fada jikin shi ta rungume shi ta ce " my brother "

Wani kyawatencen murmushi ya saki nan take idanun shi su ka kawo ruwa
Da sauri ya datse su ya sa hannayan shi biyu ya rungume ta tsam ya na fadin " i have really missed you my sister "

Yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " me too "
Da ga haka ta raba jikin su ta na kallon shi
Matse gera ta yi ta na nuna shi ta ce " bari ganin mun shirya , wlh in ka yi min ba dai'dai ba sai na koya maka hankali " ta kai karshen ta na dunkule hannun ta ta yi kamar za ta kai mishi bugu

Yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " ni na isa , ai ina son rai na , ban shirya mutuwa ba "
Wannan karan a tare su ka yi dariya har da ita

Su na tsaka da dariyar su Momy ta shigo parlourn ta na sallama , a tare su ka kai kallon su gare ta su na amsa sallamar ta a tare

Yanayin da ta tardo su ba karamin tada mata hankali ya yi ba ba ta san lokacin da ta ce " Sami me ka ke yi a nan cikin daren nan "

Safa ce ta amsa mata da cewa " momy ba wani dare sosai ne ba fa , duka duka karfe 8 da yan mintina " ta kai karshen dai'dai momy ta zauna saman sofar da ke fuskantar ta su

Ta na zama Sami ya mike ya na fadin " ni kin tuno min ma , Aunty zan koma gida ni "

Mikewa itama Safa ta yi ta na fadin " okay , amma sai ka yi sauri kar ka hadu da yan yankar kai " ta kai karshen ta na yar karamar dariya ta juya ta fara takawa ta nufi stair ta Haye da sauri

Da kallo momy ta raka ta har sai da ta Haye sannan ta kali Sami ta ce " ba na son na sake ganin ka a kusa da ita cutar nan ta ku ta isa haka , ka kyale ta , ta yi rayuwar ta , kun raba ta da iyayen ta hakan bai ishe ku, sai kun bulo da wata hanyar daban dan cutar da ita "

Dan karamin murmushi Sami ya yi kafin ya fara takowa ya zo gaban ta ya tsaya ya na kallon cikin idanun ta ya ce " a dai bar kaza cikin gashin ta , idan an a ka fige ta wlh sai kin rasa bakin magana , kar ki manta abun da ki ka aikata , Good night "

Ya na gama fadar haka ya ci gaba da takawar shi ya fice parlourn
Ita dai momy da kallo ta raka shi har sai da ya fice sannan ta mike ta Haye stair ita ma su ka bar parlourn ba kowa a ciki

▪ ABUJA ( GIDAN SU TWINKLE )

zaune duk mutanan gidan su ke cikin parlourn , Banda Sami , wasu na kallon Tv , wasu na faman latsa wayar su , musaman Farida da ke ta faman Sakin murmushi

Su na a haka Daddy ya kalli Raïssa ya ce " Raïssa , ki shirya Doctor Amar na nan zuwa ranar monday , amma matsalar a Kaduna zai sauka , sai dai bayan kwana biyu ya zo ki gan shi "

Dan tsaki Raïssa ta yi , ta na yamutse fuska ta ce " Daddy wanene Amar kuma ? "

Daddy na shirin magana Noor ta riga shi cewa " yanzu Raïssa ba ki san Doctor Amar ba , kam amma an baro ki a baya " ta kai karshen ta na yar dariya

Hararrar ta Raïssa ta yi kafin ta kali Daddy ta ce " Daddy ka ga ni ko , wlh duk kai ka sa ta raina ni "
[01/09 à 21:18] MEERAH🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 💞💋

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

GA DUK ME BUKATAR WANNAN BOOK DA GA FARKO ZAI IYA JOING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 14 🥀 ❤

Cikin nitsuwa Daddy ya katse ta da cewa " yo ai gaskia ta fada , mutumin nan dan uwan ki ne baki daya , amma ki ce baki san shi ba "

Da sauri Noor ta taso ta koma geffen Daddy ta na fadin " Daddy kyale ta , ka san fa ba a zamanin mu ba ta ke , ai ko ba dan uwan ta ya kamata ta san Doctor Amar , babban mutun ne fa , ba a UK kadai ba , har a nan Nigeria ba wanda bai san shi ba , sai dai a ka ce ba kowa ya san face din shi ba , asali ma ko patient din shi ba duka su ke ganin face din shi ba "

Murmushi mai dan sauti Daddy ya yi kafin ya ce " to sannu malama ! Ke ta ina ki ka san shi haka , anya ba ke ma zan wa shi ba ? "

Da sauri ta girgiza mishi kai ta na fadin " a'a Daddy ni gaskia ban ni so , ni fa har yanzu baby ce , ga su Raïssa, da Farida zaune , sai a ce ni za a ba shi , a ka je wani mumuna ne shi ya sa ba ya son a na ganin face din shi ni gaskia ba ni so " ta kai karshen cikin shagwaba

Yar karamar dariya Daddy da Twinkle su ka yi
Ita dai Raïssa sai faman hura hanci ta ke yi , ta rasa wani irin mugun abu ya kamata ta yi wa wannan yarinyar , dan ta san ko kashe ta ta yi ba za ta ji saukin abun da ke cikin zuciyar ta ba

* WASHE GARI (MISALIN KARFE 10 NA SAFE)

* KUJE PRISON

Zaune Marwan ya ke saman wani banci , Bachir na zaune geffen shi ya na yi mishi hira , shi kuma Marwan ya na sauraron shi sai a kai a kai ya ke saka bakin shi

Su na a haka wani sojan ya iso wajen ya na sallama
A tare su ka amsa mishi sallamar sa , da ga nan ya sanar da Marwan cewar ya yi bako

Kallon sojan ya yi , sai da ya dauki dan lokaci kafin ya ce mishi " sai dai ya iso nan , dan gaskia ba zan iya tashi ba "
Ya na gama fadar haka ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi

Ba musu sojan nan ya juya
Ya na barin wajen Bachir ya yi murmushi mai dan sauti kafin ya mike tsaye ya koma bayan Marwan ya tsaya
Chapter 25 · 0% Book details