Sashe 66
Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 7 min read
gyada mishi kai Sami ya yi kafin ya ce " Eh , momy , Tun lokacin da ya gan ta ya kamu da son ta , sun sha samun sabani da momyna saboda Twinkle , har ya kai ya fara sa hannu ya na dukan ta , amma ba ta taba fadawa kowa abun da ke faruwa tsakanin su ba , kuma ko so guda ba ta taba nunawa Twinkle wani canjin saboda da ta san ba laifin ta ba ne , laifin Ali ne da ya kamu da soyayyar matar kannen shi , bayan Farida da Fadila sun cika shekara hudu , a lokacin ne ya fara shirye shiryen yadda zai yi ya kashe uncle Abdoul Karim dan ya mallake dukiyar shi ya kuma auri Twinkle , ashe a lokacin momy ta ji , kawai sai ta je ta fadawa Aziza ita ko ba ta san kansu guda da Ali , kawai Aziza ta zagayo ta fadawa Ali abun da momy ta fada mata , da kuma recording din da ke hannun momy na maganar da ya yi da abokan shi a kan shirin su wanda ta shirya gwadawa uncle Abdoul Karim , Aryan gaban ido na Ali ya sa hannu ya kashe momy da ciki a jikin ta , ko tausayin abun da ke cikin ta bai ji ba ya sa hannu da kan shi ya kashe ta , kuma babu wanda ya san wannan labarin da ga ni sai Allah sai shi Ali , sai kuma kai yanzu , ban so fada maka wannan labarin ba , amma dole yanzu ka sani , ina son ya biya abun da ya yi wa momyna , ka yi hakuri na so na yi anfani da kai ne dan daukar fansar momyna a kan Ali , saboda ni ba zan iya yin komai a kan shi ba , ba ni da wata huja da zan nuna a kama shi da kisan momy , shi ya sa na ke son ka fito , idan na gan shi a prison saboda kisan uncle Abdoul Karim zan iya rage radadin momyna da ya kashe min , har yanzu ina bakin cikin wannan ranar , kuma har yanzu ta kassa fita da ga cikin kwakwolwa ta " ya na gama fadar haka wasu hawaye ma su zafi su ka zubo mishi
da sauri ya kauda kai gefe ya na sa hannu ya goge hawayen shi
ya na a haka kawai ya ji hannun Marwan saman face din shi ya na goge mishi hawaye
a hankali Sami ya sauke ajiyar zuciya ba tare da ya juyo ba ya ce " ka yi hakuri , kawai dai na so yin anfani da wannan damar ce dan ganin an bawa Ali hukuncin abubuwan da aikata , hakan kuma ya na nufin yin anfani da kai , ka yi hakuri , i know , i was'nt be honest with you "
cikin nitsuwa Marwan ya katse shi da cewa " Sami , ni ka daina ba ni hakuri , na yi maka alkawari sai Ali ya biya a kan mutuwar Daddy , Amar da kuma ta momy , za mu ba shi hukuncin da ya dace da mutane irin su , marasa tsoron Allah , ma su son zuciya "
a hankali Sami ya juyo ya kali Marwan ya ce mishi " that's why na ke alfaharin kasancewa ta dan uwan ka "
wani murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya ce " ashe dama haka ka iya kuka ? ai ko Safa ba za ta yi irin wannan kukan ba , dubi don Allah sai ka ce wani karamin yaro "
wata yar karamar dariya Sami ya yi kafin ya ce " za ka fara maganar tsagar ka ko ? "
dariya shi ma Marwan ya yi kafin ya ce " ban rike ka ba tashi ka tafi "
mikewa Sami ya yi ya na fadin " shikenan zan tafi , dama dare ya yi ya kamata na koma gida , ka kula min da kan ka "
a hankali Marwan ya mike , su ka rungume juna kafin su yi sallama Sami ya fita
Marwan kuma ya koma cikin cell din shi zuciyar shi cike da farin cikin ba abun da ya samu Safa , wani bangaran kuma ya na jimamin mutuwar Amar
▪TWINKLE
a hankali ta ke sauko Stair , da ga gani kassan akwai abun da ke damun ta dan ga shi nan konce a saman face din ta
karasowa ta yi cikin parlourn , nan ta tardo Noor , Raïssa , Farida da Fadila su na zaune kowace rike da wayar ta ta na latsawa
sofar da Noor ke zaune ta nufa ta zauna geffen ta , ta na fadin " Noor , na ga wayar ki don Allah "
" okay momy " Ta fada cikin nitsuwa kafin ta mika mata wayar
a hankali Twinkle ta kai hannu ta karba ta fara latsawa
ta dan dauki lokaci a haka kafin ta kai wayar a kunne da allamun wani ta kira , amma sai a ka ce mata wanda ta kira wayar shi na kashe
sauko wayar ta yi ta sake saka numbar ta danna kira nan ma a ka ce mata wayar na kashe
sai da ta yi wajen kira har hudu amma wayar ta na a kashe
cikin sanyin murya Noor ta ce mata " momy wai wa ki ke ta kira haka ? ki na ji wayar a kashe ta ke "
" Noor , Safa ce na ke son kira , tun safe na ke jin gaba na na faduwa , shi ya sa na ke kiran ta na ji in ta na lafiya "
ba ta gama rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar Raïssa ta na cewa " Allah ya sa ma ta mutu "
a tare Farida da Fadila su ka bushe da dariya kafin Farida ta ce " ya wuce ta na tare da Amar , su na cen su na shan duniyar su "
cikin bacin rai Noor ta ce mata " ba dan ke ki na tafiya shan duniyar ki ba ya ke nufin kowa ma hakan ya ke , yan bakin ciki kawai to ba abun da ya same ta anniyar ku ta bi ku "
cikin bacin rai Farida ta mike ta nufi Noor ta daga hannu sama za ta mare ta
Cikin zafin nama Twinkle ta riko hannun ta , sannan ta tura ta baya har sai da ta nemi faduwa
a hankali ta mike ta na kallon ta ta ce " idan hannun ki ya taba ta , gidan sai ya yi mana kadan , mara kunya kawai , za ku tashi ku ba ni waje ko sai na saba muku ! "
a hankali Fadila ta mike ta karaso gaban ta ta tsaya ta na fadin " kin ga malama ba ki da ikon ba mu umarni a gidan nan yawwa , saboda ba gidan tsohon mij........"
ba ta kai karshen maganar ta ba kawai ta ji saukar mari Tas a kumatun ta
" idan ki ka bari na maimaita abun da na fada sai miki dukan mutuwa a cikin gidan nan " Twinkle ta fada cikin bada umarni , yau dai sun kai ta makura
da sauri Raïssa ta mike ta na fadin " kan uba , ke wa ya ba ki izinin marin ta ? lalle yau kin debo ruwan dafa kan ki cikin gidan nan , ke har kin isa , ko wanda ya haife mu ba kai ya sa hannu ya mare ta bare ke shara kawai "
wani dogon nunfashi Twinkle ta ja , ta na shirin magana Sami ya turo kofar parlourn ya shigo ya sallama
bin su da kallo ya fara yi ya na fadin " lafiya , ku ka yi tsatsaye ? " ya kai karshen ya na zama saman sofa one seater
kamar za ta yi kuka Fadila ta ce mishi " mari na wannan tsohuwar matar ta yi " ta fada ta na nuna Twinkle da ta koma ta zauna ta na ci gaba da latsa wayar Noor kamar ba a yi komai ba
" and so what dan ta mare ki ? ba momyn ki ba ce "
da sauri Farida ta katse shi da cewa " no wannan ba momyn mu ba ce , kawai matar Daddy ce , kuma ba ta da izinin sa hannu ta dake ta , kuma wlh sai na fadawa Daddy , Fadila wuce mu tafi " ta kai karshen ta na kama hannun Fadila su ka juya a tare su ka bar wajen