← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 66

Sashe 17

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta na hawa Daddy ya kali Raïssa ya ce " na lura ku na son takurawa yarinyar nan cikin gidan nan , to bari ki ji , na gaji da ganin ku cikin gidan nan , na ba ku nan da one month ko wace ta fito da mijin aure ko kuma na aura muku duk wanda na samu "

" What ? Daddy aure fa , ni gaskia ban shirya ma aure ba , kuma Daddy ni fa ban mare ta ba karya ce kawai ta ke yi min " Raïssa ta fada da dan karfi

Tsawa Daddy ya daka mata da cewa " Shut up , ba shawara na ke ba ki ba umarni ne , duk wanda ya sake yi wa yarinyar nan ko da kallon banza wlh ba mai raba ni da shi cikin gidan nan " ya na gama fadar haka ya nufi stair ya Haye shi ma

Da kallo Raïssa ta raka shi har sai da ya Haye stair sannan ta koma saman sofa ta zauna ta na gunguni ita kadai

Ta na a haka Fadila da Farida su ka shigo parlourn su na sallama
Su na sanye da Skert pink colour da kadan ya wuce guyiwa , da shirt fara mai dogayen hannu da dan karamin hijab zuwa kirji shima fari , su na rike da school bag

A tare su ka karaso cikin parlourn su ka ajiye bag din saman table kafin su zauna saman sofa two seaters

Kallon Raïssa su ka yi da kyau , har su na hada baki wajen tambayar ta lafya dan da ga gani yanayin face din ta , ta na cikin bacin rai

" wai ni wacen sakarar yarinya za ta yi wa sharri wajen Daddy, shi kuma ya yarda da maganar ta , har da cewa ya gaji da ganin mu cikin gidan nan " ta fada ta huci

Dariya Farida da Fadila su ka yi a tare kafin Fadila ta ce " ni dama sai da na fada miki , mu daina ragawa yarinyar nan , Daddy fa ya fi son ta fiye da mu "

Tsaki Raïssa ta ja kafin ta hararri Fadila ta ce " gwara tun wuri ku fido da mazajen aure dan Daddy ya ce one month ya bawa kowa in ba haka ba ya aura muku duk wanda ya ke so "

" ya aura mana duk wanda ya ke so har da ke malama , ke Fifi tashi mu tafiyar mu " Fadila ta fada ta na mike ta nufi stair ita da Farida

Da kallo Raïssa ta raka su har sai da su ka Haye sannan ita ma Raïssa ta mike ta Haye stair din ta na faman bata rai

▪ Misalin karfe 4 na yamma

▪Safa 💋

Zaune ta ke cikin parlour ta na kallon chanel din MTV hits ta na kallon wakoki
Ta na sanye cikin mini skert white colour , da yar karamar t-shirt zuwa cibi pink colour ta saki wannan golden hair din na ta

Ta na a haka Snoopy ya figo Parlourn ya na dan Haushi ya karaso wajen sofar da ta ke zaune ya konta ya na shafa cinyar ta

Murmushi ta yi kafin ta ce " lafya wa ya koro ka " ta fada ta san halin shi in sun yi bako

Dan karamin haushi ya yi ya na ida kontawa a wajen dai'dai lokacin da Sami ya shigo parlourn ya na sallama

Ta na ganin shi yanayin face din ta ya sauya , kamar ba ta ji dadin ganin shi ba
Cen kassan makoshi ta amsa mishi sallamar shi kafin ta meda kallon ta kan Tv

Shi kuma ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofa da ke geffen ta ta ya na kallon ta ya ce " Me ki ke yi a gida , ba ki je school ba yau ko me ? "

Ba tare da ta kale shi ba ta ce " ba mu da lectures yau "
Kallon Snoopy ta yi kafin ta ce " Snoopy je ka kira min Balki "
Dan karamin haushi ya yi wai shi ba ya zuwa

Matse fuska Safa ta yi kafin ta ce " Snoopy ba na son wannan abun da ka ke yi , maza tashi ka je ko kuma na yi maka fushi "

Ba dan ya so ya mike ya nufi dining room ya shiga kitchen
Ya na shiga Sami ya ce mata " wai ba za ki daina magana da wannan karan ba , ke fa ba yarinya ba "

Ta na shirin magana wayar ta da ke saman table ta yi ringing
A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta na kallon screen din
Ta ga number din ta Nigeria ce , ita dai ta san bayan momy , Haoua da Djamila sai Musadeeq da Mutalab ba wanda ke da number din ta

Cike da shakku ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na sallama
A daya bangaran kuma amsa mata sallamar ta Nabil ya yi kafin ya daura da cewa " Abokiyar hira, ya ki ke , shikenan tun da ki ka tafi ko waiwayo mu ba za a yi ba "

Dago kai ta yi a hankali dai'dai lokacin da Balki da Snoopy ke fitowa da ga cikin dining room su ka karaso cikin parlourn
Snoopy ya Haye saman sofa ya konta geffen Safa ya na kallon ta

Balki kuma ta na ganin Sami ta koma dining room dan ta gane kiran me a ka yi mata
Safa kuma daura hannun ta ta yi saman kan Snoopy ta na shafawa a hankali kafin ta ce " Sorry ban gane da wa na ke magana ba "

Yar karamar dariya Nabil ya yi kafin ya ce " Dama na san haka za ki ce , wajen boss na karbi number din ki , Nabil ne abokin aikin ki "

Daga kai sama ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta medo ta saki wani cool murmushi ta ce " Ah okay na gane ya ka ke ya aiki kuma "

" Lafya klau wlh , ya yi ke kwana biyu "

Murmushi ta yi ta na kallon Snoopy ta ce " alhamdoulilah thanks God "

" okay ya yi kyau , na zo miki da wani albishir mai dadi "

Dan washe baki ta yi kafin ta ce " Toooo ! Minene wannan albishir ? "

Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Mariam mai gabatar da shirin Jarida , to sun koma Katsina da zama , ba za ta ci gaba da gabatar da shirin ba , boss ya ce duk wanda ya ga zai iya gabatar da shirin a madadin ta , sai ya yi mishi magana , shi ya sa na kira ki dan na fada miki ko ki na son shiga wajen ta "

" hmmm nagode sosai , na yi shawara na gani , in mun gamu Friday zan fada maka "

" okay no wonder , zan bar ki na san ki na aiki sai an jima "

Murmushi ta yi kafin ta ce " okay bye " ta na gama fadar hakan kiran ya katse
Sauko da wayar ta yi ta ajiye saman table kafin ta kali Snoopy ta daura lips din ta saman forehead din shi ta sumbata

Shi dai Sami da kallo ya ke bin ta , ya rasa abun da zai ce mata

Sai da ta gama wassan ta da Snoopy sannan ta juyo ta kali Sami lokacin har Balki ta kawo mishi Drinks da snacks amma bai taba su ba

Matse gera ta yi ta na fadin " why are you look at me like this ? "

Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi ya na girgiza mata kai kafin ya ce " nothing , kawai dai ina kallon yadda ki ke wasu abubuwa kamar karamar yarinya "

Daga mishi gera guda ta yi kafin ta ce " me kuma na yi irin na yara ? "

GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE⚘❤

GA ACCOUNT ADRESS 👇👇👇👇

8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

KO KUMA TA CREADIT DA TA WADANAN NUMBER 👇👇👇

Zain (Airtel)
08081129487.

Mtn
07067953066.

NAIRA 200 NE ONLY

SANNAN KU TURA SHAIDAR TURA KUDIN A WANNAN NUMBER ( +22795577612 )

🩷✨✌️
[25/08 à 15:25] MEERAH🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🔥💦

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

P A G E 10 🥀 ❤

Dan karamin murmushi Sami ya yi kafin ya ce " sister wai me ya sa har yanzu ba ki sakin jiki da ni ? "

Daga kafadun ta ta yi allamun ban sani ba , kafin ta juya ta kali Snoopy ta ce " baby tashi ka je "

Ba musu ya diro da ga saman sofar ya girgije sannan ya fice parlourn da gudu
Ya na barin wajen ita ma ta mike ta na shirin barin wajen

Da sauri Sami ya riko hannun ta ya janyo ta ta fado a jikin shi
" ki ba ni amsa mana kafin ki tafi , why ki ka tsane ni a yanzu , lokacin da ki ke baby saman cinya ta ki ke wassa ko kin manta , why ki ka daina yanzu " ya fada ya na kallon face din ta

" i'm not a baby , so let me , kai da kan ka ka fada ni ba yarinya ba ce " ta fada ta na kokarin kwatar hannun ta

Sakin ta ya yi , dama jira ta ke , ta tashi da sauri ta yi baya ta na hararrar shi ta matse gera ta ce " tashi ka fice mana gida "

Komawa ya yi ya jingina a bayan sofar ya daura kafa daya saman daya cike da isa ya ce " in kin gaji da gani na sai ki bar gidan ga kofa nan "

Tsaki Safa ta yi kafin ta juya ta nufi hanyar stair
Da sauri ya ce mata " idan kin je ki sauya wadanan kayan kin ji ko "
Chapter 17 · 0% Book details