← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 66

Sashe 27

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya ida biye mishi sannan ya ce mishi ya je waje ya jira shi
Ba musu Snoopy ya sauko da ga jikin shi ya fice parlourn da gudu
Sai da ya fita sannan Amar ya kali Safa ya ce " amma kin jima ki na da karen nan ko , na ga ya na jin magana ba kamar Rex ba "
" wanene kuma Rex ? " ta tambaye shi ta na daga mishi gera guda
" Abokin big bro di na , shi ma, na shi karen ya na kama da wannan tak , sai dai na shi ya samu horon soja , ko za mu je ki gan shi " ya fada ya na dan murmushi
Girgiza mishi kai kawai ta yi dan ta rasa abun da za ta ce da shi

Sarai ya gane abun da ta ke tunani , sai ya ce mata " i'm sorry, na zo muku gida ba tare da sanin ka , just na kassa hakura ne , ina son na gan ki , kuma jiya kafin mu tafo sai da na duba localization din ki na ga gidan da ki ke ciki ya na fuskantar wanda za mu sauka a ciki , shi ya sa na taho nan kai tsaye ko gidan ban shiga ba "

Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " no ba haka ba ne kawai zuciya ta ta kassa yarda ne da abun da na ke gani "

" why ? Ba aljani ba ne ni , ki yarda da ni ba da niyar cuta na zo gare ki ba " ya fada mata cikin sanyi

" no ba haka ba ne , ni ma na kassa tantance abun da zuciya ta ke rada min "

Dan karamin murmushi ya yi kafin ya mike tsaye ya na kallon ta ya ce " ba komai , ni zan koma gida , please idan kin samu dama zan so ki dan leko mu , ni da brother di na ne mu ke tare "

Mikewa tsaye ita ma ta yi kafin ta ce mishi " okay , Allah ya kai mu "

Juya wa ya yi ya fara takawa ya fice parlourn ya bar ta nan tsaye
Ya na fita ta saki wani kyawatencen murmushi cikin zuciyar ta kuma ta na fadin " ko ba komai ya hadu gaskia , amma muryar shi da na ji a waya da kuma ta yanzu ta so ta dan banbanta "
Da wannan tunanin ta bar parlourn ita ma ta Haye stair da sauri
Ta na barin wajen ko Balki ta fito da ga kitchen rike da tray
Har ta karaso cikin parlourn kawai sai ta ga ba kowa
Dan karamin tsaki ta ja kafin ta juya ta koma kitchen din ta ci gaba da aikin ta

Bangaran Safa kuma ta na hawa ta wuce kai tsaye bedroom din ta ta shiga wanka
Jim kadan ta fito daure da towel a kirjin ta , ta wuce dressing room
After some minutes ta fito sanye da wata gown navy blue mara nauyi ta na sanye da wani hijab shi ma navy blue
Kai tsaye wajen daddumar ta ta nufa ta fara gabatar da sallar la'asar dan lokacin ta ya yi

Bayan ta Kamala sallar ta , ta cire hijabin ta , da gown din ta ajiye saman sofa ashe ta na sanye da wasu kananan kayan da ga kassa , Mini skert ne zuwa guyiwa da wata yar t-shirt duka pink colour , ta saki wannan golden hair din na , yau har wani curly ya yi , wayar ta ta dauka saman bedside drawer , da wani dan karamin book kamar diary haka sannan ta fito dakin

Kai tsaye parlourn kassa ta sauko , ta na tafe ta na latsa wayar ta , har ta karaso wajen sofa sannan ta zauna ta ajiye diary din geffen ta , ta ci gaba da latsa wayar ta

Kamar wadda ta tuno wani abu ta mike a dubu dari ta nufi stair da gudu
Har ta daga kafa za ta taka stair na farko ta tsaya , dan karamin tsaki ta ja kafin ta juya ta nufi kofar fita parlourn
Bayan ta fito parlourn cikin harabar gidan , kai tsaye wajen gate ta nufa
Da sauri gateman ya taso ya na tambayar in ta na bukatar wani abu
Ba ta bi ta kan shi ba sa kafa ta fice gidan , ta na fita ko Snoopy ya taso da gudu da ga inda ya ke zaune ya bi bayan ta a hankali ba tare da ta sani ba
Gidan da ke fuskantar na su ta nufa da farko har ta fara da na sanin tahowar ta saboda jibga jibgan sojojin da ke tsatsaye bakin gate din gidan
Sai dai wani abu da ba ta sani ba , Amar ya fada musu cewa yanzu sun yi bakuwa in ta zo su bar ta ta wuce
Haka ko a ka yi , tun kafin Safa ta yi musu magana mai kula da gate din ya bude mata kofar da kan shi
Sai da ta kare mishi kallo da kyau sannan ta sa kafa a hankali ta shiga gidan
Nan ta ga abun da ya fi karfin ta , duk gidan cike ya ke da manya manyan sojoji kowane rike da gun sai zagaye harabar gidan su ke yi , ga wasu manya manyan motoci cike da parking space , motoci ma su nunfashi kallo guda za ka yi musu ka san ba na kananan kudi ba ne , har sai da ta fara tambayar kan ta anya Amar doctor ne kamar yadda ta fada

Wajen wani dan balconyn da zai sada ka da cikin gidan ta nufa
A hankali ta kai hannun ta ta yi knocking kofar , shiru har ta dauki wajen ten minutes
Sake kai hannu ta yi ta yi knocking a karo na biyu nan ba shiru ba a bude mata ba
Dan karamin tsaki ta ja kafin sa hannu ta tura kofar a hankali sannan ta shiga ta na sallama
Gaskia parlourn ya hadu ga shi kuma da girma , komai na cikin Milk colour ne abun ba karamar kayatarwa ya yi ba
Cen ta hango Amar Zaune saman wata doguwar sofa bayan ta dakwai wani stair mai kyau zagaye da glass

Ya na sanye da trouser black colour da wata T-shirt navy blue , ya daure gashin kan shi baya ya saka wasu glass bakake a ido , ya na faman latsa laptop din da ke gaban shi saman table , ga wani kare sak Snoopy konce geffen kafar shi

Safa na ganin karen ta yi sauri ta karaso cikin parlourn ta na fadin " Snoopy me kuma ka ke yi nan ? "
Ba ta gama rufe bakin ta ba Snoopy da ke tsaye bayan ta ya yi mata dan haushi

A razane ta juya ta na kallon shi , a rude ta juya ta kali karen da ke konce geffen kafar wanda ta ke tunanin Amar ne
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " please Amar ina son mu yi wata magana "
Ko dago kai bai yi ba bare ya ba ta amsa , ba kuma bai ji ta ba , sarai ya ji ta tun shigowar ta parlourn
[03/09 à 21:46] MEERAH🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

DOMIN SAMUN WANNAN LITTAFIN DA GA FARKO ZA KU IYA JOING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 15 🥀 ❤

A hankali ta yi taku biyu ta karaso kusa da shi kadan ta ce " please Doctor ! "
Da sauri Karen nan ya dago kan shi ya daka mata wani wawan haushi , ba dan da ya ke ta saba da kare da yanzu ta saki fistari

Ya na shirin tashi ya biyo ta , saurayin nan ya ce " Rex , koma ka konta " ya fada da turanci kamar an yi mishi dole

Cak Safa ta tsaya ta zuba mishi ido babu ko kiftawa kamar wadda ta ga wani abun tsoro
Ta na a haka ta ji an fara tako stair a hankali
Daka kan ta ta yi ta kali stair din , Dum ta ji zuciyar ta ta buga har sai da ta zaro idanu ta na kallon Amar da ke sauko stair din a hankali ya na latsa wayar shi kai a sunkuye
Ya na sanye da wando three cuter black colour da t-shirt white colour

Sai da ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofa geffen Assad ba tare da ya dago kan shi ba , ya jingina a jikin headboard din sofar ya daura kafa daya bisa daya sannan ya ce " da ga zuwan ka sai aiki, ko hutawa ba ka yi , kar ka manta Hutu fa mu ka zo nan "
Shi sam bai san da Safa da ke tsaye gaban su ta zuba musu ido

Bangaran Safa kuma tun lokacin da Amar ya karaso cikin parlourn ta yi sumar tsaye , ita sai yanzu ta lura wanda ta fara yi wa magana ya dan fi Amar haske , ya fi shi murdaden jiki , ya kuma tara gashi ba kamar Amar ba , bayan haka su na kama tak kamar an tsaga kara

A hankali Assad ya mike tsaye ya na rike da laptop din shi cikin wata sexy voice din shi ya ce " Rex let's go " ya fada ya na takawa , da sauri Rex ya mike ya bi bayan mai gidan shi , a tare su ka Haye stair su ka bar Safa da Amar cikin parlourn

Sai da su ka bar wajen sannan Amar ya ajiye wayar shi saman cinyar shi ya dako kai a hankali
Bai sauke idanun shi ba ko ina sai saman Safa da ta yi sumar tsaye ta na kallon shi
Chapter 27 · 0% Book details