← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 66

Sashe 36

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

" oh Sorry ba na jin haoussa " ya fada da turanci

Dan zaro idanu Fadila ta yi ta na juyawa ta kali Raïssa ta juya ta kali Amar

Ta na shirin magana ta ga Raïssa ta karaso gaban Amar ta na fadin " Sannu ka da zuwa bismillah zauna mana "

Daga mata hannu ya yi sannan ya juya ya kali Safa ya ce " I'm sorry baby ina ga komawa za mu yi , uncle ne ya kire ni , ya ce ba ya gida sai dai gobe mu dawo "

A tare Farida da Fadila su ka kali juna su na zaro idanu su ka ce " baby ? " a tare

Ba su gama rufe bakin su ba , Safa ta juya da sauri za ta bar wajen
Ta yi taku biyu ta jiyo Muryar TWINKLE ta na fadin " Safa ? "

Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba ta na jin zuciyar ta na duka uku uku

Shi dai Amar tsaye ya yi ya na kallon matar nan , sai ya ga kamar Safa ce ya ke kallo kawai sai ya rasa yin wani kwakwaran motsi kawai ya tsaya ya na kallon su

Sai da TWINKLE ta karaso wajen su , sannan Safa ta juyo slowly
Da sauri TWINKLE ta rungume Safa ta na fadin " My Safa , na ji dadin ganin , i have really missed you "

Rungume ta ita ma Safa ta yi cikin sanyin murya ta ce " Good morning Mom ! "

Dan zaro idanu Amar ya yi ya na maimaita kalmar cikin zuciyar shi

Raba jikin su Safa da twinkle su ka yi , da sauri Safa ta juya ta na fadin " Good bye Mom "
Cak ta ji an riko hannun ta , da sauri Safa ta juyo ta ga Amar ne
Cikin raunin murya ta ce " Doctor please let's go "
Kallon Doctor Twinkle ta yi ta na shirin magana Noor ta riga ta cewa " My Safa tafiya za ki yi " ta kai karshen kamar za ta yi kuka

Slowly Safa ta juyo ta kali Noor ta yi mata murmushin karfin hali ta ce " i'm sorry My Noor ina dawowa ran Monday yanzu akwai inda zan je " ta kai karshen ta na kwace hannun ta da karfi da ga na Amar ta fice Parlourn da sauri

Da sauri Amar ya ce " Baby where are you going ? " ina har ta ficewar ta ta janyo door din da karfi

Dawo da kallon shi ya yi kan twinkle ya yi sannan ya ce " I'm sorry Mom....... "
Cikin nitsuwa TWINKLE ta katse shi da cewa " don't worry my son let's go home now " ta kai karshen ta na juyawa ta Haye stair

Ta na barin wajen Noor ta karaso gaban Amar ta na washe baki ta ce " hi , my name is Noor , ba zan tseda ku ba , kawai dan in ce maka ina matukar son aikin da ka ke yi , ni ma in na girma karatun doctor zan yi "

Maganar ba karamar dariya ta ba shi ba , amma sai ya danne ya saki wani cool murmushi ya mika ma ta hannu ya ce " Nice to meet you Miss Noor , an taba fada miki ki na da kyau kamar hasken wata "

Da sauri Noor ta sa hannu ta rufe fuskar ta ta na murmushi wai ita ta ji kunya

Murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " Don't be Shy like me , i'm coming back very soon , yanzu dai bari na je kar Madam ta bace min , bye " ya kai hannu ya na juyawa ya fice parlourn

Ya na fita Noor ta saki wata yar kara har da tsale kafin ta juya da gudu ta Haye stair

Ta na barin wajen Fadila ta ce " Toooo , wata sabua , Fifi kin ji abun da na ji Madam ? "

Yar karamar dariya Farida ta yi ta na kallon Raïssa ta ce " to je Raïssa kin ga samu kin ga rashi , dan da ga ganin allamu Safa ta malake zuciyar Doctor Amar , kin ji wai Madam " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya

Dan tsaki Raïssa ta yi kafin ta harare ta sama da kassa sannan ta nufi stair da gudu ta Haye , da kallo Fadila da Farida su ka raka ta har sai da ta Haye sannan su ka sake bushewa da dariya har da tapi

Bangaran Amar kuma bayan ya fito harabar gidan ya ga babu Safa ya yi tunanin ta na cikin motar amma sai ta ga ba ta nan
Da sauri ya shiga motar ya tada motar ya bar gidan da mugun gudu
Shi ya rasa ta ina ma zai fara duba ta , ya duba duk layin har karshen shi babu ita babu mai kama da ita

Da sauri ya ciro wayar shi ya fara duba localization din ta
Da sauri ya tada motar ya bar wajen
Sai da ya yi tafiya wajen ten minutes kafin ya iso cikin wani tsohon kongo
Da sauri ya yi parking din motar shi , ya sauko ko motar bai kashe ba ya shiga wajen da sauri
Cen ya hango ta zauna saman wasu brick na siminti ta na zaune ita kadai ta na dan rera waka ta na murmushi kamar mahaukaciya

Bai ce mata komai ba kawai ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak kamar baby ya juya ya bar wajen da ita
Bai sauke ta ko ina ba sai cikin motar shi , sannan ya shiga shi ma ya bar wajen da gudu

Bai ce mata komai ba har sai da su ka karaso cikin garin Kaduna , ya iso bakin kofar gidan su ya yi parking din motar

Ba tare da ya kale ta ba ya ce " Ba zan yi miki dole ki fada min abun da ke damun ki , amma zan so ki san duk ranar da ki ka ji ki na bukatar abokin da zai taya ki kuka ki kira ni kawai "

Bai kai ga karasa maganar shi ba ya ji ta fado jikin shi ta rungume shi ta na sakin kuka mai cin rai
Bai yi kokarin hana ta ba , sai ma rungume ta da ya yi shi ba ya na dan bubuga bayan ta a hankali ya na fadin " ni fa ba irin wannan kukan ba na ke so , amma please ki daina ba na son ganin ki cikin wannan halin wlh ki na karaya min zuciya "

A hankali ta dago da ga jikin shi ta na rage sautin kukan ta , ta ce " me ya sa ka damu da ni haka wai , duk rayuwa ta bayan Family na babu wanda ya taba ce min ina karaya mishi zuciya da kuka na sai kai , asali ma bayan su kai kadai ne ka taba ganin kuka na "

Dan karamin murmushi ya yi ya na kai hannu ya ciro handkerchief ya fara goge mata hawayen ta ya na fadin " to ni ma ai yanzu familyn ki ne , dan haka duk lokacin da ki ka ji wani abu na damun ki , kawai ki kira ni mu tafi shan ice cream "

Yar karamar dariya ta yi ta na shirin magana ta ji saukar lips din shi saman forehead din ta ya yi mata kiss
" shikenan yanzu tashi ki je , ki wanke face din ki , ki yi sallat sai ki tardo ni gida ina jiran ki kin ji ? "

Gyada mishi kai kawai ta yi dan ya kashe mata bakin magana, da ga haka ta sauko da ga cikin motar ta shiga cikin gidan su
Shi ma saukowa ya yi da ga cikin motar ya nufi cikin gidan na su , kafin ya shiga sai da ya bawa daya da ga cikin Sojojin da ke tsaye bakin gate a kan ya sanyo motar cikin gida

Bayan ya shiga gidan kai tsaye part din su ya wuce
Bakin shi dauke da sallama ya shigo parlourn part din su
Nan ya isko Assad zaune saman sofa ya na aiki cikin laptop din shi
Geffen shi Amar ya karaso ya zauna ya na fadin " wai yaushe za ka fita da ga cikin gidan nan , kullum ka na ciki kamar amarya "

Ba tare da ya kale shi ba ya ce " da ga ina ka ke ? "
Dan kauda kan shi gefe Amar ya yi ya na dan karamin tsaki kafin ya ce " wai yaushe za ka daina samin ido ? "

Ajiye laptop din shi Assad ya yi ya juyo ya kali Amar ya ce " fada min gaskia , me ke tsakanin ka da yarinyar nan , na ga ku na yawwan fita kai da ita "

Dan karamin murmushi Amar ya yi kafin ya ce " Love ! " a takaice
Shiru Assad ya yi ya juya ya dauki laptop din shi ya ci gaba da aikin shi

Mike wa tsaye Amar ya yi ya nufi bedroom din su
Har zai shiga ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " Sasha ko na fada maka ba za ka iya gane abun da ke cikin zuciya ta ba , saboda ba ka san wannan abun ba "

Cikin nitsuwa Assad ya katse shi da cewa " na sani , kar ka manta zuciyoyin mu a tare su ke bugu , duk wani yanayi da ka ke ciki ina jin shi a jiki na , na san ka na son yarinyar nan , ba kuma zan tseda ka ba wajen ganin ka samu soyayyar ta ba , I just don't want her to end up fucking your heart , ba zan iya jure haka ba "

Slowly Amar ya juyo ya kali Assad , har yanzu dai ya na faman latsa laptop din shi

Dan karamin murmushi Amar ya yi kafin ya juya ya shiga bedroom din su
Chapter 36 · 0% Book details