← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 66

Sashe 44

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

wannan karan sai da ya dan dauki lokaci kafin ya bude bakin shi a hankali ya ce " I know "

" and ? har yanzu ba ka samo inda ya ke ba , ina kewar dramar nan ta shi sosai " Amar ya fada ya na dan karamin murmushi

ajiye laptop din shi saman table Assad ya yi , sannan ya jingina bayan shi a jikin forehead din sofar ya juyo slowly ya kali Amar ya ce " har yanzu ina bincike , amma duk prison Nigeria ban samu me sunan Aryan ba "

gyara zaman shi Amar ya yi ya juyo su na fuskantar juna ya ce " why ba za mu tambaye ta ba , tun da har mu na da tabbacin dan uwan ta ne , na san ba za ta rasa sanin inda ya ke , kuma na san ita ma ta na son a fitar da shi da ga wajen nan , ko dan haka za ta ba mu hadin kai "

shiru Assad ya yi kamar mai tunanin wani abu
cen kuma sai ya ce ma Amar " no ba za ta fada ba , Tabass ta san inda ya ke , amma ba za ta iya fada mana ba , kuma ita da kan ta ba ta zuwa inda ya ke "

" Assad , dole akwai wanda ya ke hana ta zuwa wajen shi "
" may be matar da ta ke tare da ita "
" why , ka ke tunanin haka ? "

dan jinkirtawa Assad ya yi kafin ya ce " i don't know , kawai matar nan ba ta konta min a rai ba , she is so suspect , abun da na sani His excellency ya na da wani babban yayan bayan ita , na san ba zai rasa family ba , to ya na ina , why ba ya zowa duba ta , tun da har yarinyar Kannen shi ce , dole akwai wata a kassa , akwai wani abun da matar nan ke boyewa "

shiru Amar ya yi kamar mai tunanin wani abu ya daga kan shi sama
da sauri ya sauko shi ya matso kusan Assad ya ce " Assad , Shekaran jiya , ba na fada maka momy ta kira ni ta ce na je gaishe da mijin sister din ta da ke a Abuja "

a hankali Assad ya gyada mishi kai allamun Eh
" yawwa , gidan da mu ka je , na ga wata matar kamanin ta sak da Miss Safa , har da wata yar yarinyar a shekaru za ta kai 13 haka ita ma ta na kama sak da Miss Safa "

daga mishi gera guda Assad ya na fadin " And ? "
" And she call her Momy "
" Momy ? ka na nufin mahaifiyar ta ce "

" ga Dukan allamu , Ta na kiran ta da momy ga shi kuma su na kama tak tak kamar an tsaga kara , har kuka sai da Miss Safa ta yi da ta baro matar nan , sai da na tambaye ta in ta san su amma ta ce ba za ta iya fadamin ba "

" Amar in har wannan matar momyn ta ce , why ba za ta zauna tare da ita ba , sai ta zauna tare da kanwar mahaifin ta ? "

" Assad , ni ma ban sani ba , labarin yarinyar nan a boye ya ke , kuma an boye mata wasu abubuwa dayawa a ciki , Ita da kan ta cikin duhu ta ke "

gyada mishi kai Assad ya yi a hankali ba tare da ya ce mishi komai ba
a hankali Amar ya mike ya fara takawa zai fice dakin
a hankali Assad ya kira sunan shi , cak ya tsaya ya juyo ya na daga mishi gera guda

" Lokacin da na ke binciken prison din Nigeria , akwai wani prisoner me Sunan Marwan , duk shekara sai sun sauya mishi prison , yanzu haka ya na a Abuja , A binciken da na yi yanzu haka ya kusa cika shekara 15 a prison , kamar dai Aryan "

" ka na nufin Marwan zai iya kasance wa Aryan "

" may be , Abun da ya kara daukar hankali na a kan shi , Gobe ne birthday din shi shi ma "

DON'T FORGET TO SHARE PLEASE 🙏🙏🙏
[16/09 à 20:04] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

🥀💔( A heart touching love story & destiny ) 🥀💔

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🕊💦

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 : Free book

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ : paid book

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT

WATTPAD : @bennybite

a duk me bukatar yin magana da ni kai tsaye zai iya samu na ta wannan number +22798999753 , WhatsApp ONLY

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

( 🤣🤣🤣✌✌ yau dai Amar zai fadawa Safa abun da ke cikin zuciyar shi a gaban Televison , zan sha kallo ni dai 🤣🤣✌✌ )

{ PAGE 23 🥀 ❤ }

dawowa Amar ya yi ya koma ya zauna geffen Assad ya ce mishi " yanzu me ka ke Tunani a kai "

" nothing ! " Assad ya fada a takaice kafin ya tashi ya nufi bedroom din shi ya shige ya bar Amar nan zaune

da kallo Amar ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya tashi shi ma ya fice part din

* SAFA 💋

bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn gidan su , har ta wuce stair ta jiyo Muryar Momy ta na kiran sunan ta

a hankali Safa ta juyo ta kali cikin parlourn
ta na zaune saman sofa three seaters , ga kuma Sami zaune ta sofar da ke geffen ta , ya tsare Safa da ido

ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta juya ta koma cikin parlourn ta zauna saman sofar da ke fuskantar ta shi

ta na shirin magana momy ta riga ta cewa " da ga ina ki ke Safa "
dan karamin tsaki Safa ta yi ta na kauda kan ta gefe ta ce " ba ga ni na dawo ba "
" kin san fa mun damu a kan ki , har kiran ki na yi amma wayar ki ta na cikin bedroom din ki " Sami ya fada cikin sanyi murya

a hankali ta juyo ta kale shi kafin ta kali momy ta saki wani karamin murmushi ta ce " i'm sorry , mu na tare da doctor ne "

" shikenan , tashi ki je ki yi wanka sai ki sauko mu yi breakfast " momy ta fada

gyada mata kai kawai Safa ta yi kafin ta tashi ta nufi stair ta Haye

sai da ta Haye sannan momy ta kali Sami ta ce " me ka ke jira har yanzu ba ka tafi ba "
cikin ko in kula ya ce mata " saman kan ki na ke ne , kin ga ko wlh ki bar shiga harka ta ko kuma na fashe kwalbar "

cike da rudu momy ta ce mishi " wace kwalbar kuma ? "
yar karamar dariya Sami ya yi kafin ya ce " za ki sani nan gaba , gobe zan zo mu tafi wajen dan uwan ta , gobe ne birthday din shi "

a dubu dari momy ta mike tsaye cike da bacin rai ta ce mishi " in dai na isa da ita to babu inda za ta je , ni dama na san ba banza ka zo gidan nan ba , wlh ba bu inda Safa ta je , musaman wannan wajen "

mike wa tsaye Sami ya yi ya karaso gaban ta ya tsaya ya na kallon cikin idanun ta ya ce " Ni kuma zan gwada miki ba ki isa ba da ita , wannan asirin da ki ke boye mata tsawan shekaru , ya kusa zuwa karshe , Dan uwan ta ne , kuma sai ta je ganin shi "

" Sami fice min da ga gida , Kuma kar ka sake zuwa gidan nan , dan ba al'heri ba ne gare ta , tsawan shekaru sai yau ka tuno da ta na da dan uwa bayan kun raba ta da shi "

cikin konciyar hankali ya katse da cewa " kun dai raba ta da shi , kar ki manta duk abun da ya faru da su da hannun ki a ciki , ke da wancen yayan na ki da na ke kira uba , a tare ku ka yi musu yankar baya , duk ranar da ta gano abun da ki ke boye mata sai ta tsane ki fiye da makiyin ta "

" sami ya ishe ka haka , kar ka manta ni fa kanwar mahaifin ka ce , kuma cikin gida na ka ke "

" correction , cikin gidan Safa na ke , ko kin dauka ban da masaniya a kai , ki fara kirga lokacin da ya yi miki saura , nan gaba kadan za ki je in da ku ka aika Uncle Abdoul Karim , ba gidan yari ba , no afterlife "

ya na gama fadar haka ya saki wani cool murmushi ya fara takawa ya nufi kofar fita parlourn ya fice

da kallo ta raka shi har sai da ya fita , sai cika ta ke ta na batse wa allamun ya bata mata rai sosai
shi ko Sami ko ajikin shi ya shiga motar shi ya bar gidan

bangaran Safa kuma kai tsaye bedroom din ta ta wuce ,
ta na shiga ta sa hannu ta zuge Zip din Abayar ta har kassa sannan ta cire abayar ta tila saman sofa sannan ta nufi toilet

After some minutes ta fito sanye da bathrobe ta nufi Dressing mirror din ta , ta dauki lotion din ta , ta dawo bakin gadon ta , ta zauna sannan ta fara shafawa
Chapter 44 · 0% Book details