← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 66

Sashe 34

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da su ka yi mai isar su sannan su ka yi shiru
Raïssa ta kali Noor ta na tsuke gera ta ce " ke me ki ke yi wa dariya "

Daga kafadun ta Noor ta yi allamun ban sani ba ta na dan murmushi
Hararrar wassa Raïssa ta yi mata , yau karan farko da Noor ta yi wani abu ba ta ji haushin ba , da ga haka kowa ya ci gaba da aikin gaban shi

* AFTER TWO DAYS

* SAFA 💋

Misalin karfe 6 na safe ta shirya ta na shirin fitowa gida dan ta tafi Abuja
Ta na sanye cikin wata Abaya pink colour mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta a kai , ta ratayo wata yar karamar bag white colour , ta yi kyau over

Da sauri ta nufi parking space , ta na shirin shiga motar ta shirin shiga motar ta , Amar ya shiga gidan
Ya na sanye cikin trouser black colour da t-shirt pink colour
Ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta fasa tafiya wajen motar ta , ta nufe shi

A tsakiyar harabar gidan su ka hade tun kafin ta yi magana ya ce mata " gaskia kayan nan su yi miki over "

Hararrar wassa ta yi mishi kafin ta ce " ka fara sa idon naka ko "

Yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " shikenan na daina , yanzu mu tafi kar mu yi late " ya fada ya na shirin juyawa

Da sauri ta ce mishi " ina kuma za mu je ? Ni fa Abuja zan je "

Ba tare da ya tsaya da ga tafiyar shi ba ya ce " eh ni ma cen zan je , sai mu tafi tare ko "

Juya wa ta yi ta kali motar ta kafin ta juyo ta kale shi ta ga har ya isa bakin gate

Da sauri ta bi bayan shi su ka fita gidan a tare
Nan ta ga motar shi an yi parking din ta bakin gate din gidan su
Shi da kan shi ya bude mata kofar motar ya na mata bismillah
Ba musu ta shiga ta na yi mishi godiya
Saidda ta shiga sannan ya meda kofar ya rufe ya zagayo da sauri ya shiga wajen driver ya tada motar su ka bar wajen
Duk abun da ya faru a kan idon Assad dan ya na tsaye saman balconyn gidan su
Sarai Amar ya lura da shi amma , Ita Safa ba ta gan shi ba , sai da ya ga sun bace wa ganin shi sannan ya juya a hankali ya koma cikin bedroom din shi

Bangaran su Amar kuma , su na barin wajen Safa ta tambaye shi in ya san hanyar Abuja
Murmushi mai dan sauti ya yi ba tare da ya ce mata komai ba

Daga kafadun ta yi ta na dan tabe baki kafin ta bude bag din ta , ta ciro earpiece din ta ta saka a kunne sannan ta kunna music , ta kontar da kan ta saman glass din kofar ta ta lumshe idanun ta

Dan satar kallon ta Amar ya yi , kafin ya yi dan karamin murmushi kassa kassa ya ce " I Love you "

A dubu dari Safa ta ware idanun ta , ta na jujuya idanu kamar wadda ta ga wani abun tsoro
Sannan slowly ta meda su ta rufe
Da ga haka ba wanda ya sake ce ma wani komai har sai da su ka karaso building din Tauraruwa
Bayan Amar ya yi parking din motar ya sauko da kan shi ya bude mata kofa ta sauko sannan ya rufe .
A tare su ka nufi Hall din building din su ka shiga a tare
Duk inda su ka wuce sai mutanan wajen sun juya sun sake kallon su dan ba karamin kyau su ka yi ba , musaman da ya ke ba wanda ya san Amar sai ba su cika shi da hayaniya ba

Bayan su je sai da Safa ta roki Nabil da Ya kula da Amar kafin a fara daukar shirin za ta yi magana da Mutalab one minutes
Ba musu Nabil ya ja Amar su ka nufi waiting room ya tsaya ya na yi mishi hira , shi dai Amar kallon shi kawai ya ke yi dan bai san abun da ya ke fada ba saboda da haoussa Nabil ke yi mishi magana shi kuma ba haussar ba ya ke ji

Bangaran Safa kuma kai tsaye office din Mutalab ta wuce
Sai da ta yi mishi knocking kafin ta tura kofar ta shiga ta na yi mishi sallama
Da fara'a a fuskar shi ya amsa mata sallamar ta sannan ya daura da cewa " Miss Safa har kin karaso kenan ? "

Karaso ta yi cikin office din ta na murmushi ta ja chair ta zauna sannan ta ce " eh yanzu na iso fatan na same ku lafya "

" Alhamdoulilah Thanks God , ke fa ya week din ki "
" Alhamdoulilah ! " ta fada a takaice

Gyada kan shi ya yi kafin ya ce " ya ? Kun yi magana da Doctor Amar din ? "

" eh mun yi magana da shi amma ya ce yau ba zai samu damar zuwa ba sai dai next week "

" wow ! Gaskia na ji dadin hakan , kenan yau da wa za ki yi hira ? "

" Doctor Sadeeq , mun yi magana da shi kafin mu iso ya ce karfe 10 dai'dai ya iso nan "

Duba watch din hannun shi Mutalab ya yi kafin ya ce " to ai ga shi karfe 10 ba two minutes , ya kamata ki je ki fara daukar "

Jinjina mishi kai ta yi kafin ta ce " okay , dama na zo na fama maka cewa next Friday , ina da exams ba zan samu damar zuwa ba , if it is possible , na zo ranar monday ni da Doctor Amar sai mu yi daukar "

Shiru Mutalab ya yi na dan second ya na kallon ta kafin ya saki wani dan karamin murmushi ya ce " Ba damuwa , amma sai kin zo tun karfe 8 saboda ran monday akwai dauka dayawa da za a yi "

Cike da zumudi Safa ta mike ta na fadin " na gode sosai sir "
" mu ne da godiya yanzu je ku fara shirin ku ? "
Jinjina mishi kai tayi kafin ta nufi kofar fita ta na yi mishi sai an jima

Ta na fitowa ta ci karo da Yasmina ta taho neman ta
" Yawwa Safa ke na zo nema, tun dazu doctor Sadeeq ya zo ya na jiran ki a filin dauka ke kadai mu ke jira " Yasmina ta fada

" Mu je to tun da kun gan ni " Safa ta fada ta na murmushi
Gyada mata kai Yasmina ta yi kafin ta juya, Safa ta bi bayan ta su ka nufi lift su ka hau floor din da a le daukar

Duk an yi shirye shiryen da su ka dace Safa kadai a ke jira har doctor Sadeeq ya na wajen shi a zaune

Ta na shigowa wajen ta nufi chair din ta da sauri ta zauna ta na ba mutanan wajen hakuri late din da ta yi da ga nan su ka shiga gaishe da juna

Wanda ke kula da camera ne ya daga murya ya na fadin " Silent , silent, za a fara dauka in 1 , 2 , 3 Action "

Ya na gama fadar haka Safa ta yi wani dan karamin murmushi ta fara magana kamar haka " Assalam alaikum , ma su kallon mu barkan mu da wannan lokacin , ku na tare da Abokiyar hirar ku kamar dai kullum yau mu na tare da Doctor Sadeeq "
Da ta gama fadar haka ta juya ta kali Doctor Sadeeq ta ce " Doctor barkan ka zuwa zauran Abokiyar hira "
Dan murmushi doctor ya yi kafin ya ce " Yawwa barkan mu "

" yau dai ga shi ka sake dawowa zauren hira ta "
Gyada kan shi doctor ya yi kafin ya ce " haka ne "
" To barkan ku da zuwa "
Murmushi doctor ya yi kafin ya " Thanks " ya fada ya na dan sunkuyar da kai

" Doctor yau zan so mu tatauna a kan Test din da a ke yi kafin a yi aure prénatal test , zan so ka yi mana Karin bayani a kan shi , da kuma mahimancin shi "

Dan jinkirtawa doctor ya yi kafin ya ce " Shi dai wannan test ba dole sai in za a aure a ke yin shi ba , ya kamata a ce da ka kai wajen 18 to 20 years haka , ka yi test din , a wasu gariruwa da dama wannan test is required kafin a aura muku aure , ya kamata a ce tun kafin ku fara soyayya har a je ga zancen auren kun san genotype partner din ku dan gudun matsala da ga baya "

Katse shi Safa ta yi da cewa " yanzu doctor minene mahimancin wannan test din "

" tooo ! Ma fi yawan cin test din da a ke tambaya na HIV ne mutanan mu na nan Nigeria ba su cika tambayar na genotype ba al'halin shi ma ya na da mahimanci , akwai wasu cututuka dayawa da ta hanyar genotype ne kawai a ke iya gano su , take an examples of sickle , Haemoglobin furotin ne da ke jigilar iskar gas, ya ƙunshi sarƙoƙi 4, sarƙoƙin alpha 2 da sarƙoƙin beta 2 , A daya daga cikin sarƙoƙin beta, amino acid na shida shine glutamic acid, maye gurbin wannan acid da valine yana haifar da mummunan haemoglobin da ke nuna HBs ko S wanda ƙarfin aikinsa ya yi ƙasa da na haemoglobin HBA ko A Kwayoyin jajayen jinin da ke ɗauke da haemoglobin S suna ɗaukar siffar sikila, wanda haifar da cutar sikila "

" To yanzu doctor minene mahimancin sani genotype din shi "
Chapter 34 · 0% Book details