← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 66

Sashe 60

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani mugun kallo Marwan ya wurga mishi , ya na kallon shi cikin ido ya ce mishi " Ali Abdourahman , Allah ya isa tsakani na da kai , ka raba ni da Family na , wlh ba zan kyale ka ba "

da sauri Ali ya katse shi da cewa " yi min shiru dan iska kawai , Aikin gama ya riga da ya gama , da kai da mahaifin ka , babu wanda zai bar prison din nan a raye , na yi maka alkawari sai na ga bayan ku baki daya , maganar mahaifiyar ka kuma , eh ta na raye ba ta mutu ba , da ita da Safa duk su na raye , amma da ga yau sun mutu a wajen jama'a a wajen ku  kuma , kai ma da ga yau kowa zai yi tunanin Aryan Abdoul Karim ya mutu tare da Mahaifiyar shi da kanwar shi "

" duk ranar da ka bari na fito prison din nan a raye sai na kashe ka da hannaye na , macuci , Azalumi , maciya amana " Marwan ya fada cike da takaici 

dan karamin tsaki Ali ya yi kafin ya juya ya kali Barister ya ce " Habib mu tafi , Mu fara shirye shiryen aure na da Twinkle " ya kai karshen ya na sakin wani makirin murmushi ya fara takawa zai bar wajen 

da sauri Marwan ya mike ya na kokarin kamo shi amma sojojin nan su ka tare shi
" Ali , ka dawo nan na ce maka , wlh kar ka taba min momy na , Ali ! da kai na ke , kar ka taba min momy , wlh in wani abu ya same ta ba zan kyale ka ba " ya ke fada da karfi ya na neman kwatar kan shi da ga hannun sojojin nan

ya ma manta da karayar da ke hannun shi , har wata zufa ke karayo mishi
shi ko Ali sai tafiyar shi ya ke cikin konciyar hankali ya bar wajen ya na jin duk abun da Marwan ya fada amma bai kula shi ba 

a hankali Jikin Marwan ya fara yin sanyi , nan take ya zube a kassa sumame
sojojin nan na gani ya fadi , su ka daga kafa su ka bar wajen 
su ka bar shi nan konce , ga His excellency rai a hannun Allah , dan zuciyar shi fa ta buga lokaci guda , sam bai yi tunanin dan uwan shi na jini zai iya yi mishi wannan abun kamar wani enemy din shi

          ▪TWINKLE 

zaune ta ke saman sofa , ta yi zugum waje guda , ga wasu bushashun hawaye nan konce saman face din ta
ta na a haka Ali ya turo kofar parlourn ya shigo ya sallama

ta na ganin shi ta mike da sauri ta mike ta nufe shi a rude ta ke cewa " babban yaya , ya su ke , an fitar da su ko ? "

bai ce mata komai ba ya nufi sofa ya zauna sannan ya kai hannu cikin aljihu ya fiddo wata paper ya mika mata

ya na cewa " karba ki karanta , His excellency ya ce na ba ki ita , na san abun da ke cikin takardar ba zai yi miki dadi ba , haka zalika ni ma ban ji dadin abun da his excellency ya fada min , ba na tunanin zan iya yin hakan gaskiya "

a hankali Twinkle ta fara takawa ta nufe shi ta kai hannu ta karbi takardar ta na kallon ta zuciyar ta na duka uku uku

[23/09 à 19:21] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
                        ( YAR JARIDA )

🌸💖 ( A heart touching love story & destiny ) 💖🌸

STORY & WRITTEN BY : MEERAH  👑🌸

【THE ROYALTY LOVE 🕊🌸💕】

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 :FREE BOOK

❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤ : PAID BOOK

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP POSTING ROOM

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/BBWVomizhgVKzcxJo4XRpG

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite

               BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

___________________________________________

LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN , COMPLETE KUMA 400

GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE ⚘❤
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
👇👇👇👇
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
👇👇👇👇👇
Zain (Airtel)
08081129487 

sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753

     ___________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊____________________

             {  PAGE 30 🥀 ❤ }

a hankali ta koma saman sofa ta zauna , ta bude takardar a hankali ta fara karanto abun da ke ciki kamar haka
* MY DEAR MRS ABDOUL KARIM , KI YI HAKURI ABUN DA ZAN FADA MIKI , NA SAN YANZU KOWA YA NA TUNANIN KIN MUTU , NA JI DADIN HAKAN YADDA BA WANDA ZAI YI TUNANIN KAI MIKI HARI TARE DA YARINYAR MU , INA SON KI YARDA KI AURI ALI , NA SAN ABUN DA NA FADA MIKI YA NA DA NAUYI AMMA KI TAIMAKA DON ALLAH KO DAN SOYAYYAR DA KI KE MIN NI DA MARWAN KI YARDA KI AURE SHI , HAKAN NE KAWAI ZAI SA HANKALI NA YA KONTA , KAR KI DAMU DA NI , IN SHA ZA MU FITO DA GA NAN KE DAI KAWAI KI YI ABUN DA NA FADA MIKI , DAN IDAN KI KA BAYANAR DA KAN KI WLH BA ZA SU KYALE KI BA , ABOKAN HAMAYA SU NA DA YAWA MY TWINKLE , BA KA SAN DA WA KA KE TARE BA , KIN GA DAI ABUN DA SU KA MIN , BA NA FATAN WANI ABU YA SAME KI , SHI YA SA NA CE KI YARDA KI AURI ALI YADDA ZAI BA KI KULAWAR DA TA DACE KO DA BAN FITO BA , NI ABDOUL KARIM ABDOURAHMAN NA SAKE KI SAKI UKU , NA BAR KI LAFIYA

SIGN : ABDOUL KARIM ABDOURAHMAN *

tun ba ta Kamala karanta takardar ba , ta fara ruwan hawaye , sai da ta Kamala ta saki takardar  ta saki kuka mai cin rai

ali ya na kallon ta amma bai ce mata komai ba , sai ma mikewa da ya yi ya nufi stair ya Haye ya na wani boyayen murmushi , ya bar ta a nan parlour ta na faman kuka kamar za ta hadiye Zuciyar ta

         ▪PRESENT DAY

            ▪MARWAN

" Bayan sun kai Daddy Hospital , nan Doctor ke ce musu ya shiga doguwar suma , bai farka ba sai da ya yi shekara guda , a hakan ma bai samu wata cikakiyar lafiya ba , dan kullum cikin shan magani ya ke , magana ma gagarar shi ta ke , ya daina yi wa kowa magana ko ni sai a kai a kai ya ke bude baki ya min magana , da ga haka mu ka samu labarin momy ta auri Ali , har sun haifi baby , hakan ko ba karamin tadawa daddy hankali ya yi ba , haka ciwon shi ya sake tashi , na takaice miki , shekara ukun da Daddy ya yi a ciki prison din nan a Hospital ya yi su , da ga baya su ka zagayo su ka kashe shi , one month bayan rasuwar shi , su ka zagayo kai na su ka yi kokarin kashe ni , amma na tsira , kawai wata rana ina barci , wasu sojoji su ka shigo su ka kama ni , su ka kai ni wajen Chief wai na yi kokarin guduwa su ka kamo ni , da ga haka ya meda ni kotu su ka shirya min karya da gaskiya , a sake yanke min hukuncin shekara 20 bayan biyar na farko , bayan na yi shekara biyar , Sami ya kawo min ziyara a prison , nan ne ya ke ba ni labarin abun da ya ji a ranar da hakan ta faru , ashe duk maganar da Ali su ka yi Sami ya ji su , har ma ya yi kokarin tahowa ya fada min amma Ali ya hana shi fita , ya kuma hana shi komawa UK saboda cen Aziza ta tafi da ke , amma duk da haka sai da ya tafi UK dan ganin ki , na san da wuya ki tuna , amma duk lokacin da ki ka tambaye ta a kan momy da Daddy , maganin barci ta ke ba ki , a haka har ki ka kai 16 years sannan ta juya labarin ta fada miki karya da gaskiya , na san abun da ya sa ma ki ka matsa mata ku dawo Nigeria , Duk abun da ya samu Familyn mu har da wannan matar a ciki "
Fadin Marwan da ya tsare Safa da idanu Sai faman ruwan Hawaye ta ke , a ce matar da ta ke kira da momy ita ta raba ta da momyn ta , ta raba ta da Daddyn ta sannan ta raba ta da dan uwan ta

Marwan kuwa ya na gama fadar haka ya saki wani kyawatencen murmushi ya kai hannu ya dauki spoon ya na cewa " Ni fa gaskiya in ba ku son cake din nan , zan cinye abu na " ya fada ya na sa spoon din cikin cake din

wani dan karamin tsaki Assad ya yi kafin ya ce " wai har yanzu ba za ka daina wannan shan Sugar ba , ka tsaya ka mana magana "
Chapter 60 · 0% Book details