Sashe 16
Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali Safa da Haoua su ka karaso wajen su na yi mata sallama
Amma ko amsa musu ba ta yi ba
A tare Safa da Haoua su ka zazauna geffen ta , su ka saka ta a tsakiya
A hankali Haoua ta daura hannun ta saman shoulder din ta , ta ce " Djami kontar da hankalin ki please , ki godewa Allah da ki ka gano gaskiyar wanene Mansour tun kafin a yi auren ku "
Haoua na gama fadar haka Djamila ta fashe ta kuka kamar wata karamar yarinya , hawaye na zubo mata bibiyu
Haoua na shirin magana Safa ta riga ta cewa " Djami ki daina wannan kukan please "
Da sauri Djamila ta rungume Safa ta na fadin " ki yi hakuri don Allah , wlh na yi nadamar yarda Mansour a rayuwa ta " ta ke fada cikin kukan
Dan bubuga bayan ta Safa ta yi kafin ta ce " please ki daina wannan kukan ya isa haka " ta kai karshen ta na dago kan ta ta sa hannayan ta biyu ta shiga goge mata hawayen ta
A hankali Djamila ta fara rage sautin kukan ta ce " Allah ya isa tsakani na da shi wlh ba zan iya yahe mishi cin amana ta da ya yi , na yarda da shi fiye da rayuwa ta , ba abun da ban yi ba a kan shi amma shi ne zai yi min haka "
Ta kai karshen ta na raba jikin ta da na Safa ta koma ta daura hannayan ta biyu a kai
Dafa kafadar ta Haoua ta yi cikin sigar rarrashi ta ce " ki yi hakuri Djami , in sha Allah sai ya yi nadamar .. "
Ba ta karasa maganar ta sakamakon hannun ta Safa ta riko allamun ta yi shiru
" Djami fada min gaskia , Wannan Dirty boy din ya yi miki wani abu ? " Safa ta fada ta na daura hannun ta saman shoulder din ta
Kallon ta Haoua ta yi ta na zaro idanu ita ba ta gane inda tambayar Safa ta dosa ba
Ita kuma Safa da allamun magaganun Djamila sun sa ta fara yin wani tunanin daban
Su na a haka su ka jiyo Muryar Djamila ta na fadin " Safa, wlh na yi nadamar mallaka mishi kai na , ban San abun da ya shige ni ba a lokacin har na yarda "
Katse ta Haoua ta yi da cewa " ke Djamila maganar me ki ke yi haka yi magana yadda zan gane " ta fada cikin rudu
Safa ce ta amsa mata da cewa " ta na nufin ya yi dis virgin din ta , i think she is pregnant "
A dubu dari Haoua ta mike ta na fadin " What ? Pregnant fa ki ka ce Safa , ke Djamila da gaske ne abun da ta fada ? " ta kai karshen ta na dawo da kallon ta kan Djamila da ta sunkuyar da kai ta na kuka kassa kassa
Sai da ta dan dauki lokaci kafin ta jinjina mata kai ba tare da ta ce komai ba
Salati Haoua ta yi ta na daura hannayan ta saman kai
Ita dai Safa da ido kawai ta ke bin su dan dama ta hango hakan
Cike da takaici Haoua ke fadin " haba Djamila , haba Djamila ta ya za ki yi irin wannan abun , ina ilimin ki , sau biyu ki na saukar Alkur'ani ki na cikin ta ukun , amma za ki yarda ki aika ta zunibi irin wannan "
Da sauri Safa ta katse da cewa " Haoua ya isa haka don Allah " ta fada da dan karfi
Komawa Haoua ta yi ta zauna ta buga tagumi
Dafa kafadar Djamila Safa ta yi cikin sanyin murya ta ce " Djami ban ga laifin ki ba , na san ba a kan ki a ka fara wannan abun ba , mata dayawa su na yarda da kalaman da namiji har su mallaka musu abun da ya fi ko wane daraja a rayuwar su , sai su yi anfani da son da a ke musu su na sa yan mata su yi musu duk abun da su ke so , musaman idan da maganar aure tsakanin ku , za ki ga ya yi anfani da hakan ya na yi miki wasu abubuwa kamar mata da miji , idan kuma ki ka ki ba shi dama , ya ce miki ai da maganar aure tsakanin ku , nan gaba kadan za ki zama matar shi ko wani abu ya faru tsakanin ku ba matsala ba ce , bayan sun samu abun da su ke so har maganar auren janye wa su ke , Idan kuma a ka yi auren , ba zai taba yarda da ke ba , dan kullum tunanin shi kin konta da wasu mazan bayan shi , Djami kin yi ganganci gaskia , yanzu babyn da ke cikin cikinki ya za ki yi da shi , in yan gidan ku su ka san wannan maganar ya za ki yi da wane ido za ki kale su "
( 🤧🤧 gaskia Mansour bai kyauta miki ba , kema kin yi rashin hankali 🤧 ba sadakin ki ba ya kawo kawai tambaya ce ya yi amma za ki tashi ki bashi akalar rayuwar ki 🤧 gaskia mata ya kamata mu yi wa kan mu fada a kan yarda da saurayi lokaci guda har ya kai mu aika ta abun da za mu jima mu na nadamar shi 🤧 samarin yanzu duk Samarin shaho ne sai iya sa kaya da karya amma ba sisin kobo ba ilimi adini bare na boko 🤣🤣🤣 )
Ita dai Djamila ban da kuka ba abun da ta ke yi , ta rasa da wani ido za ta kali Safa da Haoua wannan abun kunya da me ya yi kama
Su na a haka Haoua ta ce " yanzu ya za muyi da wancen dan iskan mu kai karar shi police station "
Cikin nitsuwa Safa ta ce " no ko mun kai karar shi ba abun da zai faru , ai ita ta kai kan ta , ba abun da zai janyo mata sai kunya da kananan magaganu "
Da sauri Djamila ta katse ta da cewa " ni aborted din shi zan yi " ta fada cikin kukan nata
Hannu Safa ta kai ta dan buge ta a baya ta ce " ba ki da hankali ne , zunibi biyu ki ke son yi , ga na ciki , ga na zubar da shi , are you mad ? Yanzu ki fara fadawa dirty boy din nan ki na da ciki , da ga baya ma san abun yi " ta na gama fadar haka ta mike ta fara takawa ta bar wajen
Da sauri Haoua ta mike ita ma ta bar wajen
Su ka bar Djamila ita kadai zaune ta na faman kuka
Bangaran Safa kuma kai tsaye parking space ta nufa ta shiga motar ta ta tada ta bar school din
Bari dai in leko Noor yanzu gaskia
▪ABUJA ( GIDAN SU TWINKLE )
Zaune Noor ta ke cikin parlour ta na kallon Tv
Ta na sanye da wata gown mai bala'in kyau ta sha adon stone , light green colour ce , ta na da wani madauri da ga tsakiyar ta , ta na sanye da wani dan karamin hijab White colour
Ta daura wani Bowl dauke da popcorn saman cinyar ta , ta na ci ta na kallon Tv
Ta na a haka wata kyakyawar budurwa ta shigo parlour ta na sallama
Ta na sanye da wando jeans Navy blue , da riga dai'dai guyiwa white colour , ta na yafe da wani veil Baki , hannun ta rike da wata yar karamar bag
Yarinyar ta na da dan tsayi , da jiki , skin din ta chocolate ne mai kyau ta so ta dan yi kama da Sami musaman wajen hancin su , a shekaru za ta kai 23 years haka
Ta na shigowa ta samu doguwar sofa ta Haye ta na fadin "ke Noor , tashi kawo min ruwa "
Ko kallon ta Noor ba ta yi ba ta ci gaba da kallon TV din ta
Kai hannu yarinyar ta yi ta dauki remote ta kashe Tv kafin ta kali Noor ta ce " za ki tashi ko sai na dake ki "
Slowly Noor ta jiyo ta kali yarinyar nan sama da kassa kafin ta ja dan siririn tsaki ta kauda kai gefe ta ce " in ni zan kawo miki ruwan kar ki sha "
Zaro idanu yarinyar ta yi ta na mikewa tsaye ta ce " Gaskia ne , wuyan ni ya isa yanka Noor , har ni za ki kalla ki fadawa wannan maganar "
Noor na shirin magana ta ga an turo kofar parlourn a na sallama
Ta na jiyo Muryar shi ta saki wata yar karamar kara ta fashe da kukan karya ta daura hannun ta guda saman kumatun ta
Wani dattijo ne ya shigo cikin parlourn ya na sallama , ya na sanye da manyan kaya na shadda Fara , kamanin shi Daya da Sami har yanayin Skin din su wato Chocolate , ya dan lattijantaka a shekaru zai kai 50 zuwa 55
Ya na shigowa ya jiyo kukan Noor
Da sauri ya nufe ta ya na fadin " Chalele na me ya faru ki ke kuka "
Cikin kukan karyan na ta ta ce " Daddy , ba Raïssa ba ce , wai cewa ta yi na dauko mata ruwa , shi ne na ce mata Film na ke kallo ta kira Maid ta kawo mata , shi ne ta dauki remote ta kashe min Tv har da mari na " ta kai karshen ta na saukowa da ga saman Sofar har sai da bowl din popcorn ya zube a kassa ta nufi stair da gudu ta Haye