← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 66

Sashe 32

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddumar ta ta nufa ta hau ta tada sallar ta
Kamar dai kullum yau ma da ta Kamala sai da ta zauna karatun kur'ani har lokacin sallar isha ya zagayo ta tashi ta yi
Bayan ta gama duk sallolin ta , sai ta cire hijabin ta ta ajiye saman sofa sannan ta nufi bed din ta ta Haye ta konta ta kai hannu ta dauki remote ta kara gudun ac sannan ta kashe lamps din dakin ta janyo bargo ta rufe duk jikin ta har kai , ta karanto adu'ar barci ta lumshe idanun ta ba ta yi 30 minutes barci barawo ya yi gaba da ita

* WASHE GARI

Har wajen karfe 9 na safe , Safa ba ta farka da ga barcin ta ba , kuma momy ba ta tafi neman ta ba kawai ta sa kai ta fice ta tafi wajen aikin ta dan ta san kullum sai Safa ta riga ta fita shi ya sa ba ta tsaya neman ta ba

Ta na tsaka da barcin ta kawai sai ta ji wani mugun haske ya ziyarce ta
A hankali ta ware idanun ta kafin ta meda su da sauri da datse cikin wata yar siririyar murya ta ce " ke Balki rufe min Windows din nan "

" ba ita ba ce " ta jiyo Muryar shi ya na fada
A razane ta bude idanun ta ta fara bin dakin da kallo
Cen ta hango shi tsaye wajen Window ya nade hanayan shi a kirji ya na kallon ta , ashe shi ne ya janye curtain din ya bude Window din , ya shigo gidan nan ya janyo Snoopy su tafi wajen Rex sai ya ga har yanzu motar ta na cikin parking space , shi ne ya shigo ya wuce kai tsaye bedroom din ta nan ya gan ta konce

Bargon ta ta janyo ta rufe fuskar ta ta na fadin " please rufe haske ya yi min yawa "

Ba musu ya rufe Window din amma bai meda curtain din ba , sannan ya karaso bakin gadon ya tsaya ya na fadin " why har yanzu ba ki tashi ba , na zata kin tafi school. Ko ba ki da lectures yau "

Ba tare da ta fito da ga cikin bargon ta ba ta ce " ina da "
" kuma ki ke konce har yanzu , Oya wake up " ya fada ya na sa hannu ya janye duvet din ta

Da karfi ta sa hannayan ta duka biyu ta janyo duvet din ta na fadin " please let me , ba na jin jiki na "

Sakin duvet din ya yi ya na fadin " faduwa ta zo dai'dai da zama , ke da ki ke da doctor guda a gida , fada min me ya ke damun ki " ya kai karshen ya na zama bakin gadon

Juya mishi baya ta yi ta na fadin " i don't need your help , please let me "

" Baby , please wake up , tell me what's wrong with you ? "

Slowly ta juyo , ta janye duvet din ta ta dago kai ta kaleshi ta ce " minene ka ce ? "

" what's wrong with you ? " ya maimaita mata
Girgiza mishi kai tayi kafin ta ce " no ba shi kafin wannan "
Shiru ya yi na dan mintina ya na kallon ta slowly ya ce " baby ? "
Tsuke fuska ta yi kafin ta ce " kar ka sake kira na da wannan sunnan ko na fassa maka baki "
" okay ! Okay ! Na gane abun da ke damun ki , yanzu tashi ki shirya mu tafi shan ice cream tun da ba ki son zuwa school din "

Bai gama rufe bakin shi ba ta sauko da ga saman bed din da gudu ta shiga toilet
Da kallo ya raka ta ya na dan karamin murmushin
Sai da ya ga ta shiga toilet ta rufe kofar sannan ya tashi ya fice dakin , amma ba parlourn kassa ya sauka ba , a na sama ya tsaya ya zauna saman sofa ya daura kafa daya bisa daya ya ciro wayar shi ya fara latsawa

Ya dauki wajen good 50 minutes a haka , har sai da ya fara gajiya da jiran ta , kar a je te koma barci ta share shi
Dan karamin tsaki Amar ya yi kafin ya mike tsaye ya fara takawa ya nufi bedroom din ta

Bai kai ga yin taku hudu ba ya tsaya cak ya na kare mata kallo
A hankali ta ke fitowa da ga cikin bedroom din ta na sanye cikin wata shegiyar Gown mai mugun kyau pink colour mai zannen flowers red & green colour da ga sama ta na da sirarren hannu da wata belt fara kal da ga tsakiya gown din ta zauna mata sosai kamar a jikin ta a ka yi ta
Ta na dan yafo wani veil fari kal da ga sama, wannan karan ba ta yi Rowling din shi ba , ta gyara gashin ta , ta meda shi baya ta daure ta sako wasu dan siraren guda biyu sun zubo mata a geffen fuska
Kafafun ta kuma na sanye cikin wasu sneakers White colour su ma da wata yar bag fara , sai tashin fitinannan kamshi ta ke , gaskia ta yi kyau over
( kamar na sace ta na gudu 😭😭😭 )

Tun da ta fito ya tsare ta da idanu babu ko kiftawa ya na saki wani cool murmushi , ji ya ke duk ta tafi da imanin shi
Sai da ta karaso gaban shi ta na ce mishi su tafi amma sam bai ji ta ba sai da ta kai mishi bugu a ciki

Wata yar siririyar kara ya saki ya na daura hannun shi saman ciki ya ce " why ? "
Hararrar shi ta yi kafin ba tare da ta ce mishi komai ba ta fara takawa a hankali ta yi gaba
Murmushi mai dan sauti ya yi kafin shi ma ya juya ya bi bayan ta su ka sauko stair din a tare
Kai tsaye harabar gidan su ka fito
Su na fitowa ko ta ga wata dankareriar mota fara kal an yi parking din ta dai'dai kofar fita gidan abun ya ba ta mamaki

Ta tsaya ta na karewa motar kallo ta jiyo Muryar Amar da ga bayan ta , ya na fadin " mu je ko ? "
Ba musu ta bi bayan shi su ka nufi wannan motar ,
Da kan shi ya bude mata kofar motar ya na ce mata bismillah
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta shiga cikin motar , ta na shiga ya rufe kofar ya zagayo da sauri geffen driver ya bude kofar ya shiga
Ya na shiga gateman da ke zaune saman chair ya na kallon su ya yi sauri ya bude musu gate din

Kunna motar Amar ya yi , sannan ya danna hancin motar saman titi ya bar gidan da mugun gudu

Sai da su ka bar unguwar sannan ya kale ta ya ce " ina mu ka yi dan ni ban san Garin nan ba "

" ba damuwa mu je zan gwada maka "
Da to ya amsa mata kai ya meda hankalin shi kan tukin shi
Kwatancen ta shiga yi mishi har su karaso restaurant din da ta ke yawwan zuwa ita da su Haoua

Bayan ya yi parking din motar a parking space ya yi sauri ya sauko ya zagayo ya bude mata kofar yanzu ma

Hararrar wassa ta yi mishi kassa kassa ta ce mishi " sai ka sa mutanan wajen nan sun lura da mu "

Mika matta hannun shi ya yi ya na fadin " i don't care "
Murmushi kadan ta yi kafin ta daura hannun ta saman na shi , sannan ta sauko da ga cikin motar ya meda kofar ya rufe , su ka nufi cikin restaurant din su na rike da hannun juna

Sun yi sa'a babu mutane dayawa a yanzu dan bai fi mutun 8 da su ka tardo cikin restaurant din ba
Wata table mai chair biyu su ka nufa a tare
Sai da su ka karaso sannan ya saki hannun ta ya janyo mata kujera , ba musu ta zauna saman chair din , shi kuma ya ja dayar chair ya zauna su na fuskantar juna

Su na zama wani server ya karaso table din su ya na tambayar su abun da za a kawo musu
Safa na shirin magana Amar ya riga ta ba da order din bowl din ice cream biyu daya ta chocolate daya kuma vanila , da to server ya amsa mishi kafin ya juya ya bar wajen

Ya na barin wajen ko wayar Amar ta fara ringing
Hannu ya sa cikin aljihu ya ciro wayar ta shi ya kali screen din wayar

Wani kyakyawan murmushi ya saki kafin ya sa hannu ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na fadin " Sai yau ka tuno da ni ko ? "

A daya bangaran kuma yar dariya Fares ya yi kafin ya ce " Sorry Doctor ka tafi ka bar ni da aiki ba dole ka ji ni shiru ba , anya ni ba zan biyo ka na dan huta ba "

Yar karamar dariya shi ma Amar ya yi kafin ya ce " no yi hakuri ka zauna ka kula ma na da Hospital ni ma ba zan jima ba "

" okay na ji na ba ka two weeks ka dawo ko ni na taho "
Da sauri Amar ya ce " haba guy ai ko one month Albarka , kar ka manta ni da Sasha mu ke tare ko yanzu ya gama aikin shi sai mu juyo "

" haba don Allah ? Yanzu da gaske Sasha ya na Nigeria , kam ! Kuma bai mutu ba har yanzu "

Katse shi Amar ya yi da cewa " ban son shirme ya mutu kamar ya , ko kai za ka zo ka kashe shi "
Chapter 32 · 0% Book details