← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 66

Sashe 39

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Amar , don't forget Aryan ba na Nigeria ba ne ....... "

Da sauri Amar ya katse shi da cewa " Sasha please use your brain , Aryan , Daddyn shi na Nigeria ne , kuma ya tabatar mana da ga Nigeria ya taho RUSSIA shi da wata friend's din momy ka na tune da ita "

Gyada mishi kai Assad ya yi allamun e

Ci gaba da magana Amar ya yi ya na fadin " she is our neighbor , ita da Miss Safa su ke zaune a cikin gidan nan , lokacin farko da na je gidan ina tambayar Miss Safa , nan na yi karo da ita , ta tsaya mu ga gaissa ta na tambaya ta mutanan gida , da farko ban gane ta ba amma yanzu ina da tambacin ita ce , ita ce Sasha "

" to ko ita ce me ka ke son na ce mata ? " Assad ya fada ya na mikewa zai bar wajen

Da sauri Amar ya sha gaban shi ya na fadin " Sasha ba ka son ka san abun da ya samu Aryan ne , he was your best friend ! Ta ya zai dauke lokaci guda babu shi babu alamun shi just like this , in ya na nan Nigeria ya kamata mu san halin da ya ke ciki , ya na raye ko ya mutu "

Shiru Assad ya yi na dan mintina bai ce komai ba ya na dai kallon Amar , sai da ya gaji da kallon Amar din sannan ya raba ta geffen shi ya wuce ba tare da ya ce mishi komai ba

Dan daga kan shi sama Amar ya yi ya lumshe idanun shi kafin ya sauko da kan shi slowly

" na fi ka damuwa a kan shi , ba ka yi mamakin yadda mu ka sauka cikin gidan da ya ke fuskantar gidan matar da ta rike shi a RUSSIA ba , bayan komawar ka UK sai da na zo Nigeria har sau biyu dan neman shi , amma ban yi nassara ba , wannan zuwan ma da na yi na zo ne dan na samo inda ya ke , kar ka manta Aryan kamar family na ya ke , wannan bacewar ta shi lokaci guda ta jima ta na damu na, amma wannan karan ba zan bar Nigeria sai tare da shi " Assad ya fada da ga haka kuma ya sa kai ya shige dressing room

Dan karamin murmushi Amar ya yi ya na jinjina kan shi kafin ya fara takawa ya fice dakin

* WASHE GARI

Yau tun karfe 7 na safe Safa ta farka da ga barcin ta ta shiga kitchen , musaman yau ta ce ita za ta shirya wa Amar da Assad breakfast ,

Wajen karfe 8 ta Kamala ta koma bedroom din ta yi wanka ta shirya cikin wando palazzo da T-shirt duk pink colour ta saka wata yar hula a kan ta sai baza kamshi ta ke

Da ga haka ta fito ta koma kitchen ta dauki basket din ta nufi gidan Su Amar
Bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn gidan
Amar ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi , ya na sanye da wanda three cuter da t-shirt

Ya na ganin ta ya saki wani cool murmushi , ya na amsa mata sallamar ta
Karasowa ta yi cikin parlourn ta ajiye basket din hannun ta saman table ta ce mishi " our breakfast ! "
Kallon basket din ya yi kafin ya juyo ya kale ta ya ce " da gaske ?"

Gyada mishi kai ta yi kafin ta ce mishi " Where is your kitchen , bari na dauko mana plate "

" okay shiga dining room za ki ga door din " ya fada ya na nuna mata dining room just kassan stair

Kai tsaye ta shiga dining room din , saman hannun ta na dama ta ga door din ta kitchen
Babu ko tsoro ta bude ta shiga , kitchen din babba ce gaskia komai na cikin ta white colour ne , ko ina a goge ya ke kamar ba a taba aiki cikin wajen ba

" okay , yanzu ina plate din su ke ?" Ta tambayi kan ta ta na kare wa wajen kallo ta na tsaye waje guda
A hankali ta fara jiyo kamar warin taba , kare ma wajen kallo da kyau ta yi kar a je gaz cooker ne su ka bari a bude ba su sani ba

Cen ta hango gas cooker din , da sauri ta nufe shi , ta na matso da face din ta ta na shinshi na wajen
Amma sai ta ji ba komai
Mikewa ta yi ta na " to da ga ina wannan warin tabar " ta fada ta na jujuya kan ta

Cak ta tsaya ta na kallon wata door cen da ga karshen kitchen din
Ba ta wani bata lokaci ba ta nufi door din nan , ta bude ta , ta shiga wani dan corridor , cikin shi akwai wasu door guda biyu su na fuskantar juna , sai wata guda da ga cen karshe da allamun da ga cen ne warin tabar ke fitowa

Babu ko tsoro ta nufi door din nan ta kama handle din kofar ta murda ta bude
Sai ga ta a bayan gidan , a hankali ta sa kafa ta fito ta kali damar ta babu kowa
Sai ta juyo ta kali hagun ta , nan ta ga Assad tsaye ya jingina bayan shi a jikin bango ya na sanye da kayan barcin shi farare kal , ya saki wannan curly hair din shi ya zubo mishi har saman shoulder ya daga kai sama ya na rike da taba

Dan zaro idanu Safa ta yi kafin ta fara takawa a hankali ta nufe shi ta na fadin " Sasha what are you doing here , tun da safe ka na shan taba ka san irin illar da za ta yi maka ne " ta kai karshen ta na sa hannu ta buge tabar hannun shi

A dubu dari ya juyo ya kale ta ya sa hannu ya zare glass din shi
Dum ta ji gaban ta ya fadi har sai da ta dan yi baya kamar za ta fadi , ba karamin tsoro ta ji yin arba da idanun shi ba
Ya na da dara daren Sexy eyes farare kal kamar madara sai dai kwayar cikin su ta banbanta , eye din shi na dama colour din shi light green ne , na hagu kuma hazel ne

Murya na kerma Safa ta ce " you are minnow ? That's why you always make glass ? "

A hankali ya juya kan shi cikin sanyin murya kamar an yi mishi dole ya ce " and so what ? "

" Your eyes are so beautiful " ta fada ta na kara matsowa kusa da shi
Slowly ya juyo da kan shi ya kale ta , nan take idanun su su ka sarkafe cikin na juna duk sun kassa janye wa

Su na a haka su ka fara jiyo Muryar Amar ya na kiran Safa
Dan lumshe idanun shi kadan Assad ya yi kafin ya sa hannu ya meda glass din shi ya raba ta geffen ta zai wuce

Da sauri ta riko hannun shi ta ce " please ka daina shan wannan abun wlh zai ma ka illa " ta fada mishi cikin raunin murya

Shiru ya yi ya na kallon ta ta cikin glass din shi
Sai da ya dauki wajen two minutes a haka kafin ya bude bakin shi a hankali ya ce mata " my hand ! "
Da sauri ta saki hannun shi ta na fadin " i'm sorry "

Ta na sakin shi ya juya ya ci gaba da tafiyar shi ya koma cikin gidan ya bar ta a nan

Ya na shiga ko Amar ya fito ya na kiran sunan ta
Dan karamin murmushi ta yi mishi ba tare da ta ce komai ba
Karasowa wajen ta ya yi kafin ya ce " me kuma ki ke yi a nan ? "
" nothing " ta fada a takaice
" ki na son zuwa pool ko ? " ya fada ya na daga mata gera guda
" pool kuma ? "
" eh " ya fada ya na fara takawa ya raba ta geffen ta ya yi gaba
A hankali ta juya ita ma ta bi bayan shi kafin ta kamo shi har ya sha kwana
Da sauri ta fara takawa ta yi kwanar ita ma
Nan ta gan shi tsaye bakin wata tapkekiyar Swimming pool , mai mugun girma cike pall da ruwa , ruwan sun yi launin Sky blue , gwanin burgewa

Wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta karaso geffen shi ta tsaya ba tare da ta ce komai ta na kallon pool din

" It's beautiful ? " ya tambaye ta ba tare da ya juyo da kan shi ba
" it's really soooo beautiful " ta fada ta na murmushi

Dan karamin murmushi shi ma ya yi kafin ya ce " i know , duk cikin gidan wajen nan ya fi burge ni , i don't know why "
A hankali ta juyo kai ta kaleshi ta ce " me ka ke ji cikin zuciyar ka a yanzu ? "
Shiru ya yi bai ce komai ba
Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " peace , specially with you now "

Dan karamin murmushi ta yi kafin ta juya ta kali pool din
Shiru su ka yi na dan mintina babu wanda ya sake cewa komai su na kallon pool din
Slowly Amar ya bude baki ya ce " Safa , I ............. " kut maganar ta yanke ta kassa fitowa

Ba tare da ta kale shi ba ta ce " what ? "
Da sauri ya juya ya na fadin " yunwa na ke ji "
Yar karamar dariya ita ma ta yi kafin ta juya ta bi bayan shi , su ka koma cikin gidan ta hanyar da su ka zo
Chapter 39 · 0% Book details