← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 66

Sashe 22

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Djamila ta ce " Safa don Allah kar ki tafi ki bar ni " ta fada kamar za ta yi kuka

Juyowa Safa ta yi ta kale ta , ta saki wani cool murmushi ta ce " kar ki damu , yanzu ina dawowa ba zan jima ba " ta na gama fadar haka ta sa kai ta bar dakin
Ta na fita Djamila ta fashe da matsanincin kuka ta na dafe da cikin ta

Bangaran Safa kuma kai tsaye parking space ta nufa ta shiga motar ta ta fice Hospital din da matsanincin gudu
Cikin kankanin lokaci ta isa Police station
Ta na shiga ta yi parking motar ta ta fito ta shiga police station din ta na sallama kassa kassa kamar an yi mata dole

Duk officer din wajen sai da su ka hade yawu su na kallon ta da ga sama har kassa kowa na saka abun shi cikin zuciya
Sarai Safa ta lura da hakan amma ba ta bi ta kan su

Cike da nitsuwa da sanyin murya ta ce " please ina son ganin D.P.O "
Daya da ga cikin su ne ya ce " in kara ce ki ka kawo mu za ki fadawa ba sai kin kai ga D.P.O ba "

A hankali ta juyo kai ta kaleshi sama da kassa kafin ta juya ta kali wanda ke gaban ta ta ce " it's personal , amma tun da kun matsa , ku kiri D.P.O in da kan shi ka tambaye shi mun yi magana da shi zan zo , kuma ya ce idan na zo na same shi kai tsaye office din shi , dan kar ku ce na yi muku ba dai'dai ba ya sa na tsaya muku magana da kai tsaye zan wuce wajen shi , idan na fadawa D.P.O kun bata min lokaci na san ba za ki ji dai'dai ba "

Tsayawa officer din ya yi ya na kare mata kallo da kyau , zuciyar shi na gaskata abun da ta ce dan ta yi kama da irin manyan nan da su ke zowa wajen D.P.O kai tsaye
" okay za ki iya wucewa " ya fada mata ya na nuna mata hanya

Dan karamin murmushi ta yi na fadin " Thanks " sannan ta wuce wajen office din da ya nuna mata
Da kallo duka su ka raka ta har sai da ta shiga office din sannan officer guda ya ce " why za ka barin ta ta wuce a ka je karya ta ke yi ma na ? "
" to ko karya ta yi ma na ai ba za ta yi wa D.P.O ba , in har bai san da zuwan ta ba yanzu tsal za ta fito da gudu " wanda ya yi wa Safa magana ya fada ya na yar dariya

Bangaran Safa kuma a hankali ta shiga office din D.P.O ta na sallama
A hankali D.P.O ya dago kai ya na amsa mata sallamar ,
Ba laifi ya na da dan jini a jika dan a shekaru ba zai wuce 43 years ba haka , ya na sanye da kaki din shi

A hankali ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta kafin ya tambayeta me ya ke tafe da ita
A hankali ta janyo chair ta zauna sannan ta ajiye file din hannun ta saman table din
Cikin nitsuwa ta ce mishi " Good morning , my name is Safa , kara na zo ajiyewa ganin tsaya wa magana da wadancen bata min lokaci zai yi shi ya sa na wuto kai tsaye , wani ne ya yi wa friend di ta ciki sannan ya ba ta maganin zubar da ciki ba tare da sanin ta ba , wannan rapport din ta ne da ke nuna ta sha maganin zubar da ciki , yanzu haka ta na Asibiti a na kula da ita "

A hankali ta kai hannu ta ciro wayar ta da ga cikin jakar ta ta daura saman file din ta ce " cikin wannan wayar kuma akwai video na confession din ta yadda a ka yi ya ba ta maganin ba tare da sanin ta ba "

D.P.O na kallon ta cikin ido ya kai hannu ya dauki wayar ta , ya na kunnawa sai saman video din da ta yi wa Djamila ta na ba ta labarin abun da ya faru

Ashe rike wayar ta da ta yi video ne ta ke yi mata ba tare da ta sani
Duk abun da su ka tatauna sai da D.P.O ya ji ya kuma gani

Bayan ya gama kallon video din ya ajiye wayar gaban shi ya kai hannu ya dauki file din ya shiga dubawa

Ya na tsaka da dubawa Safa ta ce " cikin ice cream din ya saka mata maganin "

Slowly ya dago kai ya kale ta , ya ce " ta ya a ka yi ki ka san cikin ice cream din ya saka mata shi "

Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta ce " hankali na ne ya ba ni "

Murmushi mai dan sauti D.P.O ya yi kafin ya ajiye file din geffen shi ya ce da ita " okay ba laifi , ki turo min video din da kuma pic din saurayin , idan mun kamo shi za mu mika karar kotu tare da hujojin da ki ka kawo " ya kai karshen ya na fido wayar shi ya mika ma ta tare da wayar ta

Karba ta yi ta tura mishi videon da wani pic na Mansour da ta taba dauka saboda bacin rana , to yau ranar ta baci

Ajiye wayar ta yi saman table ta tura wa D.P.O gaban shi sannan ta meda wayar ta cikin bag din ta ta ce " sunan yaron Mansour , gaskia ban san inda gidan su ya ke ba "

" ba damuwa wannan duk aikin mu ne , idan mun kamo shi za mu mika shi kai tsaye wajen kotu ba sai an yi shari'a ba ta yanke mishi hukuncin da ya dace "

Murmushi Safa ta yi kafin ta ce " Thanks a lot sir " ta kai karshen ta na ajiye mishi bandir din kudi yan dari biyar biyar a kila za su kai dubu dari daya

Mike wa tsaye D.P.O ya yi ya na fadin " no , ba sai kin ba da komai ba , ai hakin mu ne kula da al'umar da a ka ba mu , so rike kudin ki za su miki anfani wajen kula da friend's din ki "

Murmushi Safa ta yi kafin ta ce " nagode sosai , ni zan koma likita " ta kai karshen ta na mike wa tsaye za ta fice

Da sauri D.P.O ya ce mata " kin manta kudin ki "
A hankali ta juyo ta na fadin " ba komai tun da ba sai an bada komai ba , a rabawa yan wajen sadaka ce " to kai karshen ta na ficewa office din

Murmushi D.P.O ya yi kafin ya kai hannu ya dauki kudin sannan ya fito office din shi ma , a lokacin har Safa ta bar police station din baki daya

D.P.O na fitowa ya bi duk officer din da ke wajen ya ba su dubu biyu dubu biyu sannan ya ce musu zai turo musu hoton wani saurayi , ya na bukatar su tafi neman shi yanzu da ga haka kuma ya juya ya koma office din shi

Bangaran Safa kuma kai tsaye Hospital ta koma
Ta shiga Hospital din ta yi parking ta fito ta nufi kai tsaye dakin da Djamila ke konce

Bakin ta dauke da sallama kassa kassa ta shigo dakin
Yadda ta bar ta haka ta tardo ko motsi ba ta yi ba , sai dai jinin da a ka saka mata ya kare

Ta na shiga ta koma saman chair din da ta zauna da farko ta zauna ta na kallon ta ta ce " za ki iya tashi na Meda ki gida , dan ni fa ba na jin dadin zama a Hospital "

Jinjina mata kai Djamila ta yi ta na kokarin mikewa zaune , da sauri Safa ta mike ta riko hannun ta , ta janye mata catheter din a hankali sannan ta taimaka mata ta mike zaune kafin ta sauko da kafafun ta a hankali kassa

A hankali ta tsaye ta na cije lips din ta ba karya har yanzu ta na dan jin zafi , amma a hakan ta mike su ka fito Hospital din ita da Safa
Har nurse sai da su ka tsayar da su a kan ba a ba su izinin tafiya amma Safa ta share su , ta nufi motar ta ta budewa Djamila ta shiga sannan ta tada ta bar wajen da mugun gudu dama gwana ce ai

Kai tsaye gidan su ta nufa da Djamila , ita dai Djamila da ido kawai ta ke bin ta kassa cewa komai
Har sai da Safa ta karaso gidan su , nan Djamila ta sha ruwan idon ta, yau dai ta ga irin Daular da Safa ke ciki
Ba ta ida shan ruwan mamakin ta ba sai da su ka shigo parlourn nan ta zama cikakiyar bakyauya

Su na shiga Safa ta nufi doguwar Sofa ta Haye ta konta ta na warware veil din ta
Ita dai Djamila ta na tsaye bakin kofar ta kassa karasowa

Ganin hakan ya sa Safa dan dago kai ta na kallon ta ta ce " me ki ke jira a nan, zo zauna mana za a kawo miki abun sha na san ki na jin yunwa "

Ba musu Djamila ta karaso cikin parlourn ta na jan kafa a hankali ta zauna saman sofar da ke geffen ta Safa

Ta na zama ko Snoopy ya shigo da wani matsanincin gudu
A razane Djamila ta mike ta na sakin kara ta rasa wajen guduwa dama mugun tsoron kare gare ta

Da sauri Safa ta mike zaune ta na fadin " ke kontar da hankalin ki ba abun da zai miki " ta kai karshen dai'dai Snoopy ya karaso wajen kafar ta ya zauna ya na fido halshe waje ya na kallon Safa
Chapter 22 · 0% Book details