← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 66

Sashe 54

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri ta fada jikin shi ta rungume shi tsam ta na fadin " Ina mutuwar son ka ka sani ko ? " ta fada kamar za ta yi kuka 

a hankali ya zagayo da dayan hannun shi a bayan ta ya kai lips din shi saman forehead din ta ya manna mata kiss sannan ya ce " Ina mutuwar son ki ni ma baby "

kamar da ga sama su ka jiyo Muryar wani saurayi bakin kofar shigowa parlourn ya na fadin " and me ? Who loves me ? "

wata yar karamar kara Safa ta saki kafin ta diro da ga saman cinyar his excellency ta nufi saurayin nan da gudu ta na fadin " Aryan , Aryan ! "

ta na karasowa wajen shi ya sa hannayan shi biyu ya daga ta sama ya juya da ita cikin parlourn kafin ya ce " My Puppy , Na yi kewar ki over "

saurayin kyakyawan gaske ne , Fari kal da shi kamanin shi daya tak da Safa ya na kama da yan china , sai dai ya so ya yi jinin Hausawa , a shekaru ba zai wuce 15 years , kunsan yadda yaran turawa ke da saurin tassowa , Idan ka gan shi sai ka ce ya kai shekara 20 , ga shi kuma ya da tsayi da murdaden jiki , gashin kan shi golden ne kamar na Safa shi ma , mai mugun laushi ya daure shi a baya
ya na sanye da wani Jeans White color da T-shirt Navy blue , kafafun shi cikin wasu sneakers farare kal su ma  ya hadu over 

Sai da ya gama juyawar shi sannan ya tsaya , ya ce ma Safa " Na yi kewar ki sosai da sosai "

wata yar karamar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Aryan amma tare za mu koma Moscow ? "
" Yeah tare za mu koma " ya fada ya na fara takawa ya nufi sofa ya zauna

tsuke fuska Twinkle ta yi ta na cewa " Yanzu Marwan ba za ka gaishe ni ba "

wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya sauke Safa ya tashi ya nufi Twinkle ya rungume ta ya na fadin " na yi kewar ki over My momy "

rungume shi ta yi ita ma ta yi ta na fadin " ni ma na yi kewar ka sosai my boy "

a hankali ya raba jikin shi da nata ya na shirin magana His excellency ya kai hannu ya murde mishi kunne ya na cewa " Yanzu tsakani da Allah Marwan me na fada maka ? ba cewa na yi ba ka jira zan je na dauko ka ? "

" ashhhhh Daddy please let me da zafi wlh , kuma na yi wajen one hour da jirgin mu ya sauka na yi ta jiran ku amma ba ku zo ba , shi ya sa na taho na yi muku surprise "

sakin kunnen shi His excellency ya yi ya na cewa " ba za ka kira ni ba ? shikenan yanzu tafi ka yi wanka ka zo ka ci abinci "

" Okay dad " ya fada a takaice kafin ya juya ya mikawa Safa hannu
da gudu ta karaso wajen shi ya sa hannu ya daga sama ya daura saman kafadar shi ya nufi stair ya na fadin " Daddy ka sa a kawo min kayana bedroom di na "

ya kai karshen ya na fara taka stair , a nan ma wani dan karamin parlour ne , komai na cikin Pink color ne , ga wasu Door guda hudu a jere

kai tsaye Door ta biyu ya nufa , ya tura kofar ya shiga ya na sallama kassa kassa
wani kyawatencen parlour ne , ya kawatu da kayan more rayuwa har da fridge komai na cikin Milk color ne , da ga gani wajen kullum cikin Shara da guga ya ke

kai tsaye Door din da ke fuskantar kofar shigowa parlourn ya nufa , ya tura ta
nan kuma wani kyawatencen bedroom ne , komai na ciki Milk color ne , da wani Royal bed Fari kal shinfide da wata bedsheet Milk color mai mugun kyau , gadon ya na fuskantar wasu door guda biyu a tsakanin su kuma akwai wani dressing room dauke da kwallaban Perfume da lautions

a geffen door ta farko akwai wata Sofa three seaters , sai wata one seater a geffen ta
ga wani Chinesse carpet Fari kal gaban ta , saman shi akwai wata yar karamar Table ta glass dauke da flowers irin na decoration haka

cen bayan gadon akwai wata yar table , dauke da books da wata yar karamar laps kamar bedside lamps , sai wata yar chair din ta kamar office haka
a geffen ta Table din akwai wani Wall na zalar glass , an rufe shi da wasu curtain white color su ma abun dai Masha Allah 

kai tsaye saman gadon ya sauke Safa sannan ya kai hannu cikin aljihun shi ya fido wayoyin shi ya ajiye saman bedside drawer
ya na shirin magana wata Maid ta shigo janye da trolley biyu ta na sallama

dan runsunawa ta yi ta na cewa " barka da zuwa yallabai "
ba tare da ya juyo ba ya ce mata " yawwa kai mu su dressing room " ya fada ya na kokarin cire watch din hannun shi
da to ta amsa mishi kafin ta ja trolley din ta nufi door ta biyu ta shiga
ta na shiga , kuma ta fito sannan ta karaso geffen Marwan ta ce " Sir ku na bukatar wani abu ne ? "

" no za ki iya tafiya " ya fada ya na zama bakin gado ya kai hannu ya fara cire sneakers din shi

" Puppy , tashi mu tafi ko ? " ta fada ta na mikawa Safa hannu

noke mata kafada Safa ta yi kafin ta konta saman gadon ta juya mata baya
wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya ce mata " don't worry za ki iya tafiya kawai "

" okay sir " ta fada ta na dan runsunawa kafin ta juya ta fice abun ta

ta na fita Marwan ya mike tsaye ya ce ma Safa " Puppy , zan shiga wanka , kar ki yi min barna kin ji ko ? na san halin ki "

" Aryan , don't forget I'm an angel , babu abun da zan yi "

" hmmmm na ji madam , ke dai kawai na tardo kin taba min kaya , ba zan ba ki gift din ki ba " ta fada ya na fara takawa ya nufi door ta farko

da sauri Safa ta mike zaune ta na fadin " da gaske Aryan ka kawo min gift ? "

" bari na fito ki gani " ya fada ya na shiga toilet din ya janyo Door 

sai da ya dauki wajen good one hour cikin Toilet din kafin ya fito sanye da bathrobe , bai bi ta kan Safa ba ya wuce dressing room 

ya na shiga ko wayar shi ta fara ringing
da sauri Safa ta mike zaune ta kai hannu ta dauki wayar ta jingina bayan ta a jikin forehead din gadon ta dauki kiran sannan ta kai wayar a kunne ta na fadin " Hello  "

Shiru ba a amsa mata ba , a hankali ta sauko wayar ta ga kalli screen din ta ga kiran bai katse ba 
sai ta meda wayar a kunne ta sake cewa " Hello ! Here the earth , is There anyone ? " 

sai da a ka dauki wajen Two minutes kafin ta jiyo wata Zazzakar sexy voice cike da nitsuwa a ka ce mata " where is Aryan ? "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " me za ka ba ni idan na fada maka ? "

ta na gama fadar haka ta ji an kwace mata wayar ,
da sauri ta juyo ta na kallon Marwan tsaye bakin gadon sanye da wasu pajama blue ma su mugun kyau
" me na ce miki ah ? "

" but Aryan , ba abun da na yi fa yanzu na dauki wayar , kuma tambaye shi ba abun da na ce mishi " ta fada cikin shagwaba 

bai ce mata komai ba ya kai wayar a kunne ya ce " Hi guy , how are you ? "

a daya bangaran kuma a ka ce mishi " who is she ? "

murmushi mai dan sauti Marwan ya yi kafin ya ce " ina ruwan ka uban tambaya , where is Doctor ? " ya fada da turanci

dan jinkirtawa ya yi kafin ya amsa mishi da cewa " Ya na barci " ya ba shi amsa da turanci shi ma

" Gaskiya Doctor ya ji dadin rayuwar shi , har ya samu damar yin barci  "

" na ga kai har damar komawa gida ka samu "

" Hmmm na ji shikenan , tell me How are you , ya jikin naka ? "
" Fine , yaushe za ka dawo ? "

wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya ce " har ka fara kewa ta kennan ? "

wani dan karamin tsaki mutumin nan ya yi kafin ya katse kiran ba tare da ya ce komai ba
sauko wayar Aryan ya yi ya na yar karamar dariya kafin ya kai hannu ajiye ta saman bedside drawer , kar ku manta duk maganar nan da su ke da turanci su ka yi ta

[20/09 à 23:47] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
                        ( YAR JARIDA )

🌸💖 ( A heart touching love story & destiny ) 💖🌸

STORY & WRITTEN BY : MEERAH  👑🌸

【THE ROYALTY LOVE 🕊🌸💕】

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 :FREE BOOK

❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤ : PAID BOOK

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite

               BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

___________________________________________
Chapter 54 · 0% Book details