← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 66

Sashe 35

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Yanzu a ce ke AS wato ki na da haemoglobin HBA da Kuma HBS a ke je shi ma wanda ki ke so AS ne akwai chance ta kaso daya cikin hudu ku samu yaro wanda zai kasance SS wato duk haemoglobin din shi ma su siffar sikila ne , to wannan yaron ya na dauke da cutar sikila , tun kafin ya shigo duniya cikin zai iya zubewa , in ma cikin bai Zube ba ya shigo duniya ba zai kai shekara 20 ba zai mutu kin ga wannan daukar al'haki ne "

" Gaskia daukar al'haki ne ...... "

Cikin nitsuwa doctor ya katse Safa da cewa " ko shi wannan blood type da mutane su ka watsar ya na da mahimanci dan ko shi ya na iya hana aure tsakanin ku "

" kamar ya kuma doctor ? "

Gyara zaman shi doctor ya yi kafin ya ce " yanzu a ce ke Rhesus factor din ki negatif ne , shi kuma wanda za ki aura na shi positif ne , yanzu a ce kin samu ciki to yaron da ke cikin cikin ki Rhesus din shi negatif ne , to a nan babu matsala , amma in a ka je Rhesus din shi postif ne nan fa akwai matsala da hadari gare ki , ma'anar Rhesus na babyn yana shiga cikin jinin na ki ta cikin mahaifa, dole ne a kawar da na biyun wato Rhesus positif na babyn daga jinin ki cikin ten minutes bayan haihuwa . in ba haka ba, ba za ku ƙara samun cikin wani ɗa ba , za ki zama sterile "

" to yanzu Doctor ta ya za a iya guje ma wadanan abubuwa duka " Safa ta tambayeshi

" shi dai wannan Rhesus bayan Haihuwa allura ce a ke yi wa mahaifiyar , amma gaskia allurar ta na da tsada , ma fi sauki shi ne tun kafin ku fara soyayya ku tambayi partner din ku genotype din shi , in bai sani ba ba laifi ou tafi Hospital ku yi shi kyauta ne ba sai kun biya ba , zai fi muku ku rabu tun abun bai yi nisa ba da ku zo nu na nadama da ga baya , kin San dama haoussawa ba ce wa rigakafi ya fi magani "

Yar dariya Safa ta yi kafin ta ce " Eh kuma gaskia ne "
Ta na gama fadar haka ta juya ta kali camera ta ce " To ma su kallon mu kun dai ji bayanai da ga bakin Doctor Sadeeq a kan mahimanci Premarital test idan har yanzu ba ki yi shi ba , to tun wuri gwara ku je ku yi ku san genotype din ku da kuma blood type saboda bacin rana "
Dawo da kallon ta ta yi kan doctor ta ce " Doctor mun gode sosai da lokacin ka da ka ba mu "
Murmushi kadan doctor ya yi ya na fadin " no ni ne da Godiya "
" To doctor sai ayiwa ma su kallon mu sallama "
Juya wa doctor ya yi ya kali camera ya na yin sallama
Amsa mishi sallamar shi Safa ta yi kafin ta daura da cewa " Duka duka a nan mu ka kawo karshen shirin na mu na Abokiyar hirar ku , Tare da ni Doctor Sadeeq mu ke cewa mu hadu da ku a sati na gaba na barku lafya "
Ta na gama fadar haka mai kula da camera ya daga murya ya na fadin " Cut ! "
Da ga haka kuma duk mutanan wajen su ka shiga yin tapi , murmushi Safa dai ta yi kafin ta sauko da ga saman plateau din ba ta bi ta kan su ta bar wajen da sauri ko Doctor Sadeeq ba ta tsaya yi ma sai an jima ba
Kai tsaye waiting room ta nufa , bakin ta dauke da sallama ta shigo wajen
Nan ta ga Amar da Nabil su na zaune su na kallon Tv da ke gaban su , ashe duk abun da su ka tatauna su na kallon su directly
Kallon Safa Amar ya yi kafin ya ce " Har kun gama ? "
Murmushi kawai ta yi mishi ta na gyada mishi kai
Mikewa tsaye ya yi ya mika wa Nabil hannu ya na fadin " My friend , see you next time "
Riko hannun shi Nabil ya yi su ka yi musbaha ya ce mishi sai ya dawo , da ga nan Safa ta yi mishi sallama ita ma sannan su ka bar wajen ita da Amar
[10/09 à 20:04] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🕊

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺: FREE BOOK

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ : PAID BOOK

DOMIN SAMUN WANNAN LITTAFIN DA GA FARKO , ZA KU IYA JOING MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

ZA KU IY SAMUN WANNAN PAGE A WATTPAD TA HANYAR WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://www.wattpad.com/1475830151?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=bennybite

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 19 🥀 ❤

Ba su tsaya neman kowa ba su ka bar building din a tare dama Daukar ce kawai ke kawo Safa wajen duk wani abu da ya dace Mutalab ya ce ya dauki nauyin shi ita daukar da kuma guest din ta kawai su ke bukata in wata ya yi kuma su biya ta duk da ita Safa ba dan kudin ba ta ke yi musu aikin su ne dai ba su sani ba

Bayan sun shiga motar su su ka bar wajen su ka hau titi
Safa ta kali Amar ta tambaye shi ina za su je ne yanzu
Ba tare da ya kale ta ba ya ce " Gidan wani uncle di na , tun jiya ya kamata na je amma na bari mu taho tare zan so ya gan ki " ya kai karshen ya na juyawa ya kale ta

Dan karamin murmushi ta yi ta na kauda kan ta gefe
" ka san inda gidan ya ke ne ? " Safa ta tambaye shi ba tare da ta juyo da kallon ta ba

" eh na sani " ya ba ta amsa a takaice
Slowly ta juyo ta kaleshi ta ce " Why ba ku taho tare da Assad ba "

Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi kafin ya ce " bai san da zaman Assad ba , Asali ma a tunanin su ni kadai ne ba Twins ba "

" how? Ban gane ba ka na nufin a tunanin su Assad ya mutu ko ya " Safa ta fada ta na dan lekon face din shi

Shiru ya yi bai ce mata komai ba
Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " zan ba ki labarin idan mun koma gida saboda ya na da tsayi "

Jinjina kan ta kawai Safa ta yi kafin ta juya ta sunkuyar da kan ta ta shiga latsa wayar ta

Sun dauki wajen five minutes a haka kafin ta ji ya danna horn
Ba ta dago kan ta ba har sai da gateman ya bude musu gate , Amar ya danna hancin motar cikin gidan ya nufi parking space ya yi parking ya kashe motar sannan ya sauko ya zagayo geffen Safa ya bude mata kofar ya na fadin " To madam sai a sauko "

Sai a lokacin ta kashe wayar ta , ta meda ta cikin bag din ta , sannan ta sa kafa ta sauko , Amar ya meda kofar ya rufe ya na ce mata su tafi

Dum Safa ta ji gaban ta ya fadi ganin gidan da su ke ciki har sai da ta yi sumar tsaye

Ganin yadda ta yi tsaye waje guda ya sa Amar kamo hannun ta ya ja ta su ka nufi kofar shigowa parlourn
Sai da su ka iso bakin kofar sannan ya saki hannun ta ya yi knocking
Bai kai ga yin na biyu ba a ka bude mishi door din

Ya na shirin shiga wayar shi ta fara ringing
Komawa gefe ya yi ya ce ma Safa ta shiga ya na zuwa

Jinjina mishi kai ta yi ta na hadiye wasu yawu sannan ta daga kafa kamar wadda a ka zarewa lakar jiki ta shiga parlourn ta na sallama , ta yi sa'a ko Daddy ba ya nan shi da Sami da khalifa , amma duk matan gidan su na nan Twinkle kuma ta na bedroom din ta , yan matan ne kawai a parlourn kowa ce na kallon Tv allamun shirin ya yi musu duka

Noor na ganin ta ta tashi da gudu ta rungume ta ta na fadin " oyoyo Safa na "

Dan tsaki Raïssa ta ja ta na kauda kan ta gefe
" zauna bari na je na kira momy " Noor ta fada ta na sakin Safa ta Haye stair da gudu
Ita dai Safa shiru ta yi ta na tsaye waje guda kamar bakuwar gidan

Noor na barin wajen Fadila ta wurga ma Safa wani mugun kallo ta na fadin " ke me ya kawo ki gidan nan ? "

Ba ta gama rufe bakin ta ba Raïssa ta daura da cewa " Ta zo abun da ta saba yi mana , nan fa ba gidan talafin marayu ba ne , kin yi batan hanya "

A tare duk su ka bushe da dariya dai'dai lokacin da Amar ya turo kofar parlourn ya shigo ya na sallama kai a sunkuye ya na duba wayar shi

Raïssa na ganin shi ta mike tsaye slowly , dama jiya Daddy ya fada mata yau doctor Amar zai zo gidan har pic din shi sai da ya turo mata , shi ya sa ta na ganin shi ta saki baki dan fa ya tafi da duk imanin ta

Shi kuma sai da ya karaso geffen Safa ya tsaya sannan ya dago kai ya na meda wayar shi cikin aljihu

Kallon mutanan parlourn ya yi ya saki wani cool murmushi ya ce " Hi guys How are you ? "

Cike da zumudi Fadila ce mishi " Lafya lau ya ka ke ? An zo lafya ? "
Chapter 35 · 0% Book details