← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 66

Sashe 40

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su na shigowa parlourn su ka tardo Assad zaune saman sofa ya na faman latsa wayar shi
Ba su bi ta kan shi ba su ka nufi sofa su ka zauna a tare , su na zama shi kuma ya tashi ya Haye war shi stair
Da kallo su ka raka shi har sai da ya Haye sannan Amar ya kali Safa ya ce " kar ki damu in dai Assad ne , ba ya cika zama da mutane "

Dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " ni dama ba wajen shi na ke zuwa ba "
Kallon ta Amar ya yi ya na dan karamin murmushi , kafin ya juya kan shi ya ci gaba da serving din su
A tare su ka yi breakfast a ranar sannan su zauna ka dan yi hira

Sai wajen karfe 12 sannan Safa ta tashi za ta koma gida
Su na fitowa harabar gidan Ruwan sama su ka barke kamar a bakin kwariya
Da sauri Amar ya ja hannun ta ya medo ta saman yar terrasse din bakin kofar shiga parlourn sannan ya ce ta jira shi bari ya dauko musu umbrella ya juya ya koma cikin parlourn

Ya na komawa ta daga kafa a hankali ta sauko da ga saman terrasse din ta karaso tsakiyar Harabar gidan

A hankali ta sa hannu ta zame hular kan ta ta daga kai sama ta lumshe idanun ta
A hankali ta bude dan bakin ta ta ce " Ya Allah , yadda duniya ta sanyi da dadi saboda saukar ni'imar ka ya rabbi akwai iyayen mu , masoyan mu , da daukacin Al'ummar Annabi kwonce a qarqashin kassa ya Afuwu ya gafuru ka sa kabarburan su su fi sanyi da ni'ima fiye da nan duniya , ya Allah have mercy upon all the departed souls , specially........" kut ta kassa karasa maganar wasu hawaye na zubo mata

[14/09 à 09:34] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 💖🕊

【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 : FREE BOOK

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ : PAID BOOK

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN

GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE ⚘❤
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
👇👇👇👇
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
👇👇👇👇👇
Zain (Airtel)
08081129487

sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

P A G E 21 🥀 ❤

Duk abun da ta yi a kan idon Assad dan ya na tsaye saman balcony shi ma ruwan na sauka kan shi

Ta na a haka kawai sai jin ta yi ruwan sun daina sauka saman face din ta
Da sauri ta bude idanun ta , sai saman wata bakar umbrella , slowly ta sauko da kan ta kassa
Ta na shirin magana Amar ya riga ta cewa " ke da na ce ki jira ni , shi ne za ki shiga ruwan in mura ta kama ki fa "

Kallon shi ta yi na dan lokaci kafin ta saki wani kyawatencen murmushi ta yi baya da sauri ta fita da ga kassan umbrellar ta koma cikin ruwan

Ya na yi taku daya ya ga ta fara juyawa cikin ruwan ta na murmushi
Kawai sai ya tsaya ya na kallon ta , ba karamin burge shi ta yi ba , kawai sai shi ma ya saki umbrellar hannun shi ya shiga cikin ruwan

Ta na ganin hakan ta saki wata yar siririyar dariya ta na ci gaba da juyawar ta
Shi ma yar karamar dariya ya yi kafin ya ce mata " ya isa haka mu koma cikin gida "
Girgiza mishi kai tayi ta na fadin " babu inda zan je sai an ida ruwan nan "
" please mu koma , kar ki yi ciwo "
" koma in ka na so ni b....... " kut maganar ta yanke sakamakon gocewa da kafar ta ta yi fuuuu ta yi baya za ta fadi ta na sakin kara

Cikin zafin nama Amar ya yi kan ta , taku biyu ya yi ya damko kugun ta , ya janyo ta da karfi ta fado saman kirjin shi , sai golden hair din ta ya bazun mata a fuska
" ashhhhhhh " ta fada da karfi ta na rumtse idanun ta

A hankali ya sa hannu ya dago kan ta , ya sa dan yatsar shi ya janye mata jelar gashin da ta zubo mata a face
" ba ki ji ciwo ba dai ? " ya fada cikin sanyi murya
Gyada mishi kai ta yi ta na kallon cikin idanun shi

Bai sake ce ma ta komai ba ya sa dayan hannun shi ya daga ta cak kamar baby ya koma cikin gidan da ita
Su na shiga shi ma Assad ya juya ya koma cikin gidan
Amar kuma bai sauke ta ko ina ba sai cikin daya da ga cikin part na sama ya wuce da ita kai tsaye bedroom din sannan ya sauke ta saman kafafun ta ya ce ta shiga ta yi wanka yanzu ya kawo mata kayan sakawa
Bai jira amsar ta ba ya juya da sauri ya fice dakin
Da kallo ta raka shi har sai da ya fita sannan ta daga kafa a hankali ta na shirin takawa
Ba shiri ta saki yar kara da allamun ta ji ciwo a kafar, amma a haka ta ja kafa ta nufi kofar da ta ke tunanin toilet ce ta shiga ta medo kofar

Ta dauki wajen good 30 minutes cikin toilet kafin ta fito daure da towel a kirjin ta
Ta na fitowa idanun su ka yi mata arba da wata kyakyawar Abaya fara kal shanye saman bed din
A hankali ta karaso wajen good ta na jan kafa , ta sa hannu ta dauki abayar ta na kare mata kallo
Wani cool murmushi ya kubce mata dan abayar ta ta ce , ya san ya na iya tafiya gidan su shi ne bai kai ta ba , sai ya dawo da ita cikin gidan su
A hankali ta dan girgiza kan ta kafin ta nufi dayar door ta dressing room ta shiga
Jim kadan ta fito sanye da Abayar ta yi Rowling veil din ta , ta yi kyau over
Ta na fitowa Amar ya shigo bedroom din ya na sallama hannu shi rike da tray din food
Ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta na amsa mishi sallamar shi

Karasowa ya yi cikin dakin ya ajiye tray din saman table din bakin sofar da ke geffen door ta shigowa
Sannan ya zauna saman sofar ya na fadin " kin yi sallat ? "
Hannu ta sa ta fara warware veil din kan ta , ta ajiye saman bed din kafin ta karaso geffen shi ta zauna sannan ta ce " eh na yi a cikin dressing room "
" to ya yi kyau , yanzu sai ki ci abinci , ki sha magani "
Da sauri ta katse shi da cewa " ni fa ba ni ciwon komai "

A hankali ya daura hannun shi saman kumatun ta kafin ya janye ya na fadin " ga shi jikin ki duk zafi , Oya bismillah yi da sauri tun bai yi sanyi ba " ya kai karshen ya na tura mata plate din gaban ta

A hankali ta kai hannu ta dauki spoon din ta fara ci , shi kuma ya zuba mata idanu ya na sakin murmushi
( kai wannan murmushin na shi na mugun ta ne gaskia ban yarda da shi ba 😑 )

Sai da ta cinye rabin shi , sannan ta ajiye spoon din ta dauki glass din ruwa ta sha
Da ga haka Amar ya mika mata drug ya ce ta sha , ba musu ta karba ta sha ta ajiye glass din sannan ta mike
Da sauri ya ce mata " ina kuma za ki je ? "
Kallon shi ta yi ta na fadin " gida zan komawa "
" amma dai har yanzu ruwa a ke yi , ni kuma ba zan iya barin ki tafi a haka ba gaskia ki bari har a ida ruwan "
" but........... "
Da sauri ya katse ta da cewa " ba wani , wuce ki zauna yanzu ina zuwa "

A hankali ta wurguna mishi baki kafin ta koma bakin bed ta zauna ta nade hanayan ta a kirji ta kauda kai gefe wai ita ta ji haushi da ya tseda ta
Shi kuma ta na zama ya dauke dishes din ya tashi ya fice dakin ya meda kayan kitchen

After some minutes ya dawo cikin bedroom din , amma abun mamaki ya tardo har ta yi barci , ta rufe jikin ta da bargo , sai nunfashi ta ke sauke wa a hankali

Wani kyawatencen murmushi ya saki kafin ta karaso bakin gadon ya Haye shi ma ya konta ya juya su na fuskantar juna ya zuba mata idanu
A hankali ya kai hannun shi ya daura saman kumatun ta , ya ce " You are so beautiful in ki na barci , wannan dan bakin tsiwar ba ya motsi , ni da ma san duk yan jarida dan karan dumi gare shi , amma na ki har tsiwa , mutun sai dan karan jaraba , ounn rigimamiya kawai , kin san wani ? " ya fada kamar ta na iya jin shi

Dan matso da face din shi ya yi murya kassa kassa ya ce " I love you ❤ , Do you want to marry me ? Don't say no please " ya kai karshen ya na marairaice fuska
Chapter 40 · 0% Book details