← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 66

Sashe 63

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata yar karamar dariya Fatma ta yi kafin ta karaso cikin parlourn geffen Musadeeq ta tsaya ta na fadin " ai mu saboda Doctor mu ka zo "

cikin rudu Rahaf ta ce " momy saboda Doctor kuma ? kenan ba ni ku ka zo gani ba ? " ta kai karshen cikin shagwaba 

" Puppy , Doctor ne ya tura jirgi mu ka taho da sunnan wai ya na son mu nema mishi auren babyn shi ya koma UK da ita "  Musadeeq ya fada ya na murmushi

wani kyawatencen murmushi Rahaf ta saki ta na washe baki ta na shirin magana Sahan ya riga ta cewa " Noo , Daddy da gaske Doctor auren Miss Safa zai yi ? " ya fada ya na zaro idanu

gyada mishi kai Musadeeq ya yi ba tare da ya ce komai ba
wata yar karamar Kara Rahaf ta saki kafin ta ce " ni dama na san Doctor ya na mugun son sister , duk lokacin da ya ke kallon har wani kyali idanun shi su ke "

" yanzu ke Rahaf sa idon da ki ke yi wa Doctor har ya kai haka ? " Fadin Sohan ya na matse gera 
wata yar karamar dariya Rahaf ta yi su na shirin su ka ji an turo kofar parlourn an shigo a na sallama

a tare duk su ka juya su na kallon Sami da ya shigo parlourn jikin shi duk Jini ne ga yanayin face din shi cike da tashin hankali

a rude Fatma ta ce mishi " Sannu dan saurayi " ta fada cikin sanyin murya

a hankali Sami ya karaso cikin parlourn ya karaso gaban Musadeeq ya ce " don Allah ina son ganin Familyn Assad & Amar " ya fada cikin raunin murya kamar ya yi kuka

kallon juna Musadeeq da Fatma su ka yi , fuskokin su cike da allamun tambaya
a hankali Musadeeq ya juya ya kali Sami ya ce mishi " i'm Musadeeq , ni ne mahaifin su , wani abu ne ya faru da su ? " ya tambaye shi dan zuciyar shi ta fara bugawa da karfi

a hankali Sami ya kai hannu cikin Aljihun shi ya Fido Wata paper ya mikawa Musadeeq ya na cewa " Amar ne ya ce na ba ku wannan "

a hankali Musadeeq ya kai hannu ya karbi paper din bugun zuciyar shi na kara tsananta
a hankali ya bude paper din nan ya fara karanto abun da ke ciki kamar haka " Hi Daddy , Hi momy , na san za ku tambayi kan ku abun da ya sa na rubuta muku wannan letter , na so na yi muku bankwana yadda ya dace , na yi muku ganin karshe , amma lokaci bai ishe ni ba , Momy you know you're the most beautiful woman in this word , ina son ki fiye da komai a duniya , na gode irin tarbiyar da ki ka ba ni da kulawa , Daddy , i just want to say to you that you are the best father in this world , na gode da irin soyayyar da ku ka nuna min , ban san cewa neman soyayya ta zai yi sanadiyar rabuwa ta da ku ta har abada , amma duk da haka ina farin ciki na hadu da macen da ta saye zuciya ta da murmushin ta , please momy please Daddy don Allah ko dan soyayyar da ku ke yi min ina son ku yi aure , please and please , sannan ba zan so ku raba zuciya ta da abun da ta ke so ba , buri na na karshe shi ne auren wadda zuciya ta ke so , dalilin shi ne na shigo Nigeria har na sa ku ka shigo ta kuma , yanzu kuma ina son ku nemawa Assad auren SAFA  saboda ita ce burin zuciya ta , kuma ba zan so a raba zuciya ta da abun da ta ke so wannan shi ne buri na na karshe , I love you More than my life , You , momy , Sohan , Sahan and Rahaf

Sign : AMAR MUSADEEQ "

a rude Musadeeq ya dago ya kali Sami , murya na kerma ya ce " ban gane abun da ke cikin takardar nan , where is Amar , Where is Assad ? "

nan Sami ya shiga fada musu halin da ya tardo Amar , Assad da Safa a ciki saman Hanya , da ga haka ya dauke su ya kai su likita

wata irin razananiyar kara ce Rahaf ta saki ta na sakin kuka lokaci guda ta fada jikin Sohan da ya ke shi ke kusan ta , ta rungume shi tsam
duk mutanan wajen Mutuwar tsaye su ka yi , specially Fatma

a razane ta nufi Sami ta na fadin " don Allah ina Amar di na ya ke , ba abun da ya same shi dai ko ? " ta fada ta na sakin kuka 

a hankali Sami sunkuyar da kan shi hawaye na zubo mishi ya ce " i'm sorry , he is die , ya ba wa Assad zuciyar shi , please mu je na kai ku Hospital din da na kai su "

bai gama rufe bakin shi ba ya ga Fatma ta nufi kofar fita parlourn da gudu , ta na sakin kuka , a hankali shi ma Sami ya juya ya bi bayan ta
su na fita Musadeeq ya juya ya ce ma su Sohan " ku zauna a nan , ba za mu jima ba " ya na gama fadar haka ko amsar su bai jira ba ya bi bayan Sami ya bar parlourn

ya na fita Rahaf ta sake sakin wani sabon kukan mai cin rai
da sauri Sohan ya rungume ta ya na dan bubuga bayan ta a hankali ya na cewa " don Allah ki yi hakuri ki daina kukan nan "

da sauri ta katse shi da cewa " Sohan ka na ji cewa ya yi Doctor ya mutu , shikenan yanzu ya bar mu , ba zan sake ganin shi ba ? "

a hankali shi ma Sahan ya karaso geffen Sohan ya tsaya ya dafa Shoulder din Rahaf ya na fadin " Puppy don Allah ki daina kukan nan , ko so ki ke ki saka mu kukan mu ma ? "

girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " ba zan iya ba , ba na tunanin zan iya jure rashin Doctor , don Allah in mafarki na ke ku tashe ni "

" ki yi hakuri don Allah , ki daina kukan nan " Fadin Sohan cikin raunin murya hawaye na zubo mishi
da sauri Sahan ya juya ya nufi stair da gudu ya haye 

        ▪THE ALBARKA HOSPITAL

a hankali Sami ya tura kofar dakin da a ka kontar da su Assad , ya shigo ya na sallama cen kassan makoshi , kafin ya koma gefe ya na yi wa su Fatma Bismillah

a tare su ka shigo cikin dakin su na Sallama kassa kassa
cen su ka hango Assad konce saman gado , ko riga babu a jikinshi , an yi mishi wani dress duk ya rufe kirjin shi , hannun shi kuma da catheter a na yi mishi karin jini
bayan Dress din da ke a kirjin shi , babu wani rauni a jikin shi

kallon Sami Fatma ta yi kafin ta ce " where is Amar ? "
a hankali Sami ya gauce gefe ya nuna mata dayan gadon da ke cen dayan geffen dakin , ga mutum nan konce sama , an rufe shi da wani Farin Tissu har kai

Dum ta ji gaban ta ya fadi , slowly ta daga kafa ta nufi gadon , duk taku guda sai bugun zuciyar ta ya kara tsananta
sai da ta karaso bakin gadon , ta dago hannun ta a hankali har kerma ya ke yi
ta riko Tissu din ta fara jan shi a hankali ta bude face din shi

wata irin razananiyar kara ce ta saki ta juya da sauri sai jikin Musadeeq dama ya na tsaye a bayan ta , ya na cin karo da face din Amar ya lumshe idanun shi da sauri ya karanto kalmar shahada cikin zuciyar shi

Fatma kuma wani matsanincin kuka ta saki a jikin ta na fadin " yanzu wa ya yi wa Amar di na wannan Aikin , me ya yi musu da za su raba ni da shi haka ? wane mara imani ne ya mishi wannan kisan , ko tausayi ba bu , inallillahi wa'ina illaihi raji'un "

shi dai Musadeeq ya kassa cewa komai sai hawaye ke zubo mishi bibiyu
A hankali Sami ya karaso wajen su , cikin Sanyin murya ya ce musu " ni na san wanda ya yi mishi hakan , kuma na San dalilin shi na yin hakan "

a tare Musadeeq da Fatma su ka juyo su ka kale shi
murya na kerma Musadeeq ya ce mishi " ka sani ? su wanene su ka yi mishi haka ? ka fada min don Allah ka fada min , me Amar di na ya yi musu da za su yi mishi irin wannan kisan gillan ? "

dan sunkuyar da kai Sami ya yi kafin ya ce " Ba shi su ka so kashewa ba , Safa su ka yi kokarin kashewa , kawai Amar da Assad sun yi kokarin kare ta ne , su ka yi musu wannan abun " 

" Safa ! " Musadeeq da Fatma su ka fada a tare cikin rudu 

gyada musu kai Sami ya yi ya na cewa " Eh , Safa , Wadda ku ka zo nemawa Amar auren ta , ita ce a ka kai wa hari , kalma ta karshe da ya furta shi ne ku nemawa Assad auren ta a madadin shi , ba ya so a raba zuciyar shi da abun da ta ke so , Saboda zuciyar shi ce a jikin Assad "

" Ina ta ke ita Safar , ba abun da ya same ta ? " Musadeeq ya tambaye shi 
Chapter 63 · 0% Book details