← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 66

Sashe 33

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yar karamar dariya Fares ya yi kafin ya ce " kar fa ka manta Nigeria ta na daya da ga cikin colony din US kuma US da RUSSIA babu jituwa a tsakanin su , ka san in a ka san wanene Assad ba karamar cakwakiya za a sha ba , ga shi kuma Nigeria temperature din su ta kai wajen 30 to 40 degree Celsius al'halin a RUSSIA temperature din su ba ta wuce 10 degree ba wani lokaci har negatif ce , ka na tunanin zai iya supporting ? "

" ni na ke supporting ? , inda ba zai iya ba , ba zai zo ba " Amar ya fada dai'dai lokacin da server ya dawo rike da tray dauke da bowl biyu na ice cream Ya ajiye daya gaban Safa dayan kuma gaban Amar kafin ya juya ya bar musu wajen

" okay haka dai ka ce ! Yanzu fada min ka samo abun da ka je nema " Fares ya tambaye shi ya na daga gera guda kamar ya na gaban shi

Satar kallon Safa Amar ya yi , ya ga hankalin ta na kan wayar ta sannan ya ce " eh na samo "

Cike da zumudi Fares ya ce " da gaske don Allah ta na ina , ya take , kun yi magana da ita "

Yanzu ma sai da ya kara satar kallon Safa , cikin Russian language ya ce mishi " Duk yadda ka ke tunani ta wuce haka nan , She is so beautiful and very cute , wani ikon Allah gidan da mu ka sauka ya na fuskantar na su , yanzu haka mu na tare , mun fito shan ice cream " ya na gama fadar haka ya ga Safa ta saki wani cool murmushi na dan second ta na ci gaba da latsa wayar ta

" Doctor ka ce min har ta shigo hannu , ka yi kokari ka dawo UK da ita tun wani bai kwace maka ita ba , tsaya ma , ka fada mata ka na son ta ? "

Shiru Amar ya yi na dan lokaci kafin ya ce " no ban fada mata ba "

Dan tsaki Fares ya yi kafin ya ce " Matsala ta da kai kenan , you are very Shy , I love you din ne ka kassa fada ma ta "

" i don't like that ka sani ko , ko a tunanin fadin hakan is so easy ? So ka ke na ce ma ta ina son ki , kuma tun ba yau ba na kamu da son ki , tun lokacin da ki ka fara posting videos din ki saman social media , accidently na fara kallon su har na ji na kamu da son ki , ko zuwa Nigeria kawai dan na gan ki ne , kai a tunanin ka za ta yarda "

" Allah ya sa ta na jin Russian , ta ji duk abun da ka fada min yanzu na ga yadda za ka yi " ya kai karshen ya na bushe wa da dariya

Dan tsaki Amar ya yi kafin ya ce " sai an jima ka fara damu na " ya na gama fadar haka ya sauko wayar shi ya katse kiran ba tare da ya jira amsar Fares ba

Ajiyar wayar saman table din ya yi kafin ya kali Safa ya ce " i'm sorry na kyale ki , wlh wani aboki na ne ya kira ya ji ko mun sauka lafya "

" Uhmmm " kawai ta fada mishi ba tare da ta janye idanun ta da ga saman wayar ta ba

Shiru shi ma ya yi ya tsaya ya na kallon ta , bai taba ice cream din shi ba har sai da ta gama sannan ya tura mata ta shi gaban ta ya na fadin " kara da wannan "

Kallon shi ta yi kafin ta ce " ba za ka sha ba ne "

Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no ba na sha sugar sosai "

" okay ! " ta fada a takaice ta na kara janyo bowl din gaban ta , ta fara sha ta ci gaba da latsa wayar ta

Shi kuma Amar ya koma ya jingina a bayan chair din ya nade hanayan shi a kirji ya zuba mata wadanan Ash eyes din na shi babu ko kiftawa

Ta na tsaka da shan ice cream din ta debo spoon za ta kai wa a baki , wannan dan siririn gashin da ta zubo a geffen fuskar ta , ya fito da ga baya kunnen ta ya nemi fadawa cikin ice cream din

Da ido ta kali gashin , ta na shirin ajiye wayar ta , ta ji hannun Amar ya janye ya meda mata shi bayan kunne

A dubu dari ta dago kai za ta kale shi , ai idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi dan shi ma ita ya ke kallo , sai su ka yi ido hudu

Nan take ta ji ta tsargu da kallon cikin idanun shi , duk sai ta ji ta kassa janye na ta idanun

Wani cool murmushi ya sakin mata , cikin wata zazzakar murya mai mugun dadi da ba ta taba jin yayi magana da ita ba ya ce " ya dai lafya ki na yi min irin wannan kallon kar ki cinye ni " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda

Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta yi sauri ta sunkuyar da kan ta , ta meda idanun ta kan wayar ta
Babu shiri ta ji saukar lalawsan lips din shi saman forehead din ta ya yi mata kiss

Nan take ta dauke lokaci guda ta kassa motsi
Sai da ya koma saman chair din shi ya zauna sannan slowly ta dan dago da kan ta ta kale shi
[09/09 à 19:59] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🕊

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 : FREE BOOK

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ : PAID BOOK

DOMIN SAMUN WANNAN LITTAFIN DA GA FARKO ZA KU IYA JOING CHANEL DI NA ON WHATSAPP

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

ZA KU IYA SAMUN WANNAN PAGE A WATTPAD TA HANYAR WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇👇

https://www.wattpad.com/1475621232?utm_medium=whatsapp&utm_source=android&utm_content=share_published

【CUTIE PIE】

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 18 🥀 ❤

Sai da ya koma saman chair din shi ya zauna sannan slowly ta dan dago da kan ta ta kale sh
Shi kuma ya kauda kai gefe , ya nade hanayan shi a kirji dan ba ya son ya kale ta saboda ya san shi ta ke kallo a yanzu

Sai da ta dauki wajen five minutes ta na kallon shi babu ko kiftawa kafin ta meda kallon ta kan wayar ta , ta ci gaba da shan ice cream din

Kamar ko ya san ta janye idanun ta , sai ya dawo da kallon shi gare ta a hankali ya na murmushi

Ko da ta Kamala shan ice cream din ta sai da su ka dan dauki lokaci a ciki restaurant su na hira
Sai wajen karfe 11 sannan su ka baro restaurant din , nan ma ba gida ya kai ta kai tsaye ba , gidan su ya fara zuwa nan ma su ka zauna su ka dan yi hira , sai da ta fara jin kiran sallat sannan ta tashi ta tafi gidan su

* ABUJA ( GIDAN SU TWINKLE )

zaune Raïssa ta ke cikin parlourn su ta na kallon Tv , allamun yau ba ta je university ba
Ta na a haka Farida ta shiga parlourn babu ko sallama ta nufi Sofa ta zauna ta na ta huci allamun an bata ma ta rai

Kare mata kallo da kyau Raïssa ta yi ta na shirin magana Noor ta fara sauko stair , ta na tafe ta na latsa wayar ta ta na rera wakar Sare ta Ayra starr
Ba ta bi ta kan su ba ta nufi Sofa one seater ta zauna
Sai da ta zauna sannan ta dago kan ta , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai saman Farida

Tabe dan bakin nan nata ta yi kafin ta ce " O'O Aunty Farida lafya ki ke ta bata rai ke daya ? "

Kallon sama da kassa Farida ta yi mata kafin ta ja tsaki ta na kauda kai gefe

" Tooooo , Ni da na tambaye ki ma , no sens kawai " Noor ta fada ta na dan tsaki kafin ta meda music din ta dama earpiece ne ta ke sanye da

Hararrar ta Farida ta yi kafin ta ce " Wlh Noor ki fita da ga ido na "

Aikin banza kenan ke kadai ke ta zubar ki dan Noor sam ba ta jin ki ta yi nisa duniyar ta

" Wai me ya ke damun ki kin shigo babu ko sallama " Raïssa ta fada ta na kallon Farida

Dawo da kallon ta kan Raïssa ta yi kafin ta ce " wata yar iska ce ta kai karar boyfriend di na kotu wai ya mata ciki ya zubar mata da shi ba tare da sanin ta ba , yanzu haka maganar da na ke yi miki ya na police station sun like shi next week za su wuce da shi kotu "

Dariya sosai Raïssa ta yi , har da dafe ciki
Sai da ta gama dariyar ta da kyau kafin ta tsagaita ta na fadin " to miye na ki a ciki , tun da su ka kama shi , ai su na da kwakwarar huja ta yin hakan , dan haka ki godewa Allah da ya raba ki da shi tun yanzu kafin a je nesa "

Tsaki Farida ta yi kafin ta mike ta Haye stair da sauri
Ta na hawa Noor da Raïssa su ka bushe da dariya a tare , dama Noor ta na sauraron duk abun da ta fada kawai dai ta yi kamar ta na sauraron music ne dan kar ta dame ta
Chapter 33 · 0% Book details