← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 66

Sashe 30

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi nisa cikin tunanin ta ya jiyo Muryar Safa ta na fadin " Djami tunanin mi ki ke yi haka tun dazu ina yi miki magana "

A razane ta dawo cikin hayacin ta na fadin " no ! no ! ba komai "

Kare mata kallo da kyau Safa ta yi
Cikin sanyi ta riko hannun Djamila ta saki wani cool murmushi ta ce " okay , ki rage yawwan tunani kin ji , ga exams nan sun gaba to ya kamata ki maida hankali kan karatun ki "

Dan karamin murmushi Djamila ta yi ta na gyada ma Safa kai
Sakin hannun ta Safa ta yi ta na shirin magana kamar da ga sama ta jiyo Muryar Amar ya na fadin " ke ki na meda hankalin ki ne kan karatun ? "

Dum ta ji gaban ta ya fadi , a dubu dari ta mike tsaye ta juya ta na kallon shi
Ya na tsaye bayan ta , ya na sanye cikin trouser white colour , da t-shirt navy blue , ya saka wata face mask baki sai tashin kamshi yake yi

Cike da rudu Safa ta nufe shi ta na fadin " Amar what are you doing here ? " ta fada kamar mai rada dan kar sauran students su jiyo ta
Ita ba ta san tun shigowar Amar cikin library din ba su ka tsare shi da ido ko wane ya na kara yabawa kyawan qui duk da ya na sanye da face mask

A hankali ya dan sunkuyo da kan shi ya matso da face din shi saitin ta ta kassa kassa ya ce mata " kawai na zo ne na yi miki barka da safya , na je gida na ga baki nan "

Da sauri Safa ta yi baya , ta ce mishi " okay ! Okay ! Please ka bar wajen nan , mutane su na kallon mu "

Slowly ya dago kai ya gyara tsayuwar shi ya fara bin libraryn da kallo
Dan karamin murmushi ya saki kafin ya karaso wajen table din su Safa , ya zauna saman chair din da ta tashi ya kali su Haoua ya ce " Hi ! Sannun ku "
Murmushi mai dan sauti Haoua ta yi kafin ta ce " yawwa sannu ka kai ma "

Sai da ya bari ta karasa maganar ta sannan ya ce " sorry ba na jin haoussa "

A hankali ya juyo ya kali Safa da ke tsaye bayan shi ya ce mata " Miss Safa , ko za ki koya min ? "

Iska mai zafi ta furza da ga bakin ta ta ce " please Doctor , ka koma gida , wlh za ka janyo min kananan magaganu "

Daga mata gera guda ya yi kafin ya ce " okay , amma kin koya min ko "

Da sauri ta ce " ba haoussa ba har chinese in ka na so zan koya maka "

Gyada kan shi ya yi kafin ya mike ya fara takawa ya nufe ta , a hankali ya sunkuye da kan shi ya kai dan bakin shi saitin kunen ta ya ce " no haoussar ma kadai ta isa " ya fada mata cikin harshen chinese
Ya na gama fadar haka ko ya mike ya ci gaba da tafiyar shi
Da sauri Safa ta juya ta na kallon shi , ta na son ta yi mishi magana amma ba hali , har sai da ya fita sannan ta juya ta koma saman chair din ta ta zauna

Ta na zama , Haoua da Djamila su ka Bushe da dariya har da tapi
Hararrar su Safa ta yi ta na fadin " lafya ku ke dariya haka "
Girgiza kai su ka yi a tare sannan Haoua ta ce " Haba ba banza ki ka ki kula duk samarin makarantar nan , ashe Doctor ya na gida ajiye " ta kai karshen su na sake bushewa da dariya

Tsaki Safa ta yi sannan ta fara tatare books din ta ta meda cikin bag din ta , ta dauka ta mike ta bar musu wajen
" ki gaishe ma na shi in kin je " Haoua ta fada dan sama sama ta na yar dariya

Bangaran Safa kuma ta na barin library kai tsaye class ta koma dan ta ci gaba da karatun ta , ta na shiga Class din ta ga ba kowa
Sai ta nufi chair din ta ta zauna ta fido books din ta ta ci gaba da karatun ta , amma har ga Allah gangar jikin ta ne kawai ke a wajen , tunanin ta ya tafi wani waje kawai sai tsintar kan ta ta yi ta na sakin wani cool murmushi allamun tunanin da ta ke yi ya yi mata dadi har mai lectures din su ya shigo ba ta da labari

* AFTER SOME HOURS

Bayan sun Kamala lectures din su misalin karfe 1 na yamma , kai tsaye Safa gida ta wuce
Bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn su , ta nufi stair kai tsaye dan ta san a wannan lokacin momy ba ta dawo ba
Kamar da ga sama ta ji an amsa mata sallamar ta
Cak ta tsaya da sauri ta kai kallon ta cikin parlourn
Nan ta ga Amar konce saman sofa, ga Snoopy konce kassa shi ma

Da lumshe idanun ta ta yi ta daga kai sama , ba ta ce mishi komai ba ta wuce ta Haye stair
Ta na hawa Amar ya kali Snoopy ya ce " Aboki na , ina ga yau ran mamar ka ya baci "
Dan karamin haushi Snoopy ya yi ba tare da ya dago kan shi ba
Juya kan shi Amar ya yi ya kali ceiling sannan ya ce " ni ma haka na gani "
Sai da ya dauki wajen five minutes kafin ya sake cewa " za ka iya tafiya wajen Rex in ka gaji da zama kai kadai "
Kamar jira ya ke yi ko ya tashi da sauri ya fice parlourn
Ya na fita Amar shi ma ya tashi ya fice parlourn cikin nitsuwa ya bi bayan Snoopy su ka tafi gidan su

Bangaran Safa kuma ko da ta shiga bedroom din ta , kai tsaye toilet ta wuce ta yi wanka
Jim kadan ta fito sanye da bathrobe , ba ta tsaya bata lokaci ta Haye saman bed din ta , ta yi rub da ciki ba jimawa barci ya yi gaba da ita dama a gajiye ta ke

Ba ta farka da ga barcin ta ba sai da wayar ta ta fara karar kiran Sallat
A hankali ta kokarin bude idanun ta , ta na karanto adu'ar tashi da ga barci
Ko da ta bude idanun ta ma sai da ta dauki wajen good ten minutes a haka kafin ta mike a hankali zaune ta na karewa dakin kallo kamar bakon ta

Saukowa da ga saman bed din ta yi ta nufi toilet ta yi wani wankan , ta dauro da Alwalla sannan ta fito ta shiga dressing room
Jim kadan ta fito sanye da wani skert pink colour har kassa , da wata Shirt fara , da wani veil white colour ta yi Rowling din shi a kai sai tashin kamshi ta ke yi

Ko da ta fito ta nufi daddumar ta , ta Haye sannan ta tada sallar ta , cikin nitsuwa ta yi kayan ta , ta zauna karatun adu'a sannan ta tashi ta dauki wayar ta , ta fito dakin a haka

Kai tsaye parlourn kassa ta sauko , ta yi zaton za ta tardo Amar sai ta ga ba kowa a cikin parlourn
Ba ta kawo komai a ran ta ba ta nufi sofa ta zauna , ta na faman latsa wayar ta
Bai fi five minutes da zaman ta ba , ta ga an turo mata pic ta WhatsApp da wata number ta Nigeria
Babu tsoro ta shiga discution din ta fara download din pic din
Wani kyawatencen murmushi ta saki lokacin da idanun ta su ka yi mata arba da pic din
Amar ne konce saman bed din shi ga Snoopy da Rex konce saman kirjin shi abun ba karamin burge ta ya yi ba
A hankali ta mike tsaye ta nufi door din fita parlourn ta fito harabar gidan
Tun da gate man ya gan ta ya yi sauri ya tashi da ga saman chair din shi ya bude mata kofar fita
Godiya ta yi mishi ta na dan murmushi kafin ta sa kafa ta fice gidan baki daya

Kai tsaye gidan su Amar ta nufa , har yanzu dai wadanan jibga jibgan sojoji su na nan tsatsaye kamar ba su gajiya

Ba ta bi ta kan su ba ta nufi door din shi gidan , tun kafin ta karaso sojan da ke kula da gate din ya bude mata , dan murmushi ta yi ta na yi mishi godiya kafin ta shiga gidan ta na sallama kassa kassa

A hankali ta ke tafiyar ta har ta karaso wajen dan balconyn da zai sada ka da parlour
Hannu ta kai ta dan bubuga door din kafin ta tura ta a hankali ta shiga ta na sallama

* ASSAD 🔥

Zaune ya ke cikin parlourn shi kadai ya na faman latsa laptop din shi , da ga shi sai short da singlet duka farare kal kamar sabi , ya saka wasu glass bakake

Slowly ya dago kan shi ya kale ta ya na amsa mata sallamar ta , amsawar da shi kadai ya ji abun shi

Karasowa ta yi cikin parlourn ta na gaishe da shi , amma ina sam ba ya jin ta , ya yi nisa cikin duniyar shi duk sai ya ji ya kassa janye idanun shi da ga saman ta dan fa ba karya kayan nan sun yi mata mugun kyau ,

A hankali ta karaso gaban shi ta dan sunkuyo da kan ta, ta na lekon face din shi ta ce " Hello ! here the earth is there anyone ? "
Chapter 30 · 0% Book details