← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 66

Sashe 56

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

" ai shi ka ce , ni duba na ma tafi na yi barci na , sai da safe " ta fada ta na kokarin tashi
da sauri ya riko hannun ta ya na cewa " ina za ki je ba ki gama da ni ba ? "

" please ka kyale ni mana , at least ka bari na yi wanka mana " ta fada cikin shagwaba
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya mike tsaye ya na rike da hannun ta ya ce shikenan " Tashi mu je na yi miki "

marairaice fuska ta yi ta na cewa " babyyyyyyyy " ta fada ta na marairaice fuska
sakin hannun ta ya yi ya nufi daya da ga cikin bedroom din wajen ba tare da ya ce mata komai ba 

ta na kallon shi har sai da ya shiga sannan ta saki wani cool murmushi ta mike ta bi bayan shi

            ▪UNGUWAR MAITAMA 💔

wasu lattijawa guda hudu zaune cikin wani kyawatencen parlour , ko wane sanye da manyan Kaya na shadda

cen Daya da ga cikin su ya ce " Tun wuri ya kamata mu kai Abdoul Karim prison , Idan mu ka bar shi a fili haka wlh shi zai kai mu prison "

ya na gama fadar haka Wani Dattijon ya fara sauko stair , kamanin daya tak da His excellency , sai dai His excellency ya fi shi haske wannan kuma zai fi shi shekaru da ga gani

sai da ya karaso cikin parlourn ya zauna kusan dattijon nan da ya yi magana da ga farko ya ce " Habib ka kontar da hankalin ka , wannan karan na gina wa Abdoul Karim Ramin da ba zai iya ketarewa ba , Kafin kotu ta gano shaidun da mu ka gabatar ba na gaskiya ba ne mun riga da mun binne shi cikin kassa "

cen kuma daya ya ce " yanzu Ali ya za mu yi , sai fa Next week za mu koma kotu "

wata shegiyar Dariya wanda ya kira da Ali ya yi kafin ya ce " cikin daren nan Abdoul Karim zai tafi prison , Tare da duk ahalin shi , ku jira ku gani , Adamu , Major , Habib Minister , ku saurare ni da kyau abun da zan fada muku , kar a samu cikass a cikin plan din nan "

a tare duk su ka hada baki su na cewa " mu na sauraron ka fadi kawai "

wani makirin murmushi Ali ya saki kafin ya matso bakin sofar shi ya fara yi musu wata magana , 😑😑😑 maganar da ban ji ba ma

sai da ya Kamala maganar shi na ga sun saki wani shu'umin murmushi a tare
cen kuma wanda ya kira da Major ya ce " Wait ! Ali yanzu Batun First lady kuma fa ? da yarinyar shi wannan Puppy ? "

a hankali Ali ya koma Jikin sofar ya jingina bayan shi ya daura kafa daya bisa daya ya ce " kar ku damu da wannan , Na san abun da zan yi da su , ku dai kawai ku yi abun da na fada muku , sannan mu fara shirye²n yadda za mu yi Minister ya hau kujerar President " ya kai karshen ya sakin wani makirin murmushin geffen fuska 
cikin zuciyar shi kuma ya na cewa " da kuma yadda zan yi dukiyar Abdoul Karim ta dawo hannu na "

su na a haka kawai su ka ga an turo kofar parlourn wata mata ta shigo ta na sallama
ta na sanye da wata Abaya darck green , ta yi Rowling veil din abayar , ta so ta dan yi kama da Ali , a shekaru za ta kai 25 zuwa 30 haka , Fuskar ta babu yabo babu fallasa 

a hankali ta karaso cikin parlourn ta na fadin " barkan ku da wannan lokacin "

da fara'a a fuskokin su su ka amsa mata su na yi mata sannu da zuwa kafin su mike a tare su na ce ma Ali sai sun hadu an jima su na da aikin yi

ba musu Ali ya tashi ya raka su su ka fita a tare su na tafe ya na kara jadada Musu a kan su bi tsarin plan din su

su na fita matar nan ta nufi Sofar da Ali ya tasso ya zauna

ta kai 5 minutes a haka kafin Ali ya dawo cikin parlourn ya na sallama
a hankali ta dago kai ta ta na amsa mishi sallamar shi cen kassan makoshi
bai ce mata komai ba ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofar da ke fuskantar ta ta
irin zaman nan na kasaita , ya daura kafa daya bisa daya ya na kallon ta

cen sai ta ce mishi " na ji maganar da ku ka yi "
" yanzu Aziza labe ki ka fara yi min ? " ya tambaye ta cikin tsare gida

girgiza mishi kai ta yi ta na cewa " ni ban yi maka labe ba , ni kuma ba wannan ya kawo ki wajen ka ba "

" minene fada ina sauraron ki "

cikin sanyin murya ta ce mishi " ina son na tafi UK da Safa , dan haka ku cire ta da ga cikin plan din ku "

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " da ga cikin plan din mu , kar ki manta ke ki kawo wannan shawarar , dalilin da ya sa ma ki ka matsawa Marwan ku dawo Nigeria "

marairaice fuska ta yi ta na cewa " na sani , amma please ku cire Safa a ciki , ka fi kowa sanin dalilin da ya sa na ce mu shirya mishi hakan ba dan ba na son dan uwa na ba , tun lokacin da Safa ta shigo duniya ba kwalafa rai a kan ta , amma ya hana min ita , ina son ta dinga kira na da momy ni ma , ban damu a kan Marwan ba , amma ban da Safa please "

shiru Ali ya yi ya na kallon babu ko kiftawa sai marairaice mishi fuska ta ke
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " okay , tun yanzu ki je ki dauke ta ku bar Nigeria Tun yanzu ki koma UK da zama da ita , yadda kowa zai yi tunanin familyn Abdoul karim sun mutu baki daya , sannan duk ranar da na gan ta cikin garin nan wlh wlh kin ji na rantse ba zan kyale ta ba "

wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " na gode , batun Twinkle kuma fa ? "

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " Auren ta zan yi "

dan zaro idanu Aziza ta yi ta na cewa " What ? aure kuma ? ka na tunanin His excellency zai yarda ya sake ta , kai ka aure ta ? "

" ai ba dole ba sai ya yarda , kawai sa hannun shi na ke bukata da ga nan duk wani abu da ya mallaka har First lady za su dawo mallaki na "

" To ita za ta yarda ta aure ka ne ? "

" eh za ta yarda , dan ta ceci rayuwar mijin ta , da ta yaron ta "
[21/09 à 11:39] MEERAH 🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
                        ( YAR JARIDA )

🌸💖 ( A heart touching love story & destiny ) 💖🌸

STORY & WRITTEN BY : MEERAH  👑🌸

【THE ROYALTY LOVE 🕊🌸💕】

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 :FREE BOOK

❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤ : PAID BOOK

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP POSTING ROOM

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/BBWVomizhgVKzcxJo4XRpG

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

DON'T FORGET TO FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT
WATTPAD : @bennybite

               BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

___________________________________________

LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN

GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE ⚘❤
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
👇👇👇👇
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
👇👇👇👇👇
Zain (Airtel)
08081129487 

sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753

     ___________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊____________________

{PAGE 28 🥂✍}

cikin Rudu Aziza ta ce mishi " Ali me ka shirya musu ?  "
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " kin ga malama tashi ki fice min gida , ba na bukatar ki a yanzu , Idan kuma ki ka bari ba ki je kin dauke Safa ba nan da Two hours wlh duk abun da ya same ta kar ki ce ban fada miki ba " ta fada cike da isa

shiru Aziza ta yi ta na kallon shi ya na dariyar shi , ba tare da ta ce mishi komai ba ta mike ta nufi Hanyar fita parlourn ta fice abun ta , ta bar shi nan zaune shi kadai ya na faman sakin murmushi da ga gani na mugun ta

ta na fita wani dan saurayi ya fara tako stair , a shekaru ba zai wuce 16 years ba , ya na sanye da wani jeans brown da Shirt white color ya na tafe ya na latsa wayar shi 

bai bi ta kan Ali da ke zaune ba ya wuce ya nufi hanyar fita
har ya kai bakin kofa ya jiyo Muryar Ali ya na cewa " kai Sami ina za ka je ? "

ba tare da ya juyo ba ya ce " zan je wajen Marwan , yanzu ya yi min text ya ce min ya dawo "

" Dawo ina da magana da kai " Ali ya fada cikin bada umarni

wata yar karamar ajiyar zuciya Sami ya sauke kafin ya juya a hankali ya dawo cikin parlourn ya zauna ya na ci gaba da latsa wayar shi

" Ba na son ka koma UK , a nan za ka ci gaba da karatun ka "
Chapter 56 · 0% Book details