← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 66

Sashe 55

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

LITTAFIN EXILED PRINCE PAID NE A KAN NAIRA 200 ZA KU IYA SHIGA PAID GROUP DIN

GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ❤⚘EXILED PRINCE ⚘❤
ZAI IYA TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT
👇👇👇👇
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

IDAN KUMA KATI NE TA WANNAN NUMBER
👇👇👇👇👇
Zain (Airtel)
08081129487 

sai ku turo shaidar biyan ta wannan number
+22795577612 ko kuma wannan +22798999753

     ___________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊____________________

            {   PAGE 27 🥀 ❤ }

a hankali Marwan ya juyo ya kali Safa ya ce " mu je ki ga surprise din ki ? "

da sauri ta Haye saman bayan shi ta na fadin " yeah , yeah , mu je na gani , I hope chocolate ne dayawa "

yar karamar dariya ya yi ya na mikewa tsaye da ita a bayan shi ya ce " sannu ke uwar son chocolate , to ba chocolate ba ne , Idan mun je za ki gani "

ba ta ce mishi komai ba har su ka baro part din , su ka sauko stair , kai tsaye ya nufi hanyar fita parlourn ya fice tare da Safa a bayan shi

kai tsaye Hanyar parking Space su ka na nufa , duk inda ya wuce da sojoji sai sun sara mishi su na yi mishi barka da dawowa , da fara'a a fuskar shi ya ke amsa musu ya na yi musu godiya

kai tsaye wata dankareriar mota black color mai mugun kyau ya nufa
su na isa wajen ta ya sauke Safa ya ce mata " Close your eyes "
ba musu ta sa hannayan ta ta rufe fuskar ta ta na sakin wani kyawatencen murmushi 

wani cool murmushi ya saki kafin ya bude Gidan bayan motar , sannan ya juyo ya dauki Safa ya shigar da ita cikin motar ya zaunar da ita sannan ya ce " open your eyes "

a hankali ta bude idanun ta , sai ta ga cikin mota su ke , da sauri ta juyo ta kali Marwan ta na marairaice fuska ta ce " Aryan where is the surprise ? "

" juya ki gani " ya fada ya na nuna mata dayan geffen ta da yatsa 

a hankali ta juya ta kali dayan geffen
wata yar siririyar kara ta saki ta na kallon wani dan baby dog din da ya ke konce a wajen ya dunkule waje guda abun burgewa

da sauri ta kai hannu ta dauke shi ta daura saman cinyar ta , ta juya ta kali Marwan ta ce " Aryan na wanene ? " 

wani cool murmushi Marwan ya saki kafin ya ce " our surprise , ta yi miki ? "

" na gode sosai My Aryan , Dubi he is so cute " A hankali ta dago Dog din ta na fadin " Hi baby , What's your name ? "

wani dan karamin kuka karen nan ya yi ya fido tongue din shi ya na lashe mata kumatu
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta juya ta kali Marwan ta ce " Aryan ba ka saka mishi suna ba ? "

" Ummmm ban saka mishi ba , wane ki ke so a saka mishi ? "

" Snoopy ! " ta fada ta na sakin wani kyawatencen murmushi ta juya ta kali dog din ya yi mata wani dan karamin haushi

murmushi mai dan sauti Marwan ya yi ya na dan sunkuyar da kai ya daura hannu saman Snoopy ya na cewa " Hi Snoopy , barka da shigowa Familyn mu "

da sauri Safa ta fito da ga cikin motar ta na rike da Snoopy sai da ta yi gaba kadan sannan ta sauke Snoopy kassa ta yi gaba ta na fadin " let's go ! " ta kai karshen ta na fara yin gudu 
da sauri shi ma Snoopy ya bi bayan ta , ya na haushi , haka su ka shiga zagayen garden din ta na gudu ta na dariya

wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya juya ya nufi hanyar komawa cikin gidan ya bar Safa tare da Snoopy su na wassa cikin garden , duk sojojin wajen su na kallon ta su na dan karamin murmushi

bangaran Marwan kuma kai tsaye cikin gidan ya koma
da sallama cen kassan makoshi a bakin shi ya shigo parlourn gidan
kai tsaye Stair ya nufa , har ya kai tsakiyar stair ya jiyo Muryar His excellency da Twinkle a kassan stair din

a hankali ya juyo ya sauko stair din ya nufi dan corridor din da ke kassan Stair din ya shiga Parlourn ya na sallama kassa kassa 
nan ya tardo His excellency da Twinkle zaune saman doguwar sofa , ga yanayin face din su duk a tirje da ga gani su na cikin tashin hankali

cikin nuna damuwa ya ce " Daddy , me ya faru ne ? " ta fada ya na karasowa cikin parlourn ya zauna saman sofa two seaters

cikin sanyin murya His excellency ya ce mishi " Marwan , why za ka dawo ? sai da na ce maka ka bari har mu warware wannan case din ..... "

cikin nitsuwa Marwan ya katse shi da cewa " Daddy wai me su ke jira ba su Kamala da wannan case din ba ? "

" Marwan please cikin daren nan ina son ka koma Moscow , na kira antyn ka ta ce ta na zuwa Karfe 8 na dare " Twinkle ta fada cikin sanyin murya

cikin bacin rai Marwan ya ce " No Dad ! babu inda zan je har sai an Kamala case din , how ? ta ya za su yi maka irin wannan kazafin , kowa ya sani ka na da company dayawa a cikin Nigeria , Har ma wajen Africa baki daya , ta ya za su yi tunanin kudin gomnati ka ke sata , bai kamata mu yi shiru mu sa mu ido su na bara maka suna haka ! "

" Marwan ba shawara na ke ba ka ba , Umarni na ke ba ka a matsayin mahaifin ka , ka bar kassar nan har su Kamala binciken su , ba na son wani abu ya same ku kai da Safa , shi ya sa ma na cewa Aziza ta koma Moscow tare da ita , har kura ta lafa " His excellency ya fada cikin sanyin murya 

" Daddy what about you ? " Marwan ya fada ya na marairaice fuska 

wani dan karamin murmushi His excellency ya saki kafin ya juya ya kali Twinkle ya riko hannun ta ya kai saitin bakin shi ya manna mata kiss ya ce " Idan ina tare da ita ba abun da zai faru da ni "

Wani cool murmushi Marwan ya saki kafin ya ce " okay , na gane haka abun ya ke kenan ?  shikenan zan koma Moscow amma next time da zan dawo tare da matata zan dawo "

dan tabe baki Twinkle ta yi kafin ta ce " Sannu fa , kai a shekarun nan naka wa zai ba shi yarinyar shi ? "

da sauri ya ce mata " Uncle Musadeeq mana "
ya na gama rufe bakin shi His excellency ya ce " Uncle Musadeeq ? shi ya ce ya baka yarinyar shi ne ? "

gyada mishi kai Marwan ya yi ya na cewa " Yeah , shi da kan shi ya yi min alkawari "

" Marwan ka na nufin ya ba ka auren yarinyar shi ? " Twinkle ta tambaye shi ta na dan zaro idanu

wata yar karamar dariya Marwan ya yi kafin ya ce " momy da gaske na ke fa , ya ba ni auren Rahaf , saboda haka ku fara shirye² , nan da shekaru kadan ni ma zan yi aure " 

wata yar karamar His excellency ya yi ya na cewa " Eh gaskiya sannu yaro , gaskiya sai na kiri Uncle Musadeeq na ce mishi ya sake nazari a kan shawarar shi "

mikewa tsaye Marwan ya yi ya na fadin " kun ga ni na ma tafi na shirya kayana na koma wajen masoyiya ta , byeeeeee " ya kai karshen ya na fara takawa ya bar wajen 

da kallo su ka raka shi har sai da ya fice sannan his excellency ya juyo ya kali Twinkle ya ce " yaron ki fa ya fara girma , har ya fara zancen aure ? "

hararrar wassa Twinkle ta yi mishi ta na cewa " Yaro na ko yaron ka , ba duk kai ne ka koya mishi ba " ta kai karshen ta na kauda kai

wata yar karamar dariya His excellency ya yi kafin ya zagayo da hannun shi a kugun ta , ya janyo ta jikin shi ya na cewa " tsaya , wai ya na ji har yanzu shiru , ko ba ki shirya ba ni wani babyn ba ? "

tsuke fuska ta yi ta na cewa " Ni ka kyale ni , ba wani baby , Safa da Marwan sun ishe ka " ta kai karshen ta na kauda kai

kara matso ta jikin shi ya yi ya na cewa " please my baby , ina son mu samu wani babyn , ya kamata mu yi wa Safa little sister or brother , idan ya so da ga shi ba kari please my Twinkle "

Hararrar wassa ta yi mishi ta na murmushi ta ce " Dear ka bari na dan huta mana ? " ta kai karshen ta na turo baki kamar wata yarinya

" Wane hutu kuma baby ? Dubi lokacin da mu ka haifi Marwan sai da ya yi shekara goma kafin ki yarda mu samu wani babyn "

" And ? yanzu ma ka bari har Safa ta kai shekara goma ita ma "

" so ki ke sai na tsufa da yara biyu kadai , dubi Ali yanzu fa yaran shi biyar fa , kuma duk auren shi da shekara guda ya wuce namu "
Chapter 55 · 0% Book details