← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 66

Sashe 11

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Haoua, Djamila fa ta na mutuwar son Mansour so ko kin fada mata ba yarda za ta yi ba amma , zan fada miki abun da za mu yi magriba ta gabato zan koma gida "

" okay sai mun yi waya " ta kai karshen su na rungumar juna kafin ta sauko da ga motar ta shiga gidan su , Safa kuma ta tada motar ta ta bar wajen da gudu

Cikin kankanin lokaci ta isa gida , ba ta tsaya batta lokaci ba ta wuce kai tsaye bedroom din , ta yi wanka , ta yi Alwalla , sannan ta fito ta shirya cikin Abaya baka ta yi Rowling veil din ta sannan ta nufi sallayar ta ta yi sallat
Bayan ta Kamala sallar ta , ta zauna ta na karatun Alkur'ani , har sai da a ka yi kiran sallar isha sannan ta tashi ta yi sallar

Bayan ta Kamala sallat ta tashi da ga saman sallayar , ta koma cikin dressing room
Jim kadan ta fito sanye da kananan kaya pink colour , wando ya tsaya a iya cinya da riga ta dan wuce cibiya mai shilalen hannu

Parlourn din kassa ta sauko kai tsaye , ta na tafe ta na latsa wayar ta , har sai da ta iso wajen doguwar sofa ta zauna

Ta na zama ta ajiye wayar shi geffen ta sannan ta shiga kwallawa Balki kira

Da sauri Balki ta fito da ga cikin kitchen din ta karaso gaban ta ta tsaya ta na fadin " ga ni madam , ki na bukatar wani abu "

Kallon ta Safa ta yi ta na fadin " Dauko min notebook da paper , zan rubuta miki wasu ingredients , gobe ina son ki je market ki sayo min su "

Da to Balki ta amsa mata kafin ta juya ta nufi closet din kassan Tv ta bude wani locker ta fido notebook da pen , ta karaso ta bawa Safa

Karba ta yi ta fara yin rubutu sannan ta mikawa Balki ta ce " kar ki batar da paper din nan kin ji ko "

Da to Balki ta amsa mata kafin ta dauki notebook din ta meda wajen shi sannan ita ta koma kitchen

Ta na shirin daukar wayar ta , ta jiyo sallamar momy
Juyowa ta yi ta kali momy ta na amsa mata sallamar ta kafin ta kauda kan ta ta dauki wayar ta ta gyara ta konta saman sofar

Sofar da ke geffen ta momy ta zauna ta na fadin " kin dauki card din ki , kar na manta yanzu ma "

Shiru Safa ta yi ta na ci gaba da latsa wayar
Murmushi momy ta yi kafin ta kai hannu ta shafi kan ta ta na fadin " na ji yi hakuri wlh mantawa na yi "

" uhmm " ta fada a takaice ba tare da ta kale ta ba
Mikewa tsaye momy ta yi ta nufi stair ta na fadin " ni na tafi , in ki na nema na ina bedroom "

Ko dago kai Safa ba ta yi ba , har sai da momy ta Haye war ta
Ajiye wayar ta gefe ta yi kafin ta mike ta nufi dining room ta shiga kitchen

Jim kadan ta fito rike da tray da plate din jollof rice da soyayyar kaza , sai glass biyu guda na ruwa guda na juice

Table din tsakiyar falon ta nufa ta ajiye shi sama sannan ta tura table din gaban sofar ta , ta mike ta juya ta nufi Tv ta dauki remote ta kunna ta sannan ta dawo rike remote din

Ta zauna saman sofa sannan ta dauki spoon ta fara cin abincin , ta na danna remove din ta na son ta saka Film ta kala

Ta na tsaka da hakan ta jiyo wayar ta ta fara ruri allamun shigowar sako
Da farko ta so ta kyale amma sai ta kai hannu ta duba screen din ta ga an turo mata 「 Hi 」
Da wata bakuwar number , ga shi kuma number din ba ta Nigeria ba ce
Cike da shakku ta dauki wayar ta meda da 「 Hi 」ita ma
Sannan ta ajiye wayar ta ci gaba da cin abincin ta ta na kallon Tv din ta

Ta dauki wajen good five minutes kafin a yi mata reply
Hannu ta kai ta dauki wayar ta karanto sakon kamar haka * How are you , and your day ? *
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta yi reply da * Fine , what about you ? *

Wannan karan ta na turawa a ka yi mata reply da * Fine Thanks For asking 😊 *
* Okay , ko zan iya sannin da wa na ke magana * ta na gama rubuta hakan ta ajiye wayar ta geffen ta ta ci gaba da cin abincin ta

Wajen two minutes a dauka kafin a yi reply amma ba ta duba ba , ta ci gaba da cin abincin ta
Sai da ta Kamala , ta dauki ruwa ta sha , sannan ta dauki glass din juice ta ajiye saman table ta dauki tray din , ta mike ta nufi dining room ta wuce kitchen ta ajiye sannan ta fito

Ta na dawo ta zauna saman sofa ta mike kafafun ta saman table , ta kai hannu ta dauki glass din juice ta kai bakin ta ta na sha ta na kallon Tv

Cen ta jiyo wayar ta na ruri allamun shigowar sako
Ba tare da ta kali wayar ba ta kai hannu ta dauke ta , ta kawo saitin fuskar ta sannan ta karanto sakon kamar haka * Ba zan iya fada miki suna na yanzu ba , but ni dai babban masoyin ki ne , ina yawwan kallon shirin ki a tiktok , Instagram shi ya sa na yi kokarin samo number din ki kawai dan na fada miki abun da ke zuciya ta *
Sannan ta karanto na biyun shi ma * please ki amsa min mana , kar ki ji tsoro wlh mutun ne ni ba aljani ba 🥺🥺 *

Yar karamar dariya ta yi dan fa maganar shi ta karshe ta ba ta dariya wai mutum ne ba aljani ba
* ba karamin abu zai ba ni tsoro , nagode da irin kwarin guyiwar da ku ke ba ni , ina jin dadin hakan sosai * ta tura mishi ta na murmushi

* okay nagode sosai , shin ko zan iya sannin sunnan ki , pleaseeeee 🥺🥺 *
* My name is Safa 💋 *
* just Safa ? *
* yes, just Safa , what is your name too ? *
* sorry , i can't tell you 😞💔 *
* why ? , are you a criminal , a spy , or a celebrity ? *
* All 😅 *
* All ? 😳😳😳 *
* yes All 😎😎 kyawo na ne ya sa na zama Criminal , Dan leken asirin lafiyar ku ne ni , sannan kuma celebrity saboda kowa ya san ni , ko ke na san kin san ni 😎 *
Ba ta san lokacin da ta bushe da dariya jin abun da ya ce
Sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta mishi reply da * wow sannu ko , duka kai kadai , seriously tell me your name now *
* okay my name is Musadeeq 🌹*
* okay Mister Musadeeq , Good night , lokacin barci na ya yi *
* okay Good night miss Safa ❤ please can we keep contact 🥺🙏*
* no problem 😊*
* Thanks 😊 *
* Never mind *
* bye *
* bye *
Ta na rubuta mishi text na karshe ta ajiye wayar ta gefe ta ci gaba da kallon film din ta ta na shan juice din ta
Sai da ta kai wajen karfe 12 na dare ta na kallon film kafin ta kashe tv din ta dauki wayar ta ta koma bedroom din ta
Ko da ta koma ba ta konta kai tsaye ba , sai ta shiga ta yi wanka ta fito ta shirya cikin kayan barcin ta pink colour , ta shafa wasu lotion din ta , sannan ta Haye gadon ta ta konta ba tare da ta kashe wutar dakin ba, ba jimawa barci ya dauke ta

* ABUJA ( KUJE PRISON )

" Marwan Abdoul Karim , ka yi bako " wani soja ne tsaye bakin wata cell ya na kwallawa saurayin da ke cikin cell din kira , ba ka iya ganin komai da ga cikin cell saboda dare ne ga shi kuma wajen ba wasu lamps ba a dakwai

A hankali saurayin ya sauko da kafafun shi , ya na dan lumshe idanun shi allamun barci ma ya ke
Slowly ya bude bakin shi ya ce " wanene kuma ke nema na cikin wannan uban daren ? " ya fada kassa kassa yadda shi kadai ya ji abin da ya ce

Mikewa tsaye ya yi kafin ya tako a hankali ya fito cell din ya yi gaba, sojan na biye da bayan shi
Dakin da a ke kawo ziyara ya kai shi , sannan ya zaunar da shi saman chair , ya koma bayan shi ya tsaya ya na nade hanayan shi a kirji
Chapter 11 · 0% Book details