← Book details Haske Biyu Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 66

Sashe 21

Haske Biyu Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safa ta na zaune saman waiting chair ta na faman latsa wayar ta cikin konciyar hankali
A haka wani doctor ya karaso wajen ya na yi ma ta sallama ya na tambayar ahalin yarinyar da a ka kawo yanzun nan

Cikin ko in kula Safa ta ce " mariniya ce , ni ka dai ce yar uwarta "
" okay , biyo ni office di na " ya fada ya na juyawa ya fara takawa ya yi gaba
Cikin konciyar hankali ta mike ta bi bayan shi ta na ci gaba da latsa wayar ta

A tare su ka shiga office din doctor su na yin sallama a tare
Shi ya nufi chair din shi ya zauna sannan ya ce mata bismillah ta zauna
Ba musu ta zauna saman chair din da ke fuskantar shi ta na kallon shi ba tare da ta ce komai ba

Cikin nitsuwa ya ce mata " shin kin san ta na da ciki ? "
Jinjina mishi kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba

Shi ma jinjina kan shi ya yi kafin ya ce " kin san da hakan , amma ba za ki iya tsaya ki kula da ita ba yadda ya dace "

Cikin nitsuwa Safa ta katse shi da ce " Doctor , ka fada min abun da ke damun ta kai tsaye ba sai ka shiga yi min kwana ba "

Dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " shikenan , maganin zubar da ciki ta sha , yanzu haka cikin da ke jikin ta ya zube , an yi sa'a ya fice ba tare da ya yi ma ta illa ba "

A hankali Safa ta lumshe idanun ta , ta sake budewa , cikin nitsuwa Safa ta ce ma Doctor " please Doctor zan iya samun ko da photocopie na rapport din ta ? "

" me kuma za ki yi da shi , ai aikin gama ya riga ya gama , ba anfanin da zai miki " Doctor ya fada cikin ko in kula

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta matso ta kale shi cikin ido ta ce " Doctor , ba ita ba ta sha wannan maganin , ba ta shi akayi ba tare da sanin ta ba , ina bukatar rapport din dan na kai wannan karar gaban kotu , ya fuskanci hukuncin da ya dace "

Kare mata kallo da kyau Doctor ya yi na dan mintina kafin ya ce " shawarar da zan ba ki , gwara ki ba wa kan ki lafya ki je ki kula da yar uwar ki , duk da ban yarda da cewa ita yar uwar ki ce ba , amma hakan zai fi mu ku , ko kin kai wannan karar kotu ba abun da za su iya yi miki "

Dan karamin murmushi Safa ta yi kafin ta koma jikin chair ta jingina ta na kallon cikin ido
Cike da kasaita ta ce mishi " ku na daya da ga cikin dalilan da ya sa mata ba su da daraja a cikin society din ga , a matsayin ka na doctor kamata ya yi ka fara tambaya ta ya a ka yi ta shan wannan maganin , da tunanin ka , ya kamata ka yi nazari a kan abun da na ce , ba da sanin ta ta sha wannan maganin , wanda ya yi mata cikin shi ya ba ta wannan maganin ta sha , yanzu a ganin ka inda ta mutu da kisan kai za a kira wannan abun , tun da ba ta mutu ba , abun da ta rasa ya kama a kwacin mata hakin shi , ni ba wani abu na roke ka ka , kawai photocopie na rapport din ta na ke so , sauran zancen duk ba na ka ba ne , dan na san ba abun da za ka anfane ni da shi bayan rapport din , dan haka kawai ka ba ni ba sai mun shiga musayan yawu ba "

Gaskia ba karamin kwarjini ta yi wa doctor ba yanayin da yi maganar ji ya ke kamar ya na magana da wani babban mutun da ya san ciwon kan shi , ba da yarinyar da sai ya yi d'iya da ita

Dan karamin murmushi doctor ya yi kafin ya dauki wani file ya fice office din
Ta wutsiyar ido Safa ta raka shi da kallo har sai da ya fita sannan ta juyo ta na sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta sannan ta daga kai sama

Jim kadan Doctor ya dawo rike da file din da wani kuma daban
Ya na zuwa ya ajiye mata sabon gaban ta ya ce " ga shi nan, duk wani abu da za ki bukata ya na ciki "

Slowly ta sauko da kan ta , ta dauki file din ba tare da ta yi mishi godiya ba, ta mike ta juya za ta bar office din

Har ta rike handle din kofar ta jiyo Muryar Doctor ya na fadin " wannan dakiyar ta ki ba za ta anfane ki ba in har wanda ya yi mata wannan abun ya na sama da ku , amma ina yi muku fatan sa'a, Allah ya ba ki ikon karbar ma ta hakin ta , ki je ta na cikin room 4 "

Jinjina mishi kai kawai Safa ta yi ba tare da ta ce komai ta sa kai ta fice office din
Ta na fita doctor ya saki wani cool murmushi shi gaskia bai ta ba ganin yarinyar da ta burge shi kamar wannan ba , da wannan tunanin ya ci gaba da aikin shi
[28/08 à 18:50] MEERAH🪷🩷:

💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )

( A heart touching love story & destiny )

STORY & WRITTEN BY : MEERAH ❤

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

P A G E 1 2 🥀 ❤

Safa kuma ta na barin office din ta wuce kai tsaye room 4 in da doctor ya fada mata
Bakin ta dauke da wasu kassa kassa ta shigo dakin , Djamila na konce saman gado ta kauda kai gefe ta daura hannun ta da ke sanye da catheter saman ciki , a na yi mata Karin jini

Chair din da ke bakin gadon Safa ta nufa ta zauna ta daura kafa daya bisa daya , ta nade hanayan ta a kirji , ta na rike da wayar ta da hannu guda

Cikin nitsuwa ta ce " Djami , ya jikin na ki ? "
Ba tare da ta kale ta ba ta ce " Da sauki "
Jinjina kan ta Safa ta yi sannan ta ce " Djami , bayan rabuwar mu , kin hadu da Mansour ne ? "

Gyada ma ta Djamila ta yi allamun e
" zan so ki fada min abun da ya faru lokacin da ki ka gan shi "

Ajiyar zuciya Djamila ta sauke sai da ta dan dauki lokaci kafin ta ce " Na fada mishi ina ciki , da farko ya bata rai har ya ce na zubar da shi amma na nuna mishi ni ba zan iya ba ina son baby na , ban san yadda a ka yi kawai kawai lokaci guda ya shiga ba ni hakuri , wai wassa ya ke min shi ma ya na son babyn , ni na dauka da gaske ya ke , da ga haka ya ce min mu tafi shan ice cream , ba musu na bishi mu ka tafi dan a lokacin gaskia ina kwadayin ta , bayan mun je restaurant din mun zauna ya ce min na jira shi zai yi order , sannan ya tashi ya tafi reception , jim kadan ya dawo rike da bowl din ice cream guda biyu , ya ba ni guda ya rike guda , mu ka cikin konciyar hankali ya na yi min wassa , har da cewa in na haifi mace sunan mamar shi zai saka ma ta haka dai na biye mishi mu ka yi hirar mu har wajen magriba sannan ya raka ni har kofar gidan mu kafin ya juya ya yi tafiyar shi , cikin daren na fara jin ciki na ya fara yi min ciwo kadan kadan , ban kawo komai a raina ba na yi barci a haka , washe gari tun wajen karfe 8 na fara jiyo hayaniya cikin gida , ina bude idanu na ciki na ya yi wata irin muguwar murdewa har sai da na yi kara , a hankali na fara jan kafa na fito dan neman taimakon mama , ina fitowa ko sannu babu ta hau ni da fada wai na jamu su abun kunya , ashe hayaniya da na ji , mahaifin Mansour ne ya zo ya ce an fassa auren mu dama tambaya ce kawai to sun janye , wai Mansour ya fada mishi ina dauke da cikin shege su kuma ba za su karbi dan gaban fatiha ba cikin ahalin su bare kuma wanda ba jinin su ba , da haka duk mutanan gidan su ka hau ni da fada har na fadi a wajen ciwon ciki na ya ci gaba da tsananta amma ba su lura ba , a haka har su ka watse su ka bar ni ni kadai a wajen , sai da na dan samu sauki dai'dai Naïma ta fito da ga wanka na roke ta ta dauko min waya ta har na samu na kire ki " ta kai karshen wasu hawaye na zubo mata

Ajiyar zuciya Safa ta sauke kafin ta sauke hannayan ta , ta kali Djamila ta ce " to sai ki kontar da hankalin ki yanzu , abun da su ke magana a kai Allah ya karbi abun shi , cikin ya Zube kin huta "

A razane Djamila ta ke kallon Safa ta na son ta yi magana amma ta kassa fitowa
Mikewa tsaye Safa ta yi sannan ta ce " zan je wani waje , yanzu ina dawowa " ta kai karshen ta na juyawa za ta bar dakin
Chapter 21 · 0% Book details