Sashe 8
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk irin bayanin da zata mata ba yadda zata yi ba. Yau ita ce ranar arashe ta jarrabawar su zaune suke a exam hall in hankalin kowa yana kan amsa tambayar da take rubuce a jikin question paper in shi amma banda Anisa wadda take zaune in banda juya biro ba abun da take. A hankali taji wata murya wadda har duniya ta na e ba zata ta a mantawa da wannan muryar ba tana iran sunan ta cikin murya mai firgitar wa. "Anisaaaaaa! Anisaaaaaa! Anisaaaaaa!" Da sauri ta ago kanta tare da bin wajen da take jin ana iran sunan nata da kallo sai dai tana kai kallon ta wajen taga fitar ta waje. Kamar wadda aka tsikara da allura haka taji gaba aya zaman hall in ya gagareta inda kuma ta wani angaren taji ba abun da take so kamar ta fita tabi bayan ta. ewa tsaye tayi sannan ta fice daga cikin hall in inda ba wanda ya lura da fitar ta ta. Wata hanya daban taga Amrah ta bi inda hanyar jeji ne. A hankali Anisa ta shiga bin ta domin kuwa da ta tsaya sai taji jikin ta kamar ana watsa mata ruwan zafi. Haka ta dinga binta har suka urewa ganin mutanen. Anisa bata ankara ba sai ganin su tayi a wani asungurmin daji mai cike da wasu irin bishiyoyi masu duhu da raishen su kamar zai ta o sararin samaniya saboda tsawo. Waige-waige Anisa ta fara domin kuwa shigowar su jejin keda wuya ta nemi Amra sama ko asa ta rasa. ***** angaren Inspector Rasheed kuwa sosai ya du ufa wajen bincike domin gano makashin su Afra da Azra Sai dai har zuwa yanzu ba wata warar shaida da ya samu wadda zata taimaka mishi wajen gano wanda yake aikata kisan. Zaune yake a cikin office in shi yana an rubuce-rubuce, haka kawai jefi-jefi sai ya saki tsaki sakamakon ji da yayi kwata-kwata baya son yin aikin yau Tashi yayi daga kan kujerar sa sannan ya fita bakin kanta inda ya tarar da su kofur Bala a zaune. Duban shi ya kai wajen Kofur Bala in sannan yace. "Kofur Bala a fito da mota zamu je asibiti da gidan Justice Kabir da kuma gidan su marigayiya Afrah". Sara mishi Kofur Bala yayi sannan yace. "Ok Sir". Motar aka fito mishi da ita inda suka shiga suka nufi asibitin da gawarwakin su Afrah suke. Sai dai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa inda Inspector Rasheed ya san irin aikin da zai ara ratta owa kan shi da bai je asibitin ba. Lokacin da suka isa asibitin kai tsaye suka wuce akin adana gawarwakin. Kasancewar ma'aikatan wajen sun san shi yasa basu hana shi shiga ba. Suna shiga cikin akin ya bu aci da a janyo akwatin gawar da Afrah take ciki. Abun mamaki da aure kai ana janyo akwatin suka tarar da akwatin wayam kamar ba'a ta a ajiyar gawa a ciki ba. Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da Inspector Rasheed ya shiga maimaitawa duk kuwa da cewar bai tabbatar da hassasshen nashi ba. Gaba aya suma mutanen da suke wajen take mamaki da ru ani ya ziyarci fuskokin su a lokaci guda. Kofur Bala kuwa ji yayi kamar ace mishi it ya fice a guje domin kuwa shi daman wallahi tun farko ba san wannan Case in yake ba. Saurin kallon ma'aikatan wajen Inspector Rasheed yayi hankalin shi a matu ar tashe sannan yace. "Mai nake kallo haka?, Ina gawar cikin akwatin nan take?". Ya fa a fuska ba annuri. "Ranka ya da e ai wannan lamari sai dai mu tambayi juna domin kuwa wallahi ban san amsar da zan baka ba". aya daga cikin ma'aikatan Mutuary in ya fa "Wannan wane irin zancen banza ne kake son gayamun alhalin kune masu gadin akin, idan ban tambaye ku ba wa ku ke so na tambaya?" Inspector Rasheed ya fa a cikin tsawa. Gaba aya wajen shiru ya auka,domin kuwa wannan ba on al'amari ne kuma sabon abu a wajen mutanen asibitin baki aya, duba da cewar wannan shine karo na farko tun daga lokacin da aka kafa asibitin da aka ta a neman gawa aka rasa a cikin akin. "A fito da akwatin aya gawar". Suka tsinkayi muryar Inspector Rasheed ya fa a fuska ba fara'a. Su kam ma'aikatan wajen duk jikin su yayi sanyi aka rasa wanda zai iya tunkarar akwatin da Azra in take ciki balle a bu e shi. Kallon su Inspector Rasheed yayi sannan yace. "Wai ko baku ji abun da na fa a bane?". A hankali aya daga cikin su ya nufi akwatin da aka sanya Azra in a ciki irjin shi sai bugawa yake, mi a hannun shi da yake rawa yayi ya janyo akwatin sannan ya bu e akwatin da Azra in take ciki keda wuya mutanen wajen suka shiga tashin hankali fiye da na farko sakamakon tozali da akwatin Azra in da suka yi shima wayam sai wasu irin ananan tsutsotsi ne suke shawagi a ciki. A wannan lokacin da zaka tsaga jikin rabin mutanen wajen to ba zaka tarar da jini ba Saboda yadda suka shiga matsanancin tsoro. Nan fa aka shiga kallon-kallo a tsakanin mutanen wajen domin kuwa lamarin a yanzu ya daina basu mamaki sai tsananin tsoro. Duk wanda ka kalla a wajen tsoro ne zaka gani ya bayyana arara akan fuskokin su, idan ka ware Inspector Rasheed ka ai wanda ya shiga bin akwatunan da kallo aya bayan aya kamar mai nazarin wani abu. Umarni ya bayar da a bu e wani akwatin gawar. Da sauri an wajen suka kalli juna cikin tsananin tashin hankali,kafin daga bisani wani daga cikin su yayi arfin halin janyo wani akwati da yake kusa da akwatin Azra. Sai dai a wannan karon akwatin da aka bu in gawar tana nan lafiya a kwance a cikin akwatin ba alamar wani ba on abu a tattare da ita. Shiru wajen ya auka baka jin motsin komai sai arara sau ar numfarfashin su wanda yake nuni da alamar ru ani da tashin hankalin da suke ciki. Can dai inspector Rasheed ya ago idon shi da suka yi jawur ya bu i baki da niyyar yin magana sai kuma ya fasa ya fice domin kuwa a yadda yake j in zuciyarshi tana mishi idan yace zai yi magana za'a samu matsala. Yana fita daga cikin akin adana gawar kai tsaye office in shugaban asibitin ya nufa domin kuwa wannan lamari ne da dole a san matakin auka tun da wuri. ***** Haka Anisa ta shiga kai komo a cikin wannan daji mai cike da abun tsoro, ita kam a yanzu ta sadda ar da cewar mutuwa zata yi wani irin matsanancin tsoro ne ya rufe ta sakamakon tozali da wata bishiya da tayi kaman tana mata dariya. Bata gama shiga tashin hankali ba sai da ta tabbatar da cewa da gaske fa bishiyar dariya take mata. Jikin ta ne ya shiga wata irin karkarwa kamar mazari take kuma ta fara jin sautin dariya ta ko ina a cikin dajin yana amsa kowa. aga idon da zata yi kawai tayi arba da gaba aya bishiyoyin cikin dajin suna mata dariya, daga baya kuma kawai taga sun fashe da kuka har da hawaye. Ai Anisa na ganin haka bata san sanda ta dur ushe a wajen ba ta shiga rusa ihu tana neman agaji, sai dai ina babu mai jin ta balle a kawo mata taimako. owar abu da taji a kusa da ita ne ya sanyata saurin ago kai tare da ja da baya. Mai zata gani in ba gawar Anisa da Azra ba kwance a gefen ta wasu tsutsotsi suna biyowa ta tsakanin idanun su. Wani gigitaccen ihu Anisa ta sake sannan ta zube a wajen sumammiya. Tsananin zafin ranar da ake ne ya buge ta wanda yayi sanadiyar farfa owar ta. Idanunta take arin bu ewa dan taga hasken duniya, sai dai mai duhu ta gani a maimakon taga haske. Gaban ta ne ya fa i inda cikin sauri ta sanya hannu ta shafo idanun nata sai dai wayam taji gurbin idon nata a shafe kamar ba'a ta a hallitar ido a wajen ba. e baki tayi da niyyar yin ihu amma kuma muryar tata ta katsea sakamakon dariyar da taji a gefen ta da kuma kuka a lokaci guda suna tashi. "Dan Allah wacece ke?, Dan Allah mai ya sami idona?,Mai na miki kike son ganin bayana?". Duk a lokaci guda Anisa ta jefamata wa annan tambayoyin. A maimakon taji an bata amsa sai taji an cigaba da aka dariyar da kuma kukan har dajin sai da ya ringa amsawa. Ita kam Anisa zuwa wannan lokacin ta cire rai da sake rayuwa, take kuma duk wani tsoro ya gushe mata zuciyarta ta bushe cikin araji tace. "Mai kuke jira da nine da ba zaku kashe ni ba?, Ku kashe ni nace tun da kun raba ni da abu mafi muhimmanci a rayuwata". Anisa ta arashe maganar cikin sakin kuka mai tsuma rai. "Anisa mai kike ci na baka na zuba, ai ko baki nemi ki mutu ba to tabbas zaki mutu saboda daman mutuwa ita ta kama ce ki a wannan lokacin kamar yadda sauran an uwan ki suka mutu, amma kafin nan sai kin ani ba in cikin da na ana, sai kin fara girbar abun da kuka shuka, sai kin gane cewar cin amana ba abu ne mai kyau ba". "A.....m......r.......a.....h.....ke.....ce..." Anisa ta fa a cikin rawar murya. Wata mahaukaciyar dariya Amrah ta kwashe da ita sai da ta auki tsawon lokaci tana yin ta kafin tace. "Kina mamaki ne wadda ku ka zalunta ku ka yi sanadiyar mutuwar ta ta dawo?, Tabbas nice na dawo aukar Fansaaaaaaaaaa". *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_ *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* -------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *008* ____________________________ Jin wannan mummunan labari da hukumar makarantar suka yi ba aramin dugunzuma hankalin su ya yi ba inda ba tare da ata lokaci ba suka unguma suka nufi bayan makarantar. Innalillahi wa'innailaihi