← Book details Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 45

Sashe 42

Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ciki murna ne ko kuma akasin haka. arfe Shida dai-dai suka fito cikin shirin su na tafiya sai a sannan na ara ganin tsantsar kammannin ta da Amrah. Sanye take cikin wata sea green in abaya wadda ta fito da tsantsar baiwar kyawun da Allah ya mata. A dai-dai wannan lokacin Anwar ya araso gidan Wayyo zo ku ga idon Anwar a lokacin da ya yi arba da Farida,take kewar Amrah ta dawo mishi sabuwa ha e da aunar ta. Kafeta yayi da ido har bai san cewar mahaifin ta ya lura da hakan ba sai da ya ji sau ar hannun shi a kafa ar shi yana cewa. "Malam Anwar mu je ko kar mu makara daman kai ka ai muke jira". an sosa kai Anwar yayi yana jin wata kunya ta rufe shi sannan suka nufi motar suka shiga suka bar gidan. Anwar ne yake jan motar inda Farida da mahaifiyar ta suke baya mahaifin ta kuma yana gefen Anwar a kujerar gaba. A haka suka kama hanyar jahar Yobe in sai dai mu musu fatan sau a lafiya. ***** Washe gari sai wajen arfe sha aya su Justice Kabir suka fito cikin shirin su na komawa Zaria. Har wajen motar su Malam Kabiru suka fito suka raka su. Tsayaawa yin sallama suka yi Umar kuwa yana da tsaye a gefe sai cika yake yana batsewa tare da aikawa Justice Kabir harara. A dai-dai wannan lokacin motar su Anwar ta tsaya a gefen motar su Justice Kabir a ofar gidan Malam Kabiru Tun da motar ta tsaya Malam Kabiru ya kafe motar da ido a lokaci guda kuma yana jin zuciyar shi tana matsanancin bugawa. A hankali aka bu e murfin motar aka fito. Mahaifiyar Farida ce ta fara fitowa sai Farida da Anwar sai kuma mahaifin Farida da ya fito a arshe. Wata irin sarawa kan mahaifin Farida ya yi a lokaci guda shima Malam Kabiru ya ji haka sakamakon sar ewar da idanuwan su suka yi a cikin na juna. Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin su Umar da Farida kowa da abun da yake sa awa a asan zuciyar shi inda Umar da Usman suka shiga kallon mahaifin su sannan su juya su kalli mahaifin Farida sannan su kalli Farida cikin matsanancin mamaki. Haka a angaren Farida in ma kallo ta shiga aikawa mahaifin nata da Malam Kabiru in cikin tsananin mamaki domin kuwa duk yadda Anwar ya basu labarin kammannin da mahaifin nata yake da Malam Kabiru sai taga ashe ma wancan labari ne yanzu ne taga gaskiya ra'ayul aini. Allah mai iko Ubangiji Mai hallita, tabbas Allah abin godiya ne lalle Allah shi ka ai yake yadda yaso a kan bayin shi a kuma lokacin da ya so ku ga tsantsar kammanni. Ita kuwa Gwaggo Sa'adatu kallon Farida da ta yi sai da numfashin ta ya auke na wucin gadi domin kuwa duk a tunanin ta Amrah ce. Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga. Arewa books @shamsiyamanga. Whatsapp number 07060943991 Phone call 09065779330 Don't forget to share and comment pls. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA* : _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* ------------------------------------------------ *Bissimillahir rahmani rahim* *38-39* ________________________________ "HASSAN ashe daman da rabon ruhikan mu zaku sake kasancewa a inuwa aya?, Ashe daman akwai rabon mu sake rayuwa tare? Hassan ashe daman mutuwa ba zata auke mu ba ba tare da mun sake kallon juna ba?, Allah na gode maka bisa wannan udira da ka nuna a kan mu!, Mun auki tsawon shekaru bama tare da juna amma sai gashi lokaci guda Allah ya sake ha a fuskokin mu". Wannan su ne kalmomin da suka shiga fitowa ta bakin mahaifin Farida take kuma hawaye ya shiga sintiri ta fuskar shi sannan ya zame a asa kan gwaiwowin shi kafin kuma ya saki kuka mai sauti,yana kai goshin shi asa ya yi Sujuddu shukriyya. Malam Kabiru ne ya tako da sauri ya araso har inda mahaifin Farida in yake dur ushe sannan ya sanya hannu ya ago kafin kuma ya rungume shi tsam a jikin shi,yana jin wata sabuwar soyayyar shi tana ratsa duk wani argo da ashi na jikin shi. Kuka sosai Malam Kabiru da mahaifin Farida su ke yi kuka kuma irin mai sautin nan da ta a zuciya,duk wanda yake wajen sai da ya tausaya mu su domin kuwa abin da mamaki da kuma tausayi a ce manyan mutane irin su Malam Kabiru gasu dur ushe a asa suna kuka kamar wasu ananan yara. Farida kuwa da mahaifiyar ta da Gwaggo Sa'adatu suma tunin suka fara kukan duk da basu san dalilin kukan su Malam Kabiru in ba. Justice Kabir kuwa da mukhtar motar da basu iya shiga ba Kennan suka tsaya suma suna ganin ikon Allah. Shi kuwa Anwar da yake tsaye a gefe tun da suka fito a motar yaga mahaifin Azrah ya cika da tsananin mamakin abin da kawo mahaifin Azrah in wajen mahaifin Amrah sannan ya ma aka yi ya san inda su ke. Ganin da Usman ya yi cewar har mutane sun fara taruwa a wajen su Malam Kabiru in sun zama kamar Tv kasancewar unguwar irin unguwa ce ta mutane da yawa duba da yadda ta kasance tsohuwar unguwa. Wannan ya sanya Usman in saurin zuwa ya aga mahaifin na shi sannan ya yiwa mahaifin Farida da su Anwar iso cikin gidan. Haka suka unguma gaba aya suka shiga cikin gidan harda su Justice Kabir domin kuwa tafiyar da ya ji ya fasa yin ta gaba aya yana son ya ji ala ar Malam Kabiru da wannan mutumin. A tsakar gidan aka baje musu wata atuwar tabarma duba da yadda gidan yake da fili gashi akwai bishiyar maina atuwa a tsakar gidan. Umar ne ya fita waje inda ya nufi wani shago ya kar o lemo masu sanyi guda shida da kuma ruwan leda na pure water ya nufo gidan dashi ashe ma shagon na Umar in ne. Gidan ya ara nufowa ya kawo mu su ruwan sannan ya nemi waje ya zauna tare da gaishe da su sannan ya musu barka da zuwa. Abinci Gwaggo Sa'adatu ta tashi ta zubo musu daman bayan abincin da take matan su Umar da Usman suna kawo mata shiyasa wataran abincin har yawa yake musu. Abincin suka shiga ci inda Farida ta kasa shiru ta ago ta dubi mahaifin ta sannan tace. "Dad nifa kaina ya kulle, Dad Dan Allah ku fitar damu daga cikin wannan duhun da ku ka sanya kawunan mu, Dad ashe daman ku an biyu ne shine bamu ta a sannin hakan ba?, Dad ko da wasa baka ta a sanar damu cewar akwai wani an uwan ka na jini da yake raye ba saboda kullum idan mun tambaye ka sai kace mana an uwan ka duk sun rasu,tun muna tambaya har mu ka daina tambaya, Dad ashe daman kana da an uwa ka barmu ba tare da mun san su ba balle ka nuna mana su, yanzu Dad da halin mutuwa ya kasance ya zamu yi haka zamu mutu ba tare da mun san dangin ka ba,a yanzu ma ba dan albarkacin Ya Anwar da ya zo gidan mu ya sanar da kai cewar ya ga mai kama da kai ba da shikennan nake ga har mu mutu ba zamu ta a sannin su ba. Dad mai yasa?". Farida ta arashe maganar cikin rawar murya ga hawayen da suka shiga zarya a kuncin ta. Sunkuyar da kan shi mahaifin Farida yayi asa sannan ya tsame hannun shi daga cikin abincin da su ke ci in, kafin ya ago da kan shi ya dube su yace. "Farida ki yi ha uri wallahi ni kaina ban san dalilin da ya sanya na kasa sanar da ku asali na da kuma dangi na ba, ki sani kullum burina bai wuce na yi ido hu u da an uwa na ba amma kuma ban san dalilin da yasa na kasa neman shi ba". arashe maganar tare da sanya hannu ya goge da suka zubo mishi. "HUSSAIN ka sani ni kaina ban san mai yasa ban ta a jin ina son na nemeka ba duk kuwa da cewar na da e da sanin cewa kana raye kuma har unguwar da ka ke a cikin garin Zaria da gidan ka na sani amma kuma ban ta a sha'awar na nemeka ba". "To amma Malam ni wannan abin ya bani mamaki to wai shin ta ya aka yi ku ka rabu ma da an uwan na ka?, Sannan kana nufin Malam Umaru mai almajirai ba shine asalin mahaifin ka ba" Usman ya fa a da fuskar mamaki. Murmushi Malam Kabiru ya sake wanda kana gani kasan cewa ya e ne wanda yafi kuka ciwo sannan yace. "Tabbas Malam Umaru ba shine asalin mahaifin na ba in ta aice ma bayani ma ban san shi ba sai dalilin zuwa na Nigeria,bamu da wata ala a da shi ta an uwan taka sai dai ta musulunci sannan kuma shi in malami na ne. In sha Allah a yanzu zan sanar da ku asalin mu da kuma inda mu ka fito". *WAIWAYE* *SHEKARU HAMSIN BAYA DA SUKA SHU E.*
Chapter 42 · 0% Book details