Sashe 18
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsaye. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya in da kullum Azra bata da aiki wanda ya wuce ta ga ta ba antawa Amrah rai. Sai kuma aka yi rashin Sa'a domin kuwa Amrah bata ta a nuna ta san ma mai Azra in take ba, idan zata mata abun acin rai guda goma ta ko guda aya Amrah bata auka a matsayin abun da zai sa ran ta ya aci. Wannan abun ba aramin damun Azra yake ba domin kuwa ita kam bata da buri da ya wuce ta ga ta ona ran Amrah in musamman da ta fahimci cewa Amrah ar talakawa ce. angaren mu kuwa ni da su Afarah ba wani abu mummuna da muke nunawa Amrah na musgunawa kullum cikin jan ta a jiki mu ke, musamman da muka fahimci cewa ta fi mu saurin fahimta da gane karatu. Duk bayan sati Yaya Umar ko Yaya ko yaya Usman aya daga cikin su yana kawowa Amrah ziyara domin su duba ya yanayin karatun na ta. Shi kuwa Anwar kusan kullum afar shi tana cikin makarantar mu, domin kuwa wata irin kulawa ta musamman ya ke bawa Amrah in ga waya da suke akai-akai. Sai dai duk zuwan da Anwar in yake har yau wajen wata guda basu ta a ha uwa da su Azrah ba, ni ka ai na san shi, sai dai duk sanda ya ira yana yawan tambayar ta awayen ta kuma wani lokacin har ba mu wayar take mu gaisa dukan mu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya in da yau muke dosar wata biyu da fara karatun mu. Zaune mu ke a lecture Hall in mu in da kowa ya du ufa wajen duba takrda sakamakon test in da wani lecture in mu zai mana. An yi test Alhamdulillahi kuma test in ta yi mugun sau i ba kamar yadda muka yi tunani ba. Kasancewar kowane lecturer da irin method of yadda yake gudanar da abubuwan shi, to wannan ma haka wanda mu ke cewa Prof,a a'ida ba ya bada test sai dai ya kafe sunayen masu highest mark. "Amira Prof fa ya kafe list in wanda suka ci test in shi". Wata awar mu da mu ke ira Maryam ta fa a tana mai ficewa daga hall Da sauri muka mi e dan mu je mu duba. Murmushi Azra ta yi sannan ta ce. "Wanda ya san bai tsinana abun kirki ba ai shi zai aga hankalin shi". Ta fa a tana gyara zaman mayafin ta. Cikin ikon Allah kuwa muna zuwa muna dubawa sunan mu duka ya fito amma sunan Amrah shine a farko. Innalillahi ina wuta Azra ta jefa kanta, murna mu ke Sosai tare da rungume Amrah. Fuuuuu Azra ta juya ta bar wajen cikin tsananin unar zuciya. *MANGA* Comment Share Fisabillillahi *FANSAR FATALWA* _Tsarawa/Rubutawa_ *SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ . *Free book* -------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *014* ____________________________ Kaf cikin mu ba wanda ya lura da yanayin da Azra ta bar wajen,mu kam sai murna mu ke, Amrah ce ta fara farga da cewar Azra bata wajen,kallo na ta yi sannan ta ce. "Amira Azra fa?". Sai a sannan muka juya inda muka lura cewar Azra in bata wajen. aga kafa a na yi alamar bansani ba sannan nace. "Kun ga mu wuce Capteria mu je mu ci abinci dan wallahi yau girki na ne,kuma gaskiya ba zan iya girki ba". "Haka dai kullum mutum ya iya". Cewar Afra tana galla mun harara. Murmushi Amra ta yi sannan ta ce. "A'a ba za'a yi haka ba mu je Hostel in ni sai na girka mana, ga mu da kayan abinci kuma mai ye zamu je mu kashe ku in mu". Juyawa muka yi duka sannan muka nufi Hostel Azra kuwa tana barin bakin notice board in kai tsaye Hostel ta wuce tana tafiya kamar zata kifa ga zuciyarta da take jin tana mata wata iriyar suya kamar irjin zai one. Tana isa aki ta dannawa ofa key sannan ta cire mayafin ta ta yi wulli da shi gefe kafin kuma ta nemi bakin gado ta zauna tana mayar da numfashi kamar wadda ta yi gudun tsere. auki tsawon lokaci a haka tana zaune kafin ta yi auni ta ji abu mai umi a kuncin ta. Hannu ta sanya ta gogo wajen tabbas idan har ba arya idanun ta suka mata ba wannan hawaye ne yake zubowa daga cikin idonta. Mai hakan yake nufi?,kuka ta ke saboda waccan yarinyar ar matsiyatan?. Azra ta tambayi kan ta a zuciyar ta. arya ki ke wallahi Amra!, Wallahi arya ki ke ki zama dalilin zubar hawaye na a doron asa". Azra ta fa a cikin araji tana mi ewa tsaye tare da fara zagaye cikin akin, kafin ta cigaba da magana. "Wacece ke Amra?, Ai wallahi baki isa ki zamar mun ba in ciki ba,ya zamar mun dole na yi gaggawar aukar mataki a kan ki tun kafin lokaci ya zo ya ure mun". Bugun ofar da ta ji ana yi ne ya sanya ta saurin shiga toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito ta bu ofar. Su Amra ta gani tsaye a bakin ofar, Saurin kawar da kan ta gefe ta yi sannan ta juya ta koma cikin akin domin tsayuwar ta a wajen dai-dai ya ke da tonuwar asirin ta. Da ido muka bi ta gaba ayan mu cikin tsananin mamaki domin kuwa kallo aya muka mata muka fahimci cewa ta yi kuka. Shiga cikin akin muka yi inda na bu i baki tare da duban Azra sannan na fara magana. "Azra lafiya kuwa?". Da sauri ta ago kan ta tare da duba na irin duban mai ki ke nufi sannan ta ce. "Mai ki ka ga?, Ko wani abu ki ka ga ni daban?". Kallon juna muka yi sannan Anisa ta ce. "Azra ai ba wani abu zaki ce ta ga ba, cewa zaki yi wani abu ku ka ga, Azra alamun ki sun yi kama da na marar lafiya, kuma gashi kamar kin yi kuka". aramin tsaki Azra ta ja kafin daga bisani ta ce. "Ba wata damuwa fa, kawai an kai na ne na ji ya namun ciwo, kuma na sha magani". Addu'ar samun lafiya muka mata amma nikam ba wai na yadda da bayanin na ta bane. ****** Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum awancen mu ara arfi yake, duk in da zaka ga aya daga cikin mu to zaka ga sauran, wannan dalilin ya sanya har suna muka sanja domin kuwa idan kaje Hostel ko class in mu idan baka ce Five Stars ba to ba wanda zai gane mu ka ke nema. Kwance tashi ba wuya a wajen Allah yau mu ke shirin fara jarrabawar mu ta first semester a school. Kowa ka gani karatu ya ke ba kama hannun yaro. Mu ma a angaren mu ba'a bar mu a baya ba domin kuwa fafafa mu ke karatu sosai kamar kan mu zai cire. Cikin ikon Allah mun fara jarrabawa yau kuma Alhamdulillahi exam in yau in ya yi sau Haka abubuwa suka cigaba da tafiya in da yau mu ke zana Paper in mu ta arshen a makaranta. Mun gama jarrabawa lafiya in da kowa kuma ya fara shirin tafiya gida sakamakon hutun wasu an kwanaki da aka mana. Amra ma a angaren ta ya Anwar ya zo aukar ta, a sannan ne kuma muka taho da su Anisa da Afra da Amra in da Azra ta ke biye da mu a baya. Kasancewar duk an zo aukan mu, in da kowa motar gidan su ta zo aukan shi. "Lah Afra ga can yaya Anwar a tsaye ku zo mu je ku gaisa". Amra ta fa a tana sakin murmushi. "Ah yau zamu ga Yaya Anwar in nan dai wanda kullum aka bi aka dame mu da zancen shi" Afra ta fa a tana kai duban ta in da Anwar ya ke tsaye. Tun da suka doshi wajen Afra ta kafe Anwar da ido tana jin wani irin ba on al'amari a tattare da ita. Murmushi Anwar ya shiga sakarwa Amra in da ita ma ta shiga mayar mishi har suka isa wajen. "Ga Majnun in Amra ya araso". Amira ta fa a cikin sigar zolaya. Dariya Anwar ya yi sannan yace "Ai na wuce Majnun a wajen ta domin soyayyar mu ta wuce irin soyayyar laila da Majnun, ta zarce ta romio da Juliet, ta kere ta Ram da Sita, ko ba haka ba Masoyiya". Yaya Anwar ya fa a yana kashewa Amra ido. Rufe idon ta Amra ta yi cikin jin kunya. "Ah lalle ma Watau Anwar ko kunya ta baka ji". Amira ta fa a tana rufe baki. Tun da suka tsaya a wajen Afrah ta kafe Anwar da ido ko iftawa bata yi, lokaci guda ta ji guy in ya matu ar burge ta. Amrah ce ta juyo tana cewa. "Afra, Anisa da kuma Amira ga Ya Anwar ina". Turus ta ja ta tsaya ganin irin yadda Afrah ta kafe Anwar in da ido ko iftawa ba ta yi, bata ma san abun da Amrah in ta ke cewa ba. Cike da mamakin ganin irin kallon da Afrah in ta kewa Anwar Amrah ta ta a ta tare da jijjiga tana cewa. Wani irin ayattaccen murmushi Azra ta saki wanda ita ka ai ta san ma'anar shi a ran ta tace. "Tabbas na samu makami, Tabbas Afrah da ke zan yi amfani wajen cikar muradi na, Afarah ke zaki zamar mun makamin da zan ri a dan tarwatsa rayuwar wannan ar matsiyatan". "Afrah lafiya kuwa?". Afrah ta tainkayi muryar Amrah ta daki dodon kunnen ta kamar sau ar aradu. Da sauri Afrah ta an firgita sannan ta yi saurin basarwa tare da sosa kai alamar rashin gaskiya sannan ta ce. "Uhmmm Amrah gaskiya ya Anwar in ki ya ha u, kuma kun dace sosai wallahi, Ubangiji ya tabbatar da Alkhairi a tsakanin ku". Amrah bata kawo komai a ranta ba ta saki murmushi sannan ta ce. "Ameen ya Allah Afrah, yawwa Masoyi ga su Afrah da Anisa