Sashe 30
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Amrah karatun da ta da e da sanin shi,idan darasi zaki mata ai kamata yayi ki mata a kan sabon karatu amma wannan tun yaushe aka da e da sanin shi,a yanzu lallashi ya kamata ki mata ba wa annan suki burutsin karatun ba ko ba haka ba Amrah?". Na tsinkayi muryar Azra ta daki dodon kunnena, da sauri na juyo na dube ta inda take ta jefa mun wani kallo mai cike da gagar i na cewar Amira ina garga in ki kar ki fara jefa kan ki a cikin ramin da kika san ba zaki iya fita ba. Har na bu i baki zan yi magana sai kuma ga iran gaggawa an yiwa Amrah ana iran ta daga school management kuma da gaggawa. Wani matsanancin fa uwar gaba ne ya ziyarce mu a lokaci guda daga ni har Amrah Tashi tayi tare da aukar hijab in ta ta sanya sannan ta fara tafiya tana tangal-tangal kamar wadda wai ya fashewa a ciki. Tashi nayi da sauri zan kamata sai dai kafin na arasa inda take in har Azrah ta isa ta ri e ta tare da cewa. "Wayyo Allah Amrah kar ki fa i bari na rakaki". Ba yadda zan yi haka na yale Azrah ta kama Amrah inda muka bi bayan su muka nufi Administrative Block Duk inda muka wuce haka zaka ji ana ananun maganganu ana nuna Amrah,wasu kuwa hadda yada ba ar magana amma ba wanda muka kula tun da mun lura daman neman magana mutane suke. Su Khadijah ne suka zo wucewa Clique in su guda hadda arin wasu maza guda uku, wata iriyar dariyar suka kwashe da ita irin ta rainin hankali nan hadda tafawa sannan Khadijah ta dube su tace. "Ikon Allah nikam banga amfanin saka hijab ga wasu mutanen ba domin kuwa abun da ake oyewa in mun riga da mun gani duniya ma ta gani,to maiye na oyewar In banda munafurci,Allah dai yayi wadaran wasu mutanen wallahi". Har na bu i baki zan tanka musu kawai Amrah ta dam e mun hannu tare da jijjiga mun kai sannan muka wuce ba tare da mun tanka musu ba. A bakin Admin Block in muka tsaya muna jiran Amrah inda ita kuma ta shiga cikin Conference Hall in inda malamai suke tare a ciki ana jiran Amrah Da sallama a bakin ta ta shiga duk kuwa da ta san cewa akwai malami Kiristan a wajen amma saboda ta saba hakan bai sanya ta i yi musu sallama ba saboda ta saba. Tun da ta shiga Dr Gana ya kafeta da ido cikin tsananin tausayin ta ganin yadda duk ta zabge ta rame wasu hawaye ne yaji suna arin zubo mishi inda ya sanya hannu ya goge gudun kar a gani. Kujera aka nuna mata ta zauna sannan aka mi o mata wata farar takarda. Cikin rawar hannu ta mi a hannun ta ta kar i takardar ba tare da ta bu e ba. VC ne ya bu i bakin shi sannan ya fara magana cikin harshen turanci. "Amrah Kabir a madadin malamai da hukumar wannan makarantar muna sanar dake cewar mun dakatar dake daga karatu a cikin wannan makarantar ma'ana a yanzu ke ba alibar mu bace ba, sakamakon samun ki da muka yi da aikata laifin irin wanda tun da aka kafa wannan makaranta ba'a ta a samun makamancin irin hakan ya faru ba sai a kan ki, wannan dalilin ya sanya hukumar makaranta zauna a kan ki domin zartar da hukunci wanda yayi dai-dai da abun da kika aikata,sannan mun zartar miki da wannan hukuncin ne saboda ya zama darasi ga an bayan ki,domin kuwa mun san cewar akwai masu zuciya irin taki da yawa a duniya to amma wannan hukuncin shi zai sa duk wani mai sha'awar aikata abu kwatankwacin naki to zai tsorata idan ya tuna da irin hukuncin da aka miki in, dan haka zaki iya tashi ki tafi mun sallameki" Tun da VC in ya fara magana Amrah taji kamar an sanya wata guduma ne an buga mata a tsakiyar kai,kafe shi da ido tayi kamar an dasata a lokaci guda kuma taji kamar an sanya ruwa an wanke mata duk wani acin rai da take ciki,a maimakon tayi kuka kawai sai gani suka yi ta kwashe da wata irin dariya kamar wata zararriya,a lokaci aya kuma tana dariyar hawaye yana fitowa daga idon ta watau kuka da dariya a lokaci guda. Duk wanda yake cikin Hall in sai da Amrah ta bashi tausayi domin kuwa kallo aya zaka mata ka fahimci cewa ta zauce. ewa tsaye tayi ta fara tafiya tana tangal-tangal kamar wadda ta sha giya ta bugu. Dr Gana ne ya fara arin mi ewa da sauri zai ri o ta sai dai take Shahid ya ru o shi wanda yake zaune a kusa dashi sannan ya shiga jijjiga mishi kai alamar a'a. Amrah kuwa har ta fito daga cikin Hall in bata daina aka dariyar da take yi in ba ga hawayen shima bai daina zubowa ta idon ta ba. Tun daga nesa na hango ta na tafe tana tangal-tangal,da gudu na tashi inda na nufeta sai dai kafin na arasa inda take in har ta yanki jiki ta fa i ko alamar shurawa bata yi ba. Innalillahi wa'innailaihi rajiun, Hasbunnallahu wa ni'imal wakil,shine kawai abun da bakunan mutanen wajen ya shiga furtawa ganin cewa kamar Amrah in bata da rai. Cikin tsananin tashin hankali na arasa kan ta da gudu inda na shiga jijjiga ta ina iran sunan ta. "Amrah dan Allah ki tashi, Amrah dan girman Allah ki taimakawa ki tashi, Amrah ki tashi wallahi yanzu zan sanar dake gaskiyar da na oye miki, Amrah nasan ba mutuwa kika yi ba, Amrah ki tashiiiiii". Na fa a ina sakin wata razannanniyyar ara tare da ame Amrah in a jikina. A dai-dai wannan lokacin su Afrah da Anisa da Azra suka araso wajen da gudu suna arin ta a Amrah in,sai dai wata irin sha a da na kaiwa wuyan Azra in shi ya dakatar da ita daga abun da take shirin aikatawa Cikin wata iriyar murya wadda kamar ba tawa ba na fara magana. "Na rantse da girman Ubangiji idan har Amrah ta mutu wallahi tallahi sai na kashe ku gaba aya sai dai nima a kashe ni tsinnannu kawai wa anda suka kwashe kayan su daga gaban ma'aiki,wallahi sai rayuwar ku ta tagayyara domin kuwa tun a nan duniya na tabbatar Allah ba zai bar ku ba dan wallahi sai kun ga sakayya mafi muni". Duk irin yadda Azra ta so ta wace kan ta daga irin sha ar da na mata abun ya gagara,tsananin tsoro da tashin hankali ne ya bayyana a fuskokin su Afrah da Anisa ganin cewar har Azra in ta fara fita a hayyacin ta. Mutanen wajen ne suka shiga kiciniyar wace Azra daga hannun nawa amma ina! Duk irin yawan mutanen wajen sun kasa wace Azra daga hannuna domin kuwa wani irin arfi nayi ba zaka ce mutum bane da wannan arfin. yar dai aka samu aka wace Azra in a hannun nawa wadda tunin ta da e da sumewa. Nima a take kuma na yanki jiki na fa i tare da sumewa a wajen. Sosai mutanen wajen suka cika da mamakin wannan al'amarin. *MANGA* _Comment_ _Share_ _Fisabillillahi_. *FANSAR FATALWA* ( _Horror Story_ _Tsarawa/Rubutawa_ SHAMSIYYA MANGA* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* *SADAUKARWA*: _Wannan book in gaba ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_. *Free book* ------------------------------------------------- *Bissimillahir rahmani rahim* *023* ________________________________ Ambulance aka samu inda aka sanya Azra da Amira a ciki,in da ana arin aukar Amrah matasan makarantar suka ce ai wallahi ba za'a auke ta ba gara a barta ta mutu,domin kuwa bata da wani amfani a cikin al'umma. Nan fa hayaniya ta kware a wajen wasu daga cikin mutanen wajen suna goyon bayan a auki Amrah in a taimaka a kai ta asibitin inda wasu kuwa suka yi tsallen aradu suka ce ba za'a auke ta ba. Sai dai kun san an ce majoraty carry the both wannan ya sanya masu i irarin cewa ba za'a kai Amrah asibitin ba suka rinjayi masu cewa a taimaka mata Hakan ya sanya duk yadda wasu suka so a taimaka mata amma abun a ci tura gashi suna kallo rayuwar ta tana tsaka-tsaki domin kuwa a wannan halin da ake ciki ma basu sani ba shin Amrah in tana da rai ko kuma ta mutu ne. Hayaniyar da malaman da suke cikin Conference Hall in suka ji tayi yawa ne ya sanya su fitowa da sauri dan ganin mai yake faruwa. Ganin Amrah suka yi a yashe a asa ba alamar numfashi a tare da ita,ga matasan makarantar kuma sun cika a wajen maza da mata ana ta cece-kuce wasu har suna cewa a basu ita kawai suje su binne ta da ranta,wasu kuwa cewa suke a banka mata wuta kawai ta mutu, kasancewar tun ranar da abun ya faru Amrah bata sake fita koda nan da can ba,duk da cewa ko a cikin Hostel in ma ba tsira tayi tun da wani lokacin har cikin akin su ake shigowa a ci mata mutunci,babu irin ba en maganganu da ba'a gayawa Amrah in,kullum cikin kuka take karatu kuwa tunin ta ajiye shi a gefe domin kuwa da ace ba'a koreta a makarantar ba to tabbas ta san wannan semester in ba abun da zata iya tsinanawa wata ila ma a mata repeat. Dr Gana ne ya arasa inda Amrah in take a yashe ganin shi da an makarantar suka yi ya sanya suka fara darewa suna bashi hanya wajen kuma yayi tsit kasancewar shi yana daga cikin malaman da alibai suke shakka a cikin makarantar saboda baya sakewa kowa fuska balle a raina shi. Ba wanda ya saurara yana arasawa inda Amrah in take ya sanya hannu ya sunkuceta sannan ya fice daga cikin Admin Block in da ita ya nufi motar shi duk sai idanun mutanen suka dawo kan shi inda ananan maganganun suka shiga tashi. A bayan motar ya sanya Amrah sannan Anisa da Afrah suma suka shiga motar wa anda suka biyo bayan