Sashe 3
Fansar Fatalwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
daman tunin ta sume ya kai sau ba adadi. Haka dai suna ji suna gani aka fice da gawar Afrah in aka kaita asibiti aka ajiye ta a mutuary har zuwa sanda an sanda zasu gama binciken su. ***** Yau Sati guda Kennan da mutuwar Afrah amma gidan su afrah kamar yau aka yi mutuwar domin kuwa su kullum mutuwar sabuwa take zamowa a wajen su. angaren Anwar ma kullum a gidan su Afrah yake yini har zuwa dare kafin daga bisani ya tafi gidan su. Yau ma kamar kullum arfe goma ya tashi tafiya gida kamar yadda ya saba, lokacin da ya isa gidan bai tarar da an gidan su a falo ba kowa ya shige aki ya kwanta, shima akin nashi ya nufa,inda ya tura ofar akin ya shiga,kasancewar wutar akin a kashe yake ya sanya ya nufi wajen makunnar wutar ya kunna, tabbas da Anwar ya san abun da zai yi tozali da shi idan ya kunna wutar da bai fara kunnawa ba, lokacin da haske ya gama gauraye illahirin akin ne ya juya da niyyar nufar wajen gadon shi. Turus! Ya ja ya tsaya sakamakon arba da mace da yayi a zaune a tsakiyar gadon shi ta juya mishi baya kanta ba ankwale gaba aya gashin ta ya barbazu a kan gadon, wani mugun tsoro ne ya mamaye zuciyar Anwar in har sai da ya ha iyi wani yawu ji kake Mu uttt wucewar yawun zuwa ma oshin shi, a hankali ya fara takawa ya nufi wajen gadon duk da irin bugun da zuciyar shi ta ke mishi hakan ba sai ya dakata da isa wajen gadon ba,hannu ya mi a da niyyar juyo da fuskar ta ta sai dai tun kafin hannun nashi ya sau a a jikin ta ta juyo da kanta suka yi arba da juna fuskarta sha e-sha e da hawaye sai dai kuma a maimakon ya ga ruwan hawaye sai ya ga jini ne yake kwaranyowa daga cikin idanun nata, suman tsaye Anwar yayi cikin rawar murya ya fara nuna ta da hannun shi yana arin furta sunan ta Amr..... Amma ina! Tun kafin ya arasa yaji kamar an saka igiya an aure mishi wuya take ya yanki jiki ya fa i a wajen. Anwar bai tashi tsintar kan shi a ko ina ba sai a gadon asibiti ana mishi arin ruwa, arin mi ewa zaune yake amma ya kasa a hankali ya fara arin tuno abun da ya faru dashi amma abun mamaki hakan ya gagara duk wani arin sa na ganin ya tuno abun da ya faru in ya kasa inda take ya ji kan shi ya auki wani matsanancin ciwo,dafe kan nashi yayi tare da runtse idanun shi, mahaifiyar shi ce ta fara mishi sannu. "Sannu Anwar ka tashi ya jikin dai?". Ta jefa mishi wannan tambayar da sauri yayi saurin bu e idanun shi da suke a runtse dan ganin wanda yake mishi sannun domin kuwa a maimakon ya ji muryar mahaifiyar shi sai ya ji wata murya daban wadda ko shekara ari yayi wannan muryar bazata ta a zama sabuwa ko ba uwa a gare shi ba,ga mamakin shi yana bu e idon nashi sai yaga mahaifiyar tashi ce take mishi sannu, Innalillahi wa'innailaihi rajiun ya shiga maimaitawa a cikin ran shi tare da jefawa kan shi tambayar to mai hakan yake nufi?, Mai yasa muryar ta take mishi gizo?. A hankali ya fara jin alamar kuka a kusa dashi saurin juyawa yayi dan ganin waye aikuwa a take yayi arba da ita a zaune a kusa dashi fuskar ta sharkaf da hawaye, wani ras ya ji gaban shi ya fa i,da sauri ya juya ya dubi inda mahaifiyar shi take zaune ko ita ma taga abun da ya gani in,sai dai daga yanayin fuskarta ya fuskanci cewa bata ga abun da ya gani in ba,sake juyawa yayi inda take zaune in still tana zaune sai dai a wannan karon murmushi take mishi, addu'a ya fara yi duk addu'ar da tazo bakin shi, aikuwa ba'a auki lokaci ba ya nemeta ya rasa, kallon mahaifiyar shi yayi sannan ya bu i baki da niyyar sannar da ita abun da ya faru in sai dai kamar mai cutar mantau haka yaji komai ya kuma shafewa a walwar shi. *****